An karɓo
daga Ummul Mu'uminina, Ummu Abdullahi, A'ishatu (R.A) ta ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Wanda ya ƙirƙiro
wani abu cikin lamarinmu wannan, abin da ba ya cikinsa, to za a mayar masa da
kayansa." Bukhari (#2695) Muslim (#1718)
A riwayar Muslim "Wanda duk ya aikata wani
aikin da ba umaminmu a kai, an mayar masa da shi.
SHARHI
Aisha ɗaya
ce daga cikin matan Annabi (ﷺ), ta samu falalar
kasancewarta matar Annabi (ﷺ). Duk cikin matan
Annabi (ﷺ)
ya fi ƙaunar
ta sama da kowa. Don an
tambayi Annabi (ﷺ)
wa ka fi so? Ya ce, "A'isha!" Aka ce, "A cikin maza fa?" Ya
ce, "Babanta Abubakar!" [Bukhari (#3662)]. Amma duk da Annabi (ﷺ)
ya fi son Aisha, ba ya zaluntar sauran matansa saboda ita. A hannunta Annabi (ﷺ)
ya cika, ya bar duniya. Ta ce, "Allah ya karɓi
ran Annabi (ﷺ), a lokacin ina
tallafe da shi a tsakanin cinyoyina da ƙirjina."
Kuma aka binne shi a ɗakinta.
[Duba Bukhari (#1389) da Muslim (#2443)] Domin bayan rasuwarsa aka ce ina za a
kai shi, waɗansu suka ce,
"A kai shi masallaci." waɗansu
suka ce, "A kai shi Baƙi'a."
waɗansu suka ce, a kai shi
wuri kaza. Sai Sayyidina Abubakar ya ce, "Annabi (ﷺ)
ya faɗa ccwa, "Babu wani
Annabi da ya taɓa
mutuwa, face sai an binne shi a inda Allah ya karɓi
ransa." [Duba Al Musnad Na Abu Ya'ala (#22)]. Ba a ɗaukar sa a kai shi wani wuri, don haka sai aka binne
shi a ɗakin Nana A'isha.
Wannan falala ce! Don da ma Imamu Malik ya rawaito a cikin Muwaɗɗa cewa, "A'isha ta yi mafarkin
taurariɓguda uku sun faɗa ɗakinta,
sai aka wayi gari, sai ta tambayi Abubakar, sai ya yi shiru ya ƙyale
ta, bai ce mata komai ba. Da Annabi (ﷺ)
ya bar duniya aka binne shi a ɗakinta,
sai ya ce, "To wannan ɗaya
daga cikin taurarin kenan, biyun suna tafe." [Duba Muwaɗɗa-Babu ma Ja'a fi Dafnil Mayyit]. Sai
Sayyidina Abubakar kuma ya bar duniya, shi ma sai aka binne shi a ɗakinta, kusa da Kabarin Annabi (ﷺ).
A'isha ta ce, "So nake in mutu a binne ni a wajen." Sai kawai Umar ɗan Khaɗɗab
ya nemi alfarma wajen A’isha, cewa in dai ya riga ta mutuwa, yana so a binne
shi kusa da Abubakar. Ta amince in ya riga ta a sa shi, sai Umar ya riga ta
mutuwa." Wannan mafarki ya tabbata.
Ana ce mata Ummu Abdullahi, ba don ta taɓa haihuwa ba, sai dai akwai yayarta mai suna Asma‘u
bintu Abubakar, tana da ɗa
Abdullahi ɗan gidan Zubair
bin Auwam, ɗaya daga cikin
mutum goma da aka yi musu albishir da aljanna. To wannan Abdullahi ɗan Zubair bin Auwan ɗin,
shi ne Annabi (ﷺ) yake jingina wa
A'isha, ya ce mata Ummu Abdullahi. Kuma daga wannan ne malamai suka ce ya
halatta mutum ya yi alkunya ko da ba shi da ɗa.
Lafazin, 'lamarinmu' da ya zo a wannan hadisi, yana
nufin musulunci. Ma'ana wanda ya ƙirƙiro
wani abu cikin addininmu na musulunci, abin da ba ya cikin musuluncin. [Duba
Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajah 1/163].
Wannan hadisi shi ne ƙashin
bayan rusa dukkan bidi'a a kan ƙasa.
Duk abin da yake bidi‘a ne, wannan hadisi ya rusa shi. Abinda duk mutum ya gina
a kan bidi'a, Allah ba zai ba shi lada ba, don ma ba zai karƙa
ba. Akwai wasu waɗanda
za su zo wajen maganar bidi'a sai su ce, to ai idan ka ce bidi’a, kamar ka ce
kar mu hau keke, kar mu hau babur, kar mu yi amfani da dukkan wani abu ƙirkirarre,
don waɗannan abubuwa bidi’a
ne, don lokacin Annabi (ﷺ) babu su. Sai ka ce da
shi, waɗannan al'amura da ka
zana, ba addini ba ne su, wani abu ne na buƙatar
rayuwa, Annabi (ﷺ) kuwa ya rusa duk abin
da an ƙirƙire
shi ne da sunansa addini, ya ce, "Wanda ya ƙirƙiro
cikin lamarinmu wannan..." Lafazin 'wannan' kuwa da ya zo a nan, nuni ne
zuwa ga musulunci. Babu wanda zai ce idan na hau babur daga nan wurin na tafi
Damaturu, ladana bai kai na wanda ya hau mota ba; wanda ya hau mota gingimari
ta katako, ladansa bai kai wanda ya hau bambalasta ba. Babu wanda zai fadi
haka, don ba ayyukan lada ba ne, buƙatu
ne na duniya. Saboda haka duk bidi'ar da ta shafi lamarin duniya, ƙirƙira
kenan. A duniyance ka ƙirƙiro
mota, ka ƙirƙiro
kwamfuta da dukkan abin da zai taimaka wa rayuwa ta ci gaba, wannan shari'a ba
ta hana ka ba, amma ƙirƙira
ta fuskar addini, ka ƙara ko ka rage,
ka kawo wani zikiri, ko wata falala, ko wata sallah, ko wani salo na Istigfari,
to wannan shari'a ta rushe. Ya tabbata a Sahihi Muslim [#2363], Annabi (ﷺ)
an tambaye shi cewa, ga wasu mutane suna yin kilili. Shi ne su ɗauki dabino idan ya yi huda, su tsaga su dauko irin
nan, su sa a nan, don ya ba da ɗa
mai kyau. Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Wannan
ba zai yi amfani ba." Sai sahabbai suka ce, "Ai mun sha yi, kuma yana
amfani." Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Ku kuka
fi ni sanin lamarin duniya, ku je ku yi kayanku." Saboda wannan ba hailala
ba ne, ba istigfari ba ne, don haka ba ya jiran sai Annabi (ﷺ)
ya bayar da umami kafin su je su yi. Domin duk abin da yake gwaji ya tabbatar;
in haɗa sinadari kaza da kaza
zai baya da kaza, wannan a duniyarka ka je ka yi ta yin ƙirƙire
ƙirƙirenka,
ba a hana ka ba. Amma a cikin lamarin addini dole, ka bi fadin Allah,
(Duk abin da Manzo ya zo muku da shi ku karɓe shi, abin da ya hana ku, ku hanu. Lallai Allah mai
tsananin uƙuba ne) [Al-Hashr: 7]
Kuma babu wata bidi’a mai suna kyakkyawa, dukkan bidi‘a ɓata ce, kar ka taɓa
zaton akwai wata bidi'a sunanta mustahabbiya ko bidi'a hasana, wannan duk
rabe-raben, wanda ya fara kawo shi a cikin duniyur ilimi, shi ne Izzuddeen bin
Abdussalam, wanda ake kira Sulɗnil
Ulama a cikin liltafinsa ƙawa’idul Ahakam
Fi Masalihul Anam, kuma shi ɗan
mazahabar Shafi‘iyya ne, daga wurinsa Imamul ƙarafi,
ɗaya daga cikin malaman
Malikiyya ya ɗauko wannan, ya
rubuta cikin littafinsa. To tunda yake shi ɗan
Malikiyya ne, sai Shehu Usman ɗan
Fodiyo shi kuma ya ɗauko
daga cikin ittafin Imamul ƙarafi
ya sa a nasa. Abu Ishaƙ Asshaɗibi ya yi ragaraga da wannan abu (a cikin littafinsa
Al-I'itisan), kuma shi ma ɗan
Malikiyya ne, ya ce babu wata bidi'a mai suna hasana, wannan Kullu Ala Babiha.
No comments:
Post a Comment