GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (15) HADISI NA SHA BIYAR

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Lallai Annabi () ya ce, "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da kuma ranar ƙarshe, ya fadi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe, to ya girmama maƙocinsa, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe, to ya girmama baƙonsa." Bukhari (#6018) da Muslim (#48) suka rawaito.

SHARHI

Saƙo uku wannan hadisin yake ɗauke da su: Kama harshe; kar mutum ya yarda ya furta magana, sai cikin abin da yake akwai maslaha ta addini ko ta duniya. Maslahar addini,
ita ce abin ya kasance zikiri ne, ko salatin Annabi () ne, ko karatu ne, ko hailala ne, ko istigafari, ko tasbihi. Ko kuma ya kasance abu ne da yake da alaƙa da duniya. Harkar kasuwanci ne za ka ƙulla, wannan ya halatta ka furta da bakinka. Amma duk abin da ya fita daga wannan, abin da zai danganci sharri, to kamata ya yi musulmi ya kame harshensa.

Abu na biyu kuwa cikin saƙon da wannan hadisin yake ɗauke da shi, shi ne ya kasance mutum ya kula da maƙocinsa: Maƙocin nan kuwa, ko da ba musulmi ba ne. Saboda maƙoci nau'i uku ne; Akwai mai haƙƙi uku a kanka, akwai mai haƙƙi biyu, akwai mai haƙƙi ɗaya. Maƙoci mai haƙƙi uku a kanka, shi ne ga shi musulmi, ga shi kuma maƙoci, ga shi kuma akwai dangantaka ta jini a tsakaninka da shi, wanka ne, ko ƙaninka, ko ɗan wanka, ko ɗan ƙaninka, akwai dai alaƙa ta jini tsakaninka da shi. Ma'ana dai, ga haƙƙin maƙwabtaka, ga haƙƙin musulunci, ga haƙƙi na dangantaka da ke tsakaninku. Ka ga haƙƙi uku kenan! Maihaƙƙi biyu kuma a kanka, shi ne haƙƙin maƙotaka da haƙƙin musulunci, amma ba alaƙar jini tsakaninka da shi. Mai haƙƙi ɗaya, shi ne haƙƙin maƙotaka kaɗai, don shi ba musulmi ba ne, ba kuma dangantakar jini tsakaninku. To kowanne daga ciki, ana buƙatar a kyautata masa. Kowanne daga ciki idan ka yi wani abu na ihsani, ya halatta ka yi masa: Idan ka fitar da sadaƙa ta nafila, ko da mutum ba musulmi ba ne, ya halatta ka ba shi sadaƙar nafila, amma sadaka ta wajibi, ta zakka, ita kuwa dole sai musulmi.
Abu na uku da wannan hadisin yake ɗauke da shi, shi ne kyautatawa baƙo lokacin da ya ziyarce ka, lokacin da ya zo wurinka daga wani gari.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...