GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (14) HADISI NA SHA HUDU

An karɓo daga Abdullahi ɗan Mas'ud (R.A) ya ce, Manzon Allah () ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin (laifuka) guda uku: Magidanci mai zina, da ran da ta kashe rai, da wanda ya bar addininsa, ya rabu da jama'a.‘' Bukhari (#6878) da Muslim (#1676).

SJARHI

Manzon Allah () ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin laifuka guda uku...." Na farko, magidanci, Wanda ya taɓa yin aure ingantaccen aure, kuma ya zo ya aikata zina bayan aurensa, to wannan ya zama
magidanci mai zina, hukuncinsa shi ne a jefe shi. Idan an ce magidanci, abin da ake nufi, ba wai lallai sai tsoho ba, a'a! wanda ya taɓa yin aure ake nufi. Sannan kuma laifi na biyu cikin waɗannan laifuka, shi ne rai da ta kashe rai; mutum musulmi ya kashe ɗan uwansa musulmi bisa ga ganganci. Idan musulmi ya kashe dan uwansa musulmi bisa ganganci, hukuncin ɗaya daga cikin biyu ne: Hukuncin farko shi ne ƙisasi. Abin da ake nufi da ƙisasi, shi ne a kashe wannan mutumin, tunda ya kashe ɗan uwansa musulmi, sai fa idan dangin waɗanda aka kashe suka ce, a'a mu mun haƙura da ƙisasi, abin da muke so, a ba mu diyyar ɗan uwanmu. To a nan wurin, sai a sassauta hukuncin daga ƙisasi zuwa ga diyya, su ne abin da ayar suratul Baƙara take nunawa, inda Allah ya ce,
(Ya ku waɗanda suka yi imami An wajabta ƙisasi (wanda ya yi kisa a kashe shi) a kanku (cikin lamarin gawawwaki); ɗa da ɗa, bawa da bawa, mace da mace. Dukkan wanda aka yafe masa wani abu na ɗan uwansa, to sai ku bibice shi da kyautatawa, shi kuma ya biya diyyar tare da ihsani. Wancan (abin da aka ambata) sauƙi da rahama ne daga Ubangijinku, duk wanda ya ƙetare iyaka bayan haka, yana da azaba mai raɗaɗi.) [Al Bakara 178]

Duk wanda ya kashe ɗan uwansa musulmi, hukuncinsa shi ne a kashe shi, sai in dangin waɗanda aka kashe suka ce, "A'a! Mun yafe kisa yanzu, mun yarda da diyya." to sai a biya diyya. Amma idan mutum kisa ya yi na kuskure, kamar ka harba kibiya domin ka harbi barewa, sai ta zarce ka kashe wani ɗan uwanka musulmi a gona yana noma ba ka sani ba, ko ka harba bindiga ta kuɓuce ta je ta harbe wani musulmi ba ka sani ba, ko ka taho da wata mota a sukwane ka kaɗe wani ɗan uwanka musulmi ba ka sani ba, ba ganganci ka yi ba, da kuskure ne, to wannan hukuncinka, shi ne abin da suratun Nisa'i ta nuna,
(Duk wanda ya kashe mumini da kuskure, to ya 'yanta baiwa mumina da diyya abar sallamawa ga danginsa, sai dai in sun yi sadaƙa). [Annisa'iz: 92] Hukunci biyu ne a kanka a lokaci guda: Ka ga wancan ɗaya daga cikin biyu za a yi masa, amma wannan kuma biyu aka dora

masa. Ka ji wani abu na hikimar musulunci! Shi ya yi da ganganci, an ce a yi masa ɗaya daga cikin biyu, kai kuma ka yi da kuskure an ce duka biyun: Na farko shi ne ka biya diyya. Diyyar nan za ka bayar da ita ga 'yan uwan wanda aka kashe shi ɗin. Na biyu daga cikin hukunce-hukuncen, shi ne ka yi kaffara ta hanyar 'yantar da baiwa mumina. Idan ka nemi baiwa mumina ka rasa ta, to shi kenan abin da yake kanka shi ne azumin wata biyu a jere. Idan ka kashe ɗan uwanka musulmi da kuskure, ka zo ana maganar diyya, sai 'yan uwansa suka ce ai sun yafe, to shi kenan yanzu ba abin da ke kanka sai kaffara, diyya ta riga ta faɗi, sai azumin wata biyu a jere. Malamai suka ce, idan ka fara daga faIkon wata, to ba ruwanka, ƙila ka iya yin azumi hamsin da takwas shi kenan ka gama wata biyu, in watan ya yi nukusani, ya yi ashirin da tara, mai zuwa ma ya yi nukusani, ya yi ashirin da tara. Amma in daga tsakiyar wata ka fara, to dole kwana sittin za ka ƙirga.
Gaɓar, “....ya rabu da jama'a." tana nufin ya fita daga musulunci. To wanda ya yi haka, hukuncinsa shi ma a kashe shi.
To waɗannan su ne hanyoyi guda uku da jinin musulmi ke halatta. Idan ya aikata ɗaya daga cikin dangin al'amuran nan guda uku, to jininsa ya halatta! Sai dai ban da wannan guda ukun kuma, akwai waɗansu hanyoyin a wani wuri inda jinin mutum musulmi ke halatta, amma wannan hadisin ya kawo guda uku ne, sai dai ba su kaɗai ba ne. Maganar cewa idan mutum ya kashe mutum musulmi ɗan uwansa da ganganci zai dawwama a cikin wuta kamar yadda aya ta cikin suratun Nisa'i ta nuna, da dama daga cikin malaman da suka gabata cewa sukayi wannan wata razanarwa ce Ubangiji ya yi, amma ba dan zai cika wannan alƙawari ba, yana iya yafewa.
Domin ya ce, (Lallai Allah baya gafartawa in anyi shirka da shi, yana gafarta abin da yake koma-bayan wannan) [Annisa'i: 48]
Kuma idan Allah ya yi alƙawarin zai yi wa mutum azaba, sai ya yafe masa bai cika wannan alƙawarin ba, wannan ba nakasu ba ne ba, ba aibu ba ne, ya zama afuwa ce Ubangiji ya yi. An saɓa masa amma ya yafe. Idan ya yi alƙawari zai yi wa mutum rahama ne, sai bai cika wannan rahama ba, to shi ne za a ce akwai nakasu, to Allah ba ya saɓa alƙawarin rahama, don shi alƙawarin rahama cika shi, shi ne ke nuna kamala, saɓa shi tawaya ne da nakasu. Allah kuwa ba ya siffantuwa da nakasu, sai da kamala koyaushe.

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...