GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (11) HADISI NA SHA DAYA

An karɓo daga Abu Muhammad, (shi ne) Hasan ɗan Aliyyu ɗan Abu dalib, jikan Annabi () abin ƙaunarsa, ya ce, "Na haddato daga bakin Annabi () ya ce, "Ka ƙyale duk abin da ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto." Tirmizi (#2520) da Nasa'i (#5711) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce, "Hadisi ne mai kyau ingantacce."

SHARHI

Annabi () ya ce, "Ka Kyale duk abin da ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto." Ma'ana, duk wani abu da yake da kokwanto, ko zai raba
hankali biyu, ka Kyale shi, ka kama abin da ba ya raba hankali biyu, yana mayar da hankali ne wuri ɗaya. Wannan hadisin Imamu Tirmizi ya rawaito shi, haka Imamu Ahmad ya rawaito wannan hadisin a cikin Musnad, haka Imam Ibnu Hibban Al-Busti shi ma ya rawaito wannan hadisi. Ma'ana dai hadisi ne ingantacce.

Duk abin da yake sa maka kokwanto, to ka Kyale shi, ka komo izuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto. Ka zo yin alwala, ga ruwa guda biyu, wannan ruwan ana tsammanin akwai najasa a cikinsa, wannan ruwan kuma ana da tabbas ɗin ba najasa a cikinsa. Wannan wanda ake tsammanin, duk da cewa najasar ba ta bayyana ba yadda za a gani, amma ana tsammanin akwai ta a ciki, idan za ka yi aiki da wannan hadisin, ka ga wannan wanda kake da kokwanto, sai ka ajiye shi gefe guda, ka ɗauki wancan wanda ba ka da kokwanton. Kai ne kake cikin sallah mai raka'a huɗu, ka yi raka'a uku, ka tashi kana cikin raka'a ta huɗu, sai kokwanto ya zo maka, shin wannan raka'ar da na tashi ta huɗu ce, ko ta uku ce? Ka kasa tantancewa! Yanzu kana da tabbas din raka'a uku, ta huɗu ce kake da kokwanton cewa wataƙila ta hudu ce ko ba ta huɗu ce ba? A nan yadda za ka yi amfani da wannan hadisin, don ka fita daga wannan ruɗanin da ka samu kanka na sallah, sai ka yarda cewa wannan ta uku ce, ka kawo ta huɗu. Shi kenan, ka fita daga cikin kokwanto. Kai ne kake da alwala, ka tabbatar ka yi alwala kafin ka shigo masallaci, ka shigo masallaci ka yi nafila, kana karatun Alkur‘ani, sai shakka ta zo maka, shin alwalata ta warware, ko ba ta warware ba? Samuwar alwala tabbas ne, rashinta ko yanzu kokwanto ne, don ba ka da tabbas din ta warware, ko ba ta warware ba, sai ka yi aiki da wannan hadisi, ka ɗauka kana da alwala. Saboda wannan kokwanto da ya zo maka baƙo ne, ba zai ture tabbas ɗin da kake da shi na alwala ba. Haka kuma idan ka canza hukuncin, kana da tabbas ɗin cewa ka shiga bandaki ka fito, yanzu ka tabbatar ka shiga banɗaki ka fito, amma ka zo ka zauna har aka yi kiran sallah, sai kuma kokwanto ya zo maka, sai kake cewa, shin da na je banɗakin nan na fito ɗazu, na maimaita alwala ko ban maimaita ba? A nan yaddaza ka yi, sai ka ɗauka kawai ba ka yi alwala ba, domin rashin yi ɗin, shi ne asali, sai ka je ka yi. Akwai hadisin da yake taimaka wa wannan, hadisin da Annabi () yake cewa, "Idan ɗayanku yana cikin sallah, Shaiɗan yakan zo ya busa duburarsa, sai mutum ya ji kamar ya yi tusa. Idan ɗayanku ya sami kansa cikin wannan hali, kada ya fita daga cikin masallaci, har sai ya ji wari ko ya ji ƙara." [Bukhari (#137) Muslim (#361)].

4 comments:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...