GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (16) HADISI NA SHA SHIDA

An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, wani mutum ya zo, ya ce da Annabi () "Ka yi min wasiyya." sai ya ce da shi, "Kada ka yi fushi!“ sai ya yi ta maimaita buƙatarsa, sai (annabi ()) ya ce, "Kada ka yi fushi!" Bukhari (#6116) ya rawaito.

SHSRHI
Dangane da lafazin 'wasiyya‘ da ya zo a cikin jumlar, "Ka yi min wasiyya." abin da ake nufi da 'wasiyya', shi ne wata kalma taƙaitacciya da zan daɗe ina amfani da ita a cikin
rayuwata ta duniya, wadda za ta ɗora ni a kan tafarki madaidaici. Da ya ce, "Ka yi min wasiyya.", tsammaninsa .Annabi () zai rubuta masa littafi guda, amma sai ya ce masa "Kada ka yi fushi!" Sai ya yi ta maimaita buƙatarsa ta ɗazu, "....yi min wasiyya." Annabi () yana cewa "Kada ka yi fushi!" Haka dai Annabi () ya tsaya bai ce komai ba, ya ƙyale shi‘. To da aka ce, "Kada ka yi fushi!", ai fushi ba ikonka ba ne, zuwa yake yi, ba ka san ya zo ba. Ka duba Annabin Allah aka ba shi Attaura, aka ce da shi, "....riƙe ta da ƙarfi!" amma da ya zo ya sami kansa a cikin fushi, ya jefar da Attaurar gaba-ɗaya. Yayin da ya huce, sai ya ɗauke ta. To yaya za ka yi, ba za ka yi fushi ba? Ai ba zai yiwu ba a hana ka abin da ba ya yiwuwa. Don haka sai dai a ce, cewar, "Kada ka yi fushi!" yana da ma'ana guda biyu: Waɗansu suka ce ma'anar da za mu iya bayarwa wajen, "Kada ka yi fushi!" shi ne ka siffanta da halaye nagari, kamar karamci, da afuwa, da yawan haƙuri, da yawan kyauta, kar ka zamanto marowaci. To idan ka siffantu da wannan siffofin, su ne za su taimaka maka, su rika rage maka yawan fushi, in ba ka da su kuwa, dole ka yi fushi. Saboda Annabi () ya ce, "Kada ka yi fushi!" kamar yana nufin ka siffantu da ɗabi'u nagari, irin ɗabi’un da suke rage fushi.

Ma‘ana ta biyu suka ce, abin da ake nufi da "Kada ka yi fushi!" shi ne, kada ka yi aiki da fushi in ya zo maka, kar ka zartar da hukunci kana cikin fushi. Domin idan fushi ya yi yawa, ƙila ka zo ka cewa matarka, ka sake ta saki uku! daga baya ka zo kana ta bin malamai kana fatawa. Don haka duk abin da fushi ya shawarce ka, ka yi, kar ka yi aiki da wannan abin, ka nisance shi, ka zamanto

mai haƙuri, mai juriya. [Don ganin ƙarin bayani duba: Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajab 1/373-374]

Wannan wasiyya ta Annabi () ta shafi dukkan dangogin ayyuka na alheri. Kamar yadda malamai suka ce, wannan yana cikin Jawami’ul Kalim da aka ba wa Annabi (). Wato jumla guda ɗaya, amma za ta ɗauki ma‘ana mai ɗimbin yawa, domin za ta shiga cikin kowane ɓangare na rayuwa. Domin fushi yana iya sa ka yi abu ba don Allah ba, sai ya zamanto ba ka samu lada ba wajen Allah.

An rawaito daga Aliyyu bin Abi ɗalib wata rana ya fita wajen yaƙi ya ɗauki takobinsa, ya fuskanci wani kafiri gadan-gadan zai immasa, sai wannan kafiri ya tofa masa yawu, sai Aliyyu bin Abi Dalib ya fasa kashe shi, ya ja baya, ya ba shi wuri. Sai abin ya ba wa wannan kafirin mamaki, ya ce, "Abul-Hasan! Da ka biyo ni kamar za ka kashe ni, ga shi kuma ka samu damar ka kashe ni, amma da na tofa maka yawu, sai ka fasa." Ya ce, "Eh! Lokacin da na taho a karon farko, na zo ne da niyyar zan yaƙe ka, don kai kafiri ne, don ɗaukaka kalmar Allah, in gama da kai musulunci ya ci gaba, amma da ka tofa min yawu, sai na ji haushi, sai na ji tsoron kar in kashe ka, ka ɗauka don ka tofa min yawu ne, ba don kasancewarka kafiri ba. Don haka sai na fasa." To ka ga a nan wurin fushin da Annabi () yake hanawa, shi ne fushi don kanka, kar ka yi fushi don ba da kariya ga kanka, ko ba da kariya ga 'yan uwanka ko 'yan gidanku, don an keta mutuncinsu. Kar ka yi fushi don wannan! Shi ne ma'anar, "Kada ka yi fushi!".

1 comment:

  1. Wane mutum ne yazo wurin manzon Allah (SAW) don niman wasiya?

    ReplyDelete

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...