GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sep 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (13) HADISI NA SHA UKU

An karɓo daga Abu Hamza, Anas ɗan Malik (R.A), yaron gidan Annabi () ya ce, Manzon Allah () ya ce, "ɗayanku ba ya zama mai cikakken imani, har sai ya so wa ɗan uwansa abin da yake so wa kansa." Bukhari (#13) da Muslim (#45) suka rawaito
                   
SHARHI

Faɗin Annabi () cewa, "....ba ya zama mai cikakken imani....”, wannan yana kore cikar imani ne, ba wai yana kore asalin imani ba. Irin waɗannan hadisai suna da yawa.
Wani wanda bai fahimce su sosai ba, sai ya kafa hujja da su bisa cewa, mai aikata saɓo zai iya kafirta, kamar yadda khawarijawa suke yi. Sai su ɗauki irin waɗannan nassosi, sai su ce, ai duk mai saɓo ya kafurta, kuma in ya kafirta zai dawwama a cikin wuta, don Annabi () ya kore musu imani; ya ce, mazinaci a lokacin da yake zina ba shi da imani; Barawo a lokacin da yake sata ba shi da imani; da sauran irin dangin saɓo da Annabi () zai faɗa, sai ya kore imanin, ya ce babu shi. To Annabi () ba yana kore asalin imani ba ne, yana kore cikar imani ne. Abin da ya sa muka ce ba asalin imani yake korewa ba, shi ne ai masu saɓo Allah ya kiraye su da sunan imani, sannan ya ce su tuba. In ba sa saɓo, a ce su tuba? In da kafirtaa suka yi, a sa musu suna muminai? Allah ya ce, (Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku tuba, tuba mai zarcewa) [Attharim: 8] Da ba musulmai ba ne, a kira su da sunan imani? A nan hadisin, da aka ambaci 'ɗan uwa' to 'yan uwantakar musulunci ake nufi, ba 'yan uwantakar jini ba, ba 'yan uwantakar gari ba, ba 'yan uwantakar ƙabila ba. Allah yana cewa,
(Dukkan muminai 'yan uwan juna ne, ku sulhunta ‘yan uwanku, ku ji tsoron Allah ko a ji ƙan ku). [Hujurat: 10]
Dukkan dangin alherin da kake so wa kanka, haka ake so ka so wa kowane ɗaya daga cikin ɗaiɗaikun al'ummar musulmai; dukkan sharri da ba ka so wa kanka, to irinsa ake so ka guje wa dukkan ɗaiɗaikun al'ummar musulmai.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...