GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 3, 2011

ARBA'UNA HADITH NA (18) HADISI NA SHA TAKWAS

An karɓo daga Abu Zarri (shi ne) Jundubu bin Junada, da Abu Abdurrahman (Shi ne) Mu'azu ɗan Jabal (R.A), Manzon Allah () ya ce, ."Ka ji tsoron Allah, a duk inda kake, ka bi mummunan aikin da ka yi da kyakkyawan aiki, sai (wannan kyakkyawan aikin) ya shafe mummunan, ka ɗabi'anci mutane da kyakkyawar ɗabi‘a." Tirmizi (#1987) ya rawaito, ya ce, hadisi ne hasanun a wani bugun ya ce, hasanun sahihun.

SHARHI
Dangane da faɗin Manzon Allah () cewa, "Ka ji tsoron Allah a duk inda kake....", mun riga mun san menene taƙawa. Ita ce abin da duk aka ɗora maka, ka yi, abin da duk
aka hana ka, ka bari. Wannan shi ne taƙawa! Kuma taƙawa mafi tsadar abu kenan, da Allah ya umarci mutanen farko da mutanen ƙarshe su yi, Allah ya ce, (Mun yi wasiyya ga waɗanda muka ba wa littafi gabaninku da ku, da ku ji tsoron Allah.) {Annisa'i: 131] Na farko da na ƙarshe, duk an umarce su da taƙawa. A wani lokaci za a ce, "Ka ji tsoron Allah!" wani lokacin sai a ce, "Ka ji tsoron wuta!" wani lokacin sai a ce, "Ka ji tsoron yinin tashin alƙiyama!“ Ayoyin da suke nuna haka, duk abu ɗaya ne, ma'anarsu dai tana komawa zuwa ga abu ɗaya: Ka ji tsoron fushin Allah! Ka ji tsoron uƙubar Allah! Uƙubar Allah kuwa, ita ce wuta. Wannan wutar ɗin yaushe ne ranar shigar ta, ranar tashin alƙiyama, don haka idan an ce ka ji tsoron wunin, ba wai wunin ba, a’a! abin da zai faru cikinsa. In an ce ka ji tsoron wuta, ba wai don ita ba, sai don saboda uƙuba ce da Allah ya tanada don kar ya yi fushi da kai. In an ce ka ji tsoronta, don shi ne zai yi fushi da kai, ya tilasta ma shiga cikinta. Saboda haka dai duk abu ɗaya ne, "Ka ji tsoron Allah a duk inda kake....", ka ji tsoron Allah a gida, a waje, a ko'ina, ka kiyaye dokar Allah a boye, kamar yadda za ka kiyaye ta a fili, haka ake buƙata.

A gaba sai Manzon Allah () ya ce, in ka yi mummunan aiki, sai ka bi bayansa da kyakkyawa, shi wannan kyakkyawan zai goge mummunan aikin da ka yi. Dangin abubuwan da suke goge zunubi guda goma ne, Ibnul ƙayyim ya ambace su a cikin littafinsa Madaarijus Salikin, cikinsu, akwai tuba. Idan mutum ya tuba, tuba yana kankare zunubin da ya biyo baya. Allah yana cewa,
(Sai wanda ya tuba ya yi imani ya yi aiki na-gari, to waɗannan Allah yana canza munanan ayyukansu zuwa kyawawa, Allah ya kasance mai yawan gafara da jin ƙai) [Al Furkan: 70]

Akwai yawan istigfari, shi ma yana taimakawa wajen kankare zunubi, ko da yake da tuba da istigfari suna haɗuwa wuri guda:
Sannan kuma akwai aikata kyakkyawan aiki mai yawa, wanda har yawansa zai sa a manta da zunubin da ka yi: Akwai ceton masu ceto: Akwai tsayarda haddi akan mutum. ln kayi laifi sai aka tsayar da haddi akanka, shikenan an kankare maka wannan zunubin.
Daga ƙarshen hadisin, sai Manzon Allah () ya ce, "....ka ɗabi'anci mutane da kyakkyawar dabi‘a.“ da haƙuri, da juriya, da sauran al'amuran da ake son mutum ya ɗabi'antu da su.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...