GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (24) HADISI NA ASHIRIN DA HUDU

An karɓo daga Abu Zarri Algifari (R.A) daga Annabi (), cikin abin da (Annabi) ke rawaitowa daga wurin Ubangijinsa. Lallai Allah Maɗaukakin sarki ya ce, "Ya ku bayina! Na haramta wa kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a tsakaninku. Ya ku bayina! Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi, ku nemi shiryarwata, ni kuma in shiryar da ku. Ya ku bayina! Dukkaninku mayunwata ne, sai wanda na ciyar da shi, don haka ku nemi ciyarwata, ni kuma zan ciyar da ku. Ya ku bayina! Kowannenku tsirara yake ba tufafi, sai wanda na suturta, ku nemi suturata, zan suturtar da ku. Ya ku bayina! Kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gaba ɗayansu, ku nemi gafarata, ni kuma zan yi muku gafara ɗin nan. Ya ku bayina! Ba ku i'sa ku cutar da ni ba, ballantana ku ce za ku cutar da ni, ba ku isa ku amfanar da ni ba, ballantana ku ce za ku amfanar da ni. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na ƙarshenku, da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar wani mutum ɗaya cikinku mafi jin tsoron Allah, hakan ba zai kara komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na ƙarshenku, da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar mutum ɗaya mafi fajirci, hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na
ƙarshenku, da mutanenku da aljanunku, su tsaya a bigire ɗaya, kowanne ya roƙe ni, ni kuma kowanne ɗaya daga cikinku in ba shi abin da ya roƙa, hakan ba zai rage komai daga cikin abin da ke wurina ba, sai fa

gwargwadon abin da allura ta rage idan an tsoma ta cikin ruwan teku. Ya ku bayina! Kaɗai ayyukanku ne nake kididdiga su gare ku, sannan in cika muku ladanku. Wanda ya samu alheri, ya gode wa Allah, wanda ya sami wanin haka, kar ya zargi kowa sai kansa. Muslim (#2577) yarawaito.

SHARHI
Wannan hadisi ƙudusi kenan, shi ma wahayi ne daga Allah. Bambancinsa da ayar Alƙur‘ani shi ne, Alƙur'ani ana karanta shi a cikin sallah, amma hadisi ƙudusi ba zai yiwu ka karanta, ka yi sallah da shi ba, dole sai Alƙur'ani. Duk da cewa kowanne daga Allah (SWA) yake. Ana samun lada ta hanyar tilawar Alƙur'ani mai girma, an bautar da mu, mu karanta Alkur'ani mu sami lada, amma hadisul ƙudusi ba haka ba ne. Alƙur'ani an ƙalubalanci duniya da su kawo irinsa, an yi takara da shi, amma hadisul ƙudusi ba a yi ƙalubale da shi ba.

Akwai bambanci da waɗansu suke faɗa, sai su ce Allah ya yi alƙawarin kare Alƙur'ani, amma bai yi alƙawarin kare hadisul ƙudusi ba. Wannan kuskure ne! Ubangiji Ta'ala ya yi alƙawarin kare shari' ar musulunci, shari'ar musulunci kuma ita ce Alƙur'ani da Sunna Yadda Allah ya yi alƙawarin kare Alƙur'ani, haka ya yi alƙawarin kare hadisi.

Dangane da faɗin Allah (SWA) da ya zo a wannan hadisin cewa, "Ya ku bayina! Na haramta wa kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a tsakaninku...." wannan yana nufin, bai halatta wani ya zalunci wani a cikinku ba, kada ku zalunci juna. Ubangiji ya haramta wa kansa zalunci a cikin ayoyi da dama. Zalunci iri biyu ne: Na farko, shi ne zalunci mafi tsanani, wato shirka, bauta wa wanin Allah. Domin asalin kalmar 'zalunci', tana nufin ka ɗauki wani abu ka sa shi a inda bai dace ba. To lokacin da duk ka ɗau wani abu wanda haƙƙi ne na Allah, shi kaɗai, sai ka bai wa wani bawa a cikin bayin Allah, to wannan zalunci na ƙarshe kenan a duniya, kamar ka kirayi wani ba Allah ba. da nufin ya ba ka amfani, ko ya koreɓmaka wata cuta. Don haka Allah ya ce, (Kar ka kirayi wani wanda ba Allah ba, wanda ba shi cutar da kai, ba shi iya amfanar da kai, idan kuwa ka aikata, to kai ka zama cikin azzalumai.) [Yunus: 106]

Don haka Allah ya ce.

(Haƙiƙa shirka zalunci ne mai girma) [Lukman: 13]

Na biyu kuma shi ne, zalunci ƙarami, aikata ayyukan saɓo, kamar shan giya da zina da caca. Duk waɗannan zalunci ne, wanda duk ya yi wannan ya zalunci kansa, amma girman wannan bai kai wancan kashin na farko ba. Wannan zalunci ne wanda in Ubangiji ya ga dama ya yafe ma laifin da ka yi ɗin, wannan tsakaninka da shi, in ya ga dama ya ɗanɗana maka azaba gwargwadon yadda ka cancanta, sannan daga ƙarshe a cire ka a kai ka aljannah. Don a cikin 'yan aljannah akwai azzalumai, wadanda sun zalunci kansu, amma dai daga ƙarshe za a kai su aljannah.

Da Allah (SWA) ya ce, "....Ya ku bayina! Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi, ku nemi shiryarwata, ni kuma in shiryar da ku...." wani zai ga kamar ya ci karo da wani hadisin daban don ya ce, "....Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi...." amma a hadisin Bukhari [Bukhari (#1358) da Muslim (#2658)] kuma daga Abu Huraira (R.A) cewa ya yi, "Duk wani wanda aka haifa, an haife shi ne a kan musulunci." To wannan hadisin ya ce ana haifar mutum a kan musulunci, ko a kan fiɗira, wannan kuma ya ce, "....Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi....", ba cin karo da juna a tsakaninsu. Malamai suka ce, tsarkin yana nan, amma tsarkin kaɗai ba zai wadatar ba, sai idan wahayi ya zo an karɓa. Wahayi kuwa dole sai an koya maka shi, in ka ƙi karɓar wahayin, to kuma kana nan cikin ɓata da ɗimuwa, har sai lokacin da ka koyi wahayin. Wannan shi ne abin da Allah yake nufi da, "....Dukkaninku ɓatattu ne, saiwanda na shiryar da shi...." Haske guda biyu ake buƙata: Hasken fiɗira, kowa an ba shi, sai dai zai iya lalacewa, idan mutum ya tsaya a wurin da jahilci ya yi yawa, sai ya cakuɗe ya gamu da duhu, ba yadda za a yi ya samu haske, sai in hasken wahayi ya zo, sai ya
zamanto haske a kan haske. ' Shi kuwa faɗin Allah (SWA), “....hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba....” yana nuna bunƙasar mulkin Allah Ta'ala kenan. Duk mai mulki yana bunƙasa ne da dawaki da fadawa, amma Ubangijinmu haka yake shi kaɗai ba shi da abokin tarayya, ba ya buƙatar komai. Shi kuma faɗinsa cewa, ayyukanku ina kiyaye su,"....sannan in cika muku su...." yana nufin, a nan duniya zai kama ku da azaba. A sakamakon wani zunubi da ka yi, sai a ɗora maka ciwon kai, don a kankare maka wannan kuskuren da ka yi jiya ko shekaran jiya ba ka sani ba, sai ka je ƙiyama ba ka da laifin komai. Allah ya riga ya tace ka daga zunubi saboda wahalhalun da ya ɗora maka. Waɗansu suka ce a'a! wannan hukuncin a lahira ne.

2 comments:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...