GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (25) HADISI NA ASHIRIN DA BIYAR


An karɓo daga Abu Zarril Al Gifari (R.A) ya ce, "Waɗansu mutane daga cikin sahabban Annabi ()sun ce da shi, "Ya Manzon Allah ()! Ma'abota dukiya sun tafi da lada, suna yin sallar (farilla) kamar yadda muke yi, suna yin azumin (farilla) kamar yadda muke yi, amma kuma suna sadaƙa da sauran dukiyarsu. Sai Annabi () ya ce, "Shin Allah bai riga ya ba ku abin da za ku yi sadaƙa da shi ba ne? Dukkan tasbihi sadaƙa ne, dukkan wata kabbara sadaƙa ce, dukkan wata hamdala sadaƙa ce, dukkan wata hailala sadaƙa ce, umarni da kyakkyawan aiki sadaƙa ne, hana mummunan aiki sadaƙa ne, a gaɓar kowanne daga cikinku akwai sadaƙa"sai sahabbai suka ce "Ya Manzon Allah! Yanzu mutum zai biya buƙatarsa kuma ya zama yana da lada?" Sai (Annabi ) ya ce, "Ku ba ni labari da a ce ya sanya (gaɓar) tasa a cikin haram, shin yana da zunubi? To haka nan in ya sanya ta a halal zai zama yana da lada. Muslim (#1006).


SHARI
Abin nufi, " ...amma kuma suna sadaƙa da sauran dukiyarsu" wanda mu kuma ba mu da kuɗin da za mu yi sadaƙa, saboda haka mu ma a ba mu abin da za mu yi mu sami lada. Ma'ana, shi yana ganin an yi sallah tare, an yi azumi tare, to an zo sadaƙa su kuma ba su da ko kobon da za su yi sadaƙa, sai suke kishin don me wane zai yi sadaƙa, mu ba mu samu damar yin hakan ba? Ina ma mu ma, mu samu halin da za mu yi sadaƙa? Halin ya sha bamban, tsakanin masu kuɗinmu da talakawanmu da kuma na sahabbai, masu kuɗin sahabbai kullum so suke su yi alheri. Lokacin da ayar da Allah yake cewa,

(Ba za ku samu albirru ba ( wanda shi ne shiga aljanna ) har sai kun ciyar daga mafi kyan abin da kuke so). [Ali-Imran: 92] Sai Abu Dalha ya ce, "To ni dai ba abin da nake ƙauna cikin dukiyata irin makekiyar gonata da ake kira Biruhai. Wata gona ce a Madina, wadda saboda daɗin ruwanta Annabi () yana shiga ciki ya huta, ya ɗebi ruwanta ma ya sha. Abu Ɗalha ya ce, "Ba ni da abin da ya fi komai tsada irin wannan gonar, ga shi an ce ba a samun aljannah sai an ciyar daga abin da ake ƙauna, to ga ta nan wurinka, ka raba ta yadda Ubangiji ya umarce ka." [Bukhari (#1461) da Muslim ne suka rawaito wanna ƙissar]. Wato dai sai da ya duba abin da ya fi komai tsada sannan ya bayar. Su kuma talakawansu, sun nemi samun irin wannan ne, ba don su kece raini ba, ko su fi su sa'a, a'a! sai don su ciyar saboda Allah. Don haka suka zo wajen Annabi () suka ce masa "Ma'abota dukiya sun tafi da lada...." sallah mun yi tare, azumi mun yi tare, amma sadaƙa kuma sun fi mu, tunda mu ba mu da abin da za mu yi sadaƙa."Sai Annabi () ya ce da su, "Shin Allah bai riga ya ba ku abin da za ku yi sadaƙa da shi ba ne?" Ai Allah ya riga ya ba ku, "Dukkan tasbihi...." subahallahi da za ku faɗa, kamar ku ɗauki sadaƙar dukiya ne kun bayar da hannunku. Haka, "....dukkan wata kabbara...." da za ku ce, Allahu Akbar; kamar kun ɗauki sadaƙa ne kun bayar.

Akwai riwayar hadisin da ta zo sama da haka, da ta faɗi abin da aka faɗaa musu, tasbihi da hailala da kabbara, suka je suka yi ta yi, su ma masu kuɗin da suka ga haka, suka rinƙa yin tasbihin da hailalar duk gaba ɗaya. Sai suka dawo suka ce, abin da ka faɗa mana, su ma sun ji sun ci gaba da yi, sai Annabi () ya ce, "Ku haƙura, ai falalar Allah ce yake ba da ita ga wanda ya ga dama, ku haƙura.“ To da aka faɗa musu haka, suka ga ba yadda za su yi, kamar yadda hadisi na cikin Bukhari [#1416 da Muslim #1018] ya nuna, sai waɗansu daga cikinsu suke zuwa suna yin dako a kasuwa, ba don talauci ba, sai don su tara abin da zai isa su fitar da zakka, ya zamanto su ma sun taɓa yin zakka kafin su mutu. Sai su yi dako, su yi noma, su yi fatauci, so suke dai wai ya zamanto cikin rukunan musulunci, kowanne sun taɓa yi. To su sahabbai dako suka rikayi don sutara kudin da zasu fitar da zakka.

2 comments:

  1. muna godiya, amma don Allah arinka yin rubutu dakyau, yadda zaibada ma'ana me kyau

    ReplyDelete
  2. Masha Allah mungode

    ReplyDelete

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...