GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (19) HADISI NA SHA TARA

An karɓo daga Abdullahi ɗan Abbas (R.A) ya ce, "Na kasance a bayan Annabi () wata rana, sai ya ce dani, "Ya kai yaro! Zan sanar da kai waɗansu jumloli: Ka kiyaye (dokar) Allah, sai kai ma ya kiyaye ka; ka kiyaye (dokar) Allah, za ka samu (Allah) yana yi maka jagora; idan za ka roƙa, to ka roƙi Allah; in za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah. Ka sani cewa da al'umma za su taru kan su amfane ka da wani abu, ba za su iya su amfanarka da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka (cewa naka ne). Idan da al'umma za su taru kan su cuce ka da Wani abu, ba su isa su cuce ka ba, sai da abin da Allah ya riga ya rubuta maka. An riga an cire alƙalami, takardun sun bushe." Tirmizi (#2516) ya rawaito. ya ce, "Hadisi ne mai kyau ingamtacce."

A Wata riwaya wadda ba ta Tirmizi ba, "Ka kiyaye dokar Allah, za ka samu Ubangiji a gabanka (yana
maka jagoranci), ka nemi sanin Allah lokacin da kake cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani, ka sani duk abin da ya kuskure maka, da ma can ba a yi shi don ya
same ka ba, abin da duk ka ga ya same ka, da ma can ba a yi shi don ya kuskure maka ba. Ka sani cewa cin nasara yana tare da haƙuri, yayewar musiba tana tare da baƙin ciki, kuma lallai a tare da tsanani akwai sauƙi."

SHARHI

"Wannan hadisi an karɓo shi daga Abu Abbas, Abdullahi ɗan Abbas, wato ɗan gidan baffan Annabi () kenan, ya ce, "Na kasance a bayan Annabi () wata rana...." a kan wata dabba. Wannan yana ɗaya daga cikin falalarsa kenan, don adadin sahabban da Annabi () ya ɗora su a kan dabba yana tare da su, ba su da yawa, ba su fi mutum goma ba. Wani malami ya waƙe su. Don haka wata falala ce, Annabi () ya hau kan dabba, ko ya hau kan rakumi, ko kan alfadari, ko doki, ya ɗora ka a baya, kuna tare da shi, wannan falala ce, ba kowa ya samu wannan ba. Kuma wannan sai ya nuna yadda Annabi () ke ƙaskantar da kai, ya fi kowa fa, amma zai hau dabba, ba shi kaɗai ba, ya ɗora wani a bayansa.
Manzon Allah () ya ce, "....in za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah..." kaɗai, kar ka nema a wajen wani. Taimako iri biyu ne, haka neman taimako ma iri biyu ne: Ko dai ya zamanto abin da za ka roƙa ɗan Adam yana da ikon ba ka shi, wannan babu laifi, ko ya zamanto abin da za ka roƙa, ba mai ikon yin sa, sai Allah. Kamar saukar da ruwan sama, da warkar da mara lafiya, da sanya albarka cikin harkar kasuwancinka, da sanya albarka a cikin harkar nomanka, duk wannan ba wanda zai iya yi, sai Allah, to sai ka roKƙ Allah shi kaɗai. Haka neman taimako: In za ka nema, ko dai ya zamanto dan Adam yana da ikon yin sa, kamar, "Kama nan wurin mu ɗora kayan nan a mota." ko "Don Allah! Taimaka min ka tura min motata." Wannan duk ɗan Adam zai iya yi! Amma dangin taimakon da ba mai iya yi sai Allah, to shi ake nufi ka roa wajen Allah shi kaɗai.
Fadin Manzon Allah () cewa, "....da al'umma za su taru kan su amfane ka da wani abu, ba za su iya su amfane ka da komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka...." yana nufin, da a ce duk garin nan su taru sai sun sa ka zama mai arziki, in Allah bai sanya ka mai arziƙi ba, tun lokacin da aka yi rubutu ba, kana cikin mahaifiyarka, ba za ka taɓa zama mai arziƙi ba. Sai a riƙa ba ka abin, amma yana zurarewa; ka samu kuɗin masu tarin yawa, amma ka kashe, su tafi a shirme. Saboda haka in duniya za ta taru ta yi maka wani abu mai amfani, ba za su amfane ka ba, sai da abin da aka rubuta maka can wanda muka karanta a baya. Faɗin Manzon Allah () cewa, "....An riga an cire alƙalami...." yana nufin an cire shi daga kan takardar, har "....takardun sun bushe...." an gama komai kenan. Ma'ana, rubutun da aka ce mala'ika ya yi, ya riga ya yi, har takardun sun bushe, yanzu kawai abin da aka rubuta ne kawai yake gudana, wani bai isa ya canza wannan abin ba.

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...