GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (21) HADISI NA ASHIRIN DA DAYA

An karɓo daga Abu Amrin ko Abi Amrata, Sufyanu ɗan Abdullahi (R.A) ya ce, "Na ce, "Ya Manzon Allah ()! Faɗa min wata magana a cikin addinin musulunci, wadda ba zan sake tambayar waninka ba game da ita." Sai ya ce, "Ka ce, "Na yi imani da Allah." sannan kuma ka daidaitu." Muslim (#38) ya rawaito.

SHARHI

Wannan hadisi ingantacce ne, Imamu Muslim ne ya rawaito shi. Dangane da bayanin imani da Allah, wannan ya riga ya gabata a baya. A duk lokacin da aka faɗi imani, mun san
yana da rukunai guda shida, waɗanda muka yi bayaninsu a cikin hadisi na biyu, a jerin hadisan wannan littafi mai albarka. Sannan kuma da sauran abubuwan da imani ba ya cika sai da su, duk yana cikin, "Na yi imani da Allah...." Daidaituwa kuwa, a nan tana nufin daidaituwa a kan tafarki madaidaici: Kada ka ƙara, kada ka rage kan abin da shari'a ta dora ma, ka nisanci dangogin abubuwan da aka haramta maka, ka yi ƙoƙarin neman halal a cikin dukkanin al'amuran da za ka yi. Wannan shi ne daidaito. Duk mutumin da ya dace da waɗannan abubuwa guda biyu, ga imani ga daidaito, to shi kenan sai aljanna. Shi ya sa Annabi () da kansa, aka umarce shi da daidaito, aka ce masa (Ka daidaita kamar yadda aka umarce ka). [Hud 112].

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...