GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 26, 2011

ARBA'UNA HADITH (22) HADISI NA ASHIRIN DA BIYU

An karɓ0 daga Abu Abdullahi, Jabir ɗan Abdullahi Al ansariy (R.A) ya ce, "Wani mutum ya tambayi Annabi () ya ce da shi, "Ba ni labari idan na sallaci salloli na wajibi, na azumci watan Ramadan, na halatta halal, na kuma haramta haram, ban ƙara komai a kan haka ba, shin kuwa zan shiga Aljanna?" Sai Annabi () ya ce, "Eh! (za ka shiga aljanna).") Muslim (#15).

SHARHI

Abin da wannan hadisi yake nunawa, shi ne, idan mutum zai tsaya a kanwajibi kaɗai, ba tare da ya yi mustahabbi ko ɗaya a rayuwarsa ba, in dai ya sauke dukkan wajiban da ake
buƙata, zai samu shiga aljanna. Abin da wannan hadisi yake nunawa kenan! Don abin da ya zana su ne, azumi da sallah, ya ce, "....idan na sallaci salloli na wajibi, na azumci watan Ramadan..." shi kenan zan shiga aljanna? Annabi () ya ce, za ka shiga aljanna.

Akwai hadisin da ya fi wannan fito da abubuwa fili da ke cikin Sahihul Bukhari. Bukhari ya kawo shi a gurare daban daban, ɗaya daga cikinsu akwai wanda ya kawo a Kitabus Saum (# 1891) da wani mutum ya zo wurin Annabi (), kansa ko hula babu, ga kansa da ƙura, wanda hakan yake nuna kamar daga karkara yake, ya zi ya ce, "Me Allah ya wajabta min na sallah?" Annabi () ya cc, ”Salloli guda biyar, sai dai in ka ga dama ka yi nafila." Ya ce, "Me ya wajabta min na zakka?" Ya ce, kaza da kaza, "Sai dai in ka ga dama ka yi nafila." Ya ce, "Me ya wajabta min na azumi?” Ya ce, "Ramadan. Sai dai in ka ga dama ka yi nafila." Annabi () ya ba shi labarin shari'o'in musulunci, ya koyar da shi, ya sanar da shi, sannan Annabi () ya gama wannan bayani, sai wannan balarabe ya ce, "To na rantse da wanda ya aiko ka da gaskiya! Ba zan ƙara ba, ba zan rage ba." Ma'ana daga wajiban al'amuran da ka gaya min, lallai ba zan rage ba, amma ba zan yi nafila ko ɗaya ba. Sai ya tashi ya fita, sai Annabi () ya ce, "In dai da gaske yake, zai shiga aljanna!" To wannan na nuna mutumin da yake ya dakata a kan ayyukan wajibi, bai yi mustahabbi ba, wannan ba za
a zarge shi ba. Imamun Nawawi ya ce, ma'anar, "....na halatta halal na kuma
haramta haram...." shi ne na aikata abin da yake halal tare da ƙudurcewa Allah ne ya halatta min shi a zuciyata, kuma na nisanci haram tare da ƙudurcewa Ubangiji ne ya haramta min wannan abin.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...