An karɓo
daga Abu Ya'ala Shaddadu bin Ausi (R.A) daga Annabi (ﷺ)
ya ce, "Allah Ta'ala ya wajabta kyautatawa ga kowane irin abu (da mutum
zai yi a duniya) idan kuka yi nufin kisa, ku kyautata kisan, idan kun yi nufin
yanka (dabba) ku kyautata yankan, kowane dayanku (da zai yi yanka) ya wasa
wukarsa, ya hutar da abin yankansa." Muslim (#1955) ya rawaito.
SHARHI
Ma'ana, Ubangiji ya wajabta kyautatawa: Ga kowanne
irin abu da mutum zai yi a duniya, ya zamanto ya kyautata shi. Kowanne irin
abu, ɗan Adam ne, dabba ne;
yana buƙatar
ihsaninka. Don haka sai Annabi (ﷺ)
zai kawo misali ɗaya
wanda ya shafi ɗan
Adam, na biyu kuma wanda ya shafi dabba. Ya ce, "....idan kuka yi nufin
kisa...." to ku kyautata kisan. Wato mutum ne ya yi laifin kisa, kuka zo
za ku kashe shi, wannan kisan, ku kyautata shi. Abin nufi, ku yi amfani da abin
da zai zare ransa nan-take, ba wai ku ɗaure
shi da igiya ku rataye ba, ya daɗe
bai mutu ba. Wannan idan kuka yi haka, kun saɓa
wa wannan hadisin! Ba a ratayewa a musulunci, sai dai a fille kai, ko a yi
amfani da dukkan wani abu wanda nan-da-nan zai ɗauke
ran mutum cikin ƙanƙanin
lokaci, cikin sakan, ko abin da bai kai sakan ba, nan-da-nan ya dauke ran mutum
ya huta. Amma ba mutum ya jigata ba kafin ya mutu, wannan bai halatta ba.
Sannan kuma ba ya halatta ku yi musla, wato kacancana gawar mutum, ko da kafiri
ne kuka zo kashe shi, in dai kun zare masa rai, to ya riga ya gabata, ba sai
kun fille kai, kun yanke hannu, kun yanke ƙafa,
kun ja a ƙasa, wannan duk
ta'addanci ne wanda shari'a ta ce,
(Kada ku yi ta'addanci, haƙiƙa
Allah ba ya son 'yan ta'adda) [Al Bakara: 19o]
Amma malamai sun ce, in mutum ya kashe dan uwansa
musulmi kisa na ganganci, aka zo za a yi masa ƙisasi,
yayin da ya kashe ɗan
uwansa musulmi, kuma ya kacancana gawarsa, to shi ma in an zo kashe shi, babu
laifi a kacancana gawar don ya zamanto ƙisasi
ya tabbata, kamar yadda Allah ya faɗa.
Ko kuma sai dai mu kashe shi kaɗai,
ba sai mun rama abin da ya yi wa ɗan
uwansa ba? Malik da Ahmad bin Hambal da Shafi'i suka ce, ina! Ai yadda ya yi wa
ɗan uwansa shi ma sai an
yi masa. Wannan shi ne ƙisasi!
No comments:
Post a Comment