An Karɓo
daga Abu Ruƙayya, (shi ne) Tamim ɗan Ausid Dari (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ)
ya ce, "Addini nasiha ne!" Sai muka ce, "Ga wa?" sai ya ce,
" (Nasiha ne) ga Allah, da Littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin
musulmi, da dukkan mutane" Muslim ne ya rawaito (#55)
SHARHI
A larabce abin da kalmar annasiha take nunawa, shi
ne tace zuciyarka, wanke zuciyarka dangane da wanda aka ce ka yi masa nasiha ɗin. Don haka shi tace zuciya ya sha bamban: Idan ya
zamanto tace zuciya ga Allah ne, to kenan kar ka
sanya wa Allah kishiya a cikin
zuciyarka, ka wanke zuciyarka gaba-ɗaya
ga Allah, ta yadda babu wanin Allah a cikin zuciyarka. Idan ya zamanto nasiha
ga littafin Allah ne, to shi ne ka yi imani da littafin, ka yarda babu wani
littafin da ya fi shi ginna, ko mutunci a nan duniya, kana ƙoƙarin
karanta shi, kana ƙoƙarin
fahimtar abin da ke ciki, kana yin imani da dukkan abin da Alƙur‘ani
ya kawo na hukunce-hukunce. Wannan ita ce nasiha ga littafin Allah. Nasiha ga
Manzon Allah (ﷺ) kuwa, ka wanke
zuciyarka ga shi Annabin (ﷺ) wajen ƙauna.
Babu wanda kake ƙauna irin yadda
kake son Annabi (ﷺ) a nan gidan duniya,
babu wanda kake yi wa biyayya irin ta Annabi (ﷺ),
babu wanda ka mayar abin koyinka cikin kowane irin halaye nasa, irin Annabi (ﷺ).
Yadda baka yarda ka sa wa Allah kishiya wajen bauta ba, haka ba ka yarda ka sa
wa Annabi (ﷺ) kishiya wajen ɗa'a ba. Duk umarnin da ya kuskura ya ci karo da
umarnin Annabi (ﷺ), to tasa ta ƙare,
ka gama da shi, na Annabi (ﷺ) za ka ɗauka. Wannan shi ne nasiha ga Manzon Allah (ﷺ)
Nasiha ga shugabannin musulmai, shi ne yi musu ɗa‘a
cikin abin da suka yi umarni, wanda bai saɓa
wa Allah ba, da gabatar musu da shawarwari da za su taimaka musu, da yi musu
addu'a ta gari kan nauyin jama'a da ke kansu, da kokarin faɗakar da su, da jan hankalinsu ta hanyar da za su iya
karɓar nasiharka ko
maganarka ko fadakarwa.
Nasiha ga dukkan sauran musulmai 'yan uwanka kuwa,
ita ce ka so musu irin abin da kake so wa kanka. Duk da wane ya yi maka Barna,
ya yi maka ba daidai ba, amma tunda yana son Allah, yana son Manzonsa, sai kake
ƙaunarsa
a zuci, ko da ba ka faɗa
masa ba, kana ƙaunarsa. To idan ka yi
haka, ka yi wa 'yan uwanka musulmi nasiha.
Imam Khaɗɗabi
ya ce, "Nasiha ita ce son alheri ko nufatar alheri game da wanda ake yi wa
nasiha." [Duba: Jami'ul Ulum Wal- Hikam Na Ibnu Rajah 1/207]. Idan ya
shafi Ubangiji, to shi ne tsarkake shi daga dukkan tawaya; siffanta shi da
dukkan wata kamala; kore masa dukkan wani abin bauta. Idan ya shafi Annabi (ﷺ),
to shi ne jin cewa shi ya fi kowa falala da matsayi (ﷺ),
kuma lallai shari'arsa ta shafe kowace shari'a. Idan ta shafi littafin Allah,
to ita ce ɗora littafin
Allah a kan kowane littafi. Idan ta shafi ‘yan uwanka musulmai, ita cr so musu
abin da kake so wa kanka. Idan ta shafi shugabanni, to ita ce yi musu addu'a ta
gari, da fata nagari, da kuma gabatar musu da faɗakarwa
ta hanyar da za su iya ji su yarda, tsakaninka da su." [Duba: Jami'ul Ulum
Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/207-212].
No comments:
Post a Comment