An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Yana daga kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da
muhimmanci a gare shi."(” Tirmizi (#2318) da Ibnu Majah (#3976).
SHARHI
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "Yana daga
kyawun musuluncin mutum, barin abin da ba ya da muhimmanci a gare shi."
yana nufin, duk abin da ba shi da muhimmanci, to a rabu da shi. Wannan shi ke
nuna kyautatuwar
musuluncinka. Wannan muhimmancin, ta fuskar addini ne, amma ta
fuskar duniya, duk abin da ba shi da muhimmanci a duniyance, to kyawun
musuluncinka, shi ne barin wannan al'amarin, amma duk abin da yake da
muhimmanci ko ta fuskar addini ko ta fuskar duniya, to wannan ana bu
ƙatar
ka neme shi, dama an halicce ka ne domin Ibada. Allah yana cewa,
(Ban
halicci mutum da aljan ba sai don su bauta mini) [Azzariyat 56] In ta fuskar
duniya ne, Allah ya ce, (Kada ka manta rabonka daga duniya) [Al-ƙasas
77]. Amma duk abin da ba shi da muhimmanci a duniya ko lahira, to yana daga kyautatar
imanin mutum, ya bar wannan shirmen, ya kama abin da zai amfane shi, ko a
duniyarsa ko a lahirarsa. Waɗansu
suna kafa hujja da wannan hadisin, cewa idan muna tattaunawa ni da wani ta
addini, sai wani ya zo ya tsoma baki, sai mu ce ai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Yana cikin kyawun musuluncin mutum ya bar abin da bai shafe shi
ba." don haka ba da kai muke magana ba, don me za ka tsoma baki? Ba haka
hadisin yake nufi ba, abin da hadisin yake nufi, shi ne lallai mutum ya bar
abin da ba shi da muhimmanci, ba wai abin da bai shafe shi ba. Domin
tattaunawar da kuke yi, ko dai ta zamanto tana da alaƙa
da ibada, to ta shafe ni, don ni ma musulmi ne, ina dangantuwa zuwa ga wannan
addinin, ko ta zamanto tana da alaƙa
da duniya, in na sani, dole in tsoma baki a ciki, ko ya zamanto a aikin saɓo
kuke, ya wajaba a gare ni in yi hani daga mummunan aiki. To don me za ka ce ba
ta shafe ni ba? Ta kowace fuska maganar ta shafe ni, sai dai idan saɓo
kuke, na yi umarni kuka ƙi bari, sai in bar wajen.
Wannan hadisi Imamu Tirmizi ya rawaito shi da sauran waɗansu
malamai, kamar Ibnu Majah, da Imamu Ahmad a cikin Musnad, amma shi ya rawaito
shi ba ta fuskar Abu Hurairata ba, ta fuskar Hasan Bin Aliyyu Bin Abi ɗalib
ya rawaito shi. Hadisi ne ingantacce.
No comments:
Post a Comment