An karɓo
daga Abu Abdullahi, Nu'uman ɗan
Bashir, (R.A) ya ce, "Na ji Manzon Allah (ﷺ)
yana cewa, "Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane
take, amma a tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane
ba su san su ba. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, haƙiƙa
ya nemi kuɓutar da
addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka
cikih haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga
(ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara!
Iyakar Ubangiji ita ce abubuwan da ya haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki
akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan
jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya)
ita ce zuciya."
Bukhari #59 da Muslim (#1599).
SHARHI
Ma'ana, halal a bayyane yake a cikin Alƙur'ani
da hadisai tabbatattu daga Annabi (ﷺ),
haka kuma haramun a bayyane yake a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga
Annabi (ﷺ),
amma a tsakanin halal da haram, akwai
waɗansu
al'amura masu rikitarwa: Su ba su da siffa ta halal tsantsa, ballantana mu sa
su a layin halal, ba su da siffa ta haram tsantsa, ballantana mu sa su a layin
haramun. Akwai waɗansu
daga cikin siffofinsu sun yi kama da halal ta wani ɓangare, ta wani ɓangaren
kuma sun yi kama da haram, don haka sai suka zamanto masu kama da juna, ko masu
rikitarwa, ta yadda ba ka san a ajin da za ka ajiye su ba. “aɗannan abubuwa masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane
ba su san su ba, ba su san hukuncinsu ba. Wannan yana nuna akwai waɗansu kaɗan
cikin mutane sun san su, su ne malamai tabbattu a cikin ilimi, su ba su da
rikici a cikin abin, da sun ga abin za su gane. Amma da yawa cikin mutane za su
rikitar da su, su kasa gane wane aji ya kamata su ba su. [Duba Jami'ul Ulum
Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/181]
A nan wurin abin da malamai suke cewa shi ne, akwai
abubuwa da dama da asalinsu ana ɗaukar
su a halal ne, ba ka da damar ka cire su daga halacci, sai da nassi, akwai kuma
abubuwan da ake ɗaukar
su a matsayin haramci, ba ka da damar ka cire su daga haramci, sai da nassi,
Kamar misalin duk wani dangin abinci wanda zai karɓi sunan aɗɗayyib,
wanda kuma bincike ya nuna ba ya cutar da tunani, ba ya cutar da lafiyar jiki, ba
ya cutar da hankalin ɗan
Adam, ba ya gurɓata
masa tunani, to wannan abin halal ne. Idan ka ba da fatawa a kan halaccinsa, ba
a bin ka bashin dalili, duk wanda ya bi ka bashin dalili, bai san abin da yake
ba. Amma in wani ya zo ya yi da'awar haramci kan abin da yake yana cikin aɗɗayyiba, to wanda ya yi da'awar haramcin,
shi ne aa a ce ina dalilinsa? Saboda haka, asali dangane da abinci ko abin sha,
matuƙar
ya zama ba ya cutar da jiki, ko hankali, to ya zama ɗayyib, shi kuma halal ne, Allah ya ce;
(Ka ce an halatta muku dukkan dangin abinci ki abin
sha wanda yake daddaɗa)
[Suratul Ma'ida 4].
Asali kuma cikin dukkan abinci ko abin sha wanda zai
cutar da hankali, ko zai cutar da lakar jiki, yana shiga cikin babin haramun,
idan ka ba da fatawa da haramcinsa, ba ka neman dalilin da zai ƙarfafa
maka fatawarka. Sai dai zai iya yiwuwa ka samu wani abu da ba ya cutarwa a jiki
ko a hankali, amma duk da haka haram ne, saboda ba mallakarka ba ne, sato shi
ka yi, ko kwato shi ka yi. To a nan wurin sai ya zama ya tashi daga suna halal,
ya zama haram.
Waɗannan
al‘amura masu rikitarwa, malamai sun yi maganganu a kansu: Waɗansu suka ce kamar a sami wani abu wanda nassi guda
biyu suka zo a kansa, ɗaya
nassin yana nuna halaccinsa, ɗaya
nassin yana nuna haramcinsa, kuma mun kasa tantance wanne nassi ne ya riga
zuwa, ballantana mu ce nassin ƙarshe
ya shafe na farko. Wato an sami Annasikh Wal Mansukh! To wannan yana cikin
al'amura masu rikitarwa, in mun ce halal ne, ga wani nassin can ya ce haramun
ne, in mun ce haramun ne, ga wani nassin can ya ce halal ne! [Don karin bayani
duba: Jami‘ul Ulum Wal-Hikam Na Ibnu Rajab 1/183]. Amma idan ka je wajen
malamai masu zurfin ilimi sai su ce, wancan nassi na farko da ya ba da halacci,
nassi ne na Makka, wancan nassin ɗayan
da ya ba da haramci, nassi ne na Madina, na Madina ya shafe na Makka, don haka
ya zama haramun.
Waɗansu
suka ce "....al'amura masu rikitarwa...." da aka ambata a wannan
hadisin, sun ƙunshi sabon abu da zai
faru, wanda bai taɓa
faruwa ba lokacin Annabi (ﷺ) a yanzu kuma sai muka
kasa sanin a ina za mu ajiye shi. Ya yi kama da halal, ya yi kama da haram,
kuma mun kasa sanin a ina za mu ajiye shi? To irin waɗannan su ne, "....al‘amura masu
rikitarwa....", kuma suna buƙatar
malamai masu zurfin ilimi, masana game da nassosin shari'a, masana game da abin
da ke faruwa a duniyar yau, a zamanin yau, sai su haɗa nassosin shari'a da sababbin abubuwa da ke faruwa
don a san wane irin hukunci ya kamata a ba su.
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Duk
wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, to haƙiƙa
ya nemi kuɓutar da
addininsa da mutuncinsa...." yana nuna kai musulmi, yayin da duk ka ga
wani abu wanda ba ka iya tantance halacci ko haramcinsa ba, ya rikitar da kai,
to a nan tsira da addininka, tsira da mutuncinka, shi ne ka bar wannan abin.
Yayin da duk abu ya rikitar da kai, sai ka guje shi gaba ɗaya don ka kuɓuta
da addininka. Misali kai ne kake da wani samfuri na takalmi, sai ka zo ka shiga
masallaci, da ka fito, sai ka nemi takalminka ka rasa, can sai ka hangi wani
takalmi inda ba nan ka ajiye naka ba, da nisa daga inda ka ajiye naka. Amma da
ka je sai ka gan shi kamfani ɗaya,
ƙira
ɗaya, ƙila
har sabunta iri ɗaya
da naka, sai dai in da matambayi zai tambaye ka, shin kana da tabbas wannan
takalminka ne? Za ka iya rantsewa kan takalminka ne? Za ka ce "Eh! Irinsu
dai ɗaya da nawa, amma ba
zan iya ba ka tabbas cewa nawa ne ba." To wannan ya shiga cikin
"....al'amura masu rikitarwa...." Idan kana da tabbas ɗin naka ne, ko kana da yaƙini
cewa mai wannan shi ya ƙauki naka, in
kana da yaƙinin wannan, to
dama-dama, ka iya ƙauka ka riƙe
kafin ka je ka yi bincike, amma in ba ka da wannan yaƙini,
ba ka da wannan tabbas ɗin,
zato ne kake da shi, ba za ka gina hukunci kan zato ba.
Na biyu suka ce, kamar yara ne guda biyu 'yan
tagwaye mata, aka haife su a gida ɗaya,
ɗaya daga cikin yaran
matan, kun yi tarayya da ita wajen shan mama. Ma'ana mace ɗaya ta shayar da ku, kai da ita. Ka ga ya zama
tabbas wannan ta zama haram, ba za ka aure ta ba, saboda an shayar da ku, sai
aka mai da ita gidansu, bayan an yaye ta, ta girma tare da 'yar uwana wacce aka
shayar da ita a wani gida na daban. Da suka girrna, sai ka ga ɗaya daga cikinsu kana so, amma da aka zo bincike sai
aka kasa gane wacce ce kuka sha nono tare da ita, wacce ce ba ku sha tare da
ita ba, tunda ga shi Hasana da Usaina ne gida ɗaya
suka taso. Wacce aka samu tabbas ba ku sha tare da ita ba, ya halatta ka aure
ta, wacce aka samu tabbas kun sha mama tare da ita, bai halatta ba ka aure ta.
Yanzu kuma ba ka da tabbacin da za ka tantance wannan. Abin da ya kamata ka yi,
sai ka bar su duka biyun, ka je wani gidan ka yi aure. Wannan shi ne zai
tabbatar da ka kuɓutar
da addininka, ka kuɓutar
da mutuncinka, ba ka faɗa
cikin abin da Allah (SWA) ya haramta maka ba.
Shi kuwa faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Wanda
ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikin haram...." da shi
ne malamai suke cewa duk abin da ya rikitar da kai, ka kasa gane halaccin ko
haramci, to nisantarsa shi ne addini. Ka nisanci abin gaba ɗaya don ka huta wa kanka, don idan ka afka ciki, mai
yiwuwa ka iya afkawa cikin haram, ba tare da ka sani ba. Kamar makiyayi ne da
yake kiwo a gefen shinge, wato iyaka. Duk makiyayin da ya zo dabarsa na cin
ciyawar da ke kan iyaka, idan dabbar nan ta cinye ciyawar da ke kan iyaka, to za
ta shiga cikin gona ne kai tsaye. To tun asali da ta je iyaka, sai ka hana ta.
Duk abin da yake kusa da haram, mafi kyau ka nisance shi, saboda kusantarsa,
shi ne zai iya aukar da kai cikin haramun gaba ɗaya
tsundum.
A gaba sai Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "....Lallai kowane sarki yana da iyaka...." ta ikonsa, yana da
iyakar ƙasarsa,
iyakar da Ubangiji ya ɗora,
ba ya son a ƙetare ta, shi ne,
"....abubuwan da ya haramta...." Ma'ana, yadda ka san sarki ba zai so
ka shigo ƙasarsa ba, to haka
Ubangiji Ta'ala ba ya son ka ƙetare
abin da ya haramta maka: Abin da duk ya haramta, mafi kyau ka nisance shi, kar
ka kusanci inda yake. Dukkan abin da yake mai rikitarwa, to ana so muturn ya
nisance shi, saboda ya tabbatar da kariyar mutuncinsa. Shi ya sa wata rana
Annabi (ﷺ)
yana i'itikafi a masallaci, sai matarsa Safiyya ta kawo masa ziyara. Bayan ta
daɗe tana hira da Annabi (ﷺ),
sai ta tashi cikin duhun dare za ta tafi, sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Mu je in raka ki, zuwa ƙofar
masallaci." Ya raka ta har wajen masallaci, sai ga waɗansu mutane guda biyu daga nesa. Sun gane Annabi ne,
amma ba su san waccce wadda Annabi (ﷺ)
yake tare da ita ba, sun dai gan shi da wata mace. Da suka ga haka, sai suka ja
baya, za su tafi. Sai Annabi (ﷺ) ya ce, "Ku
tsaya, inda kuke!" Suka tsaya. Ya kama hannun matarsa, suka je, ya ce,
"Ni ne Muhammad Rasulullahi, wannan kuma Safiyya ce, matata. Sai suka ce,
"Ya Annabin
(2)Hadisi Na
Shida
Allah! Me ya kawo haka? Ai ba za mu munana zato gare
ka ba," Sai ya ce, "A'a! Shaiɗan
na gudana cikin jikin ɗan
Adam. Duk inda jini yake zirga-zirga, Shaiɗan
yana shiga, sai na ji tsoron kada ya jefa muku wani sharri a cikin
zuciyarku." [Duba Bukhan' (#2035) da Muslim (#2174)]. Ka ga wannan shubuha
ce ta faru, don wani na iya zuwa ya ce ya gan shi da wance, sai ya yi maza ya
kare kansa, ya nuna cewa matarsa ce.
Haka kuma Anas ɗan
Malik za shi masallacin juma'a, ashe ya makara bai sani ba, yana fitowa, ya
kusa zuwa masallaci, sai ya ga ana dawowa, an gama sallah a masallaci. A
matsayinsa kuma, idan waɗansu
suka gan shi, za su ce, ka ga ma ko juma'a ba ya zuwa, sai ya ruga a guje, ya
sami wani lungu ya Buya. Don kar ya tsaya a inda za a gan shi wurin tuhuma, a
ce ga shi ma yanzu yake zuwa masallaci, yanzu ya zo, ƙila
ba ya son ya bi limamin ne, ƙila
kaza ne, ƙila kaza ne! Don ya
kore wa kansa wannan tuhumar, sai ya ɓuya
bai flto fili jama'a sun gan shi ba.
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Lallai
a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru". idan
ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya) ita cc zuciya." yana nufin, ba abin da ke
sa a shiga aljanna sai gyaruwar zuciya, ba gyaruwar jiki ba; ba abin da ke sa a
shiga wuta, sai lalacewar zuciya, ba lalacewar gangar jiki ba. Ka rasa hannu,
ko ka rasa ƙafa, ko ka rasa ido, in
dai zuciyarka a raye take da imani, wannan ba abin da zai kawo maka cikas wajen
shiga aljanna ba ne, kuma ranar alƙiyama
duk sai an mayar ma da gaɓɓanka
kamar yadda suke lafiyayyu. Ko gurgu sai an tayar da ƙafarsa
ta mike, saboda zuciyarsa ta rayu da imani, sai a gyara jikinsa gaba ɗaya. Amma kana da dafin zuciya, shirka ta mamaye
zuciyarka ta ko'ina, ga laflyar gaɓɓai,
wannan ba abin da zai hana mutum ya shiga wuta. Shi ya sa Allah ya ce,
(Ranar da dukiya da ‘ya'ya ba sa amfani. Sai wanda
ya je wa Allah da zuciya lafiyayya) [Asshu'ara 88-89]
A
nan Allah (SWA) bai ce, "Sai wanda ya zo da jiki lafiyayye." ba, cewa
ya yi, "Sai wanda ya zo da zuciya lafiyayya." warkakkiya, wankakkiyar
zuciya, tatas, babu hassada, ba ganin ƙyashi.
To dangane da gyaruwar zuciya kuwa, zuciya ba abin da zai gyara ta, sai bin
abin da Allah ya saukar na wahayi, sai sunnonin Annabi (ﷺ).
Kullum ka yi ƙoƙarin
raya zuciyarka da Alƙur'ani mai girma, ka yi ƙoƙarin
raya zuciyarka da sauraron hadisan Annabi (ﷺ).
Hadisi Na 27
ReplyDelete