An karɓo
daga Abdullahi ɗan
Mas'ud (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin (laifuka) guda uku: Magidanci mai
zina, da ran da ta kashe rai, da wanda ya bar addininsa, ya rabu da jama'a.‘'
Bukhari (#6878) da Muslim (#1676).
SJARHI
Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Jinin mutum musulmi ba ya halatta, sai da ɗaya daga cikin laifuka guda uku...." Na farko,
magidanci, Wanda ya taɓa
yin aure ingantaccen aure, kuma ya zo ya aikata zina bayan aurensa, to wannan
ya zama
magidanci mai zina, hukuncinsa shi ne a jefe shi. Idan an ce magidanci,
abin da ake nufi, ba wai lallai sai tsoho ba, a'a! wanda ya taɓa yin aure ake nufi. Sannan kuma laifi na biyu cikin
waɗannan laifuka, shi ne
rai da ta kashe rai; mutum musulmi ya kashe ɗan
uwansa musulmi bisa ga ganganci. Idan musulmi ya kashe dan uwansa musulmi bisa
ganganci, hukuncin ɗaya
daga cikin biyu ne: Hukuncin farko shi ne ƙisasi.
Abin da ake nufi da ƙisasi, shi ne a
kashe wannan mutumin, tunda ya kashe ɗan
uwansa musulmi, sai fa idan dangin waɗanda
aka kashe suka ce, a'a mu mun haƙura
da ƙisasi,
abin da muke so, a ba mu diyyar ɗan
uwanmu. To a nan wurin, sai a sassauta hukuncin daga ƙisasi
zuwa ga diyya, su ne abin da ayar suratul Baƙara
take nunawa, inda Allah ya ce,
(Ya ku waɗanda
suka yi imami An wajabta ƙisasi (wanda ya
yi kisa a kashe shi) a kanku (cikin lamarin gawawwaki); ɗa da ɗa,
bawa da bawa, mace da mace. Dukkan wanda aka yafe masa wani abu na ɗan uwansa, to sai ku bibice shi da kyautatawa, shi
kuma ya biya diyyar tare da ihsani. Wancan (abin da aka ambata) sauƙi
da rahama ne daga Ubangijinku, duk wanda ya ƙetare
iyaka bayan haka, yana da azaba mai raɗaɗi.) [Al Bakara 178]
Duk wanda ya kashe ɗan
uwansa musulmi, hukuncinsa shi ne a kashe shi, sai in dangin waɗanda aka kashe suka ce, "A'a! Mun yafe kisa
yanzu, mun yarda da diyya." to sai a biya diyya. Amma idan mutum kisa ya
yi na kuskure, kamar ka harba kibiya domin ka harbi barewa, sai ta zarce ka
kashe wani ɗan uwanka
musulmi a gona yana noma ba ka sani ba, ko ka harba bindiga ta kuɓuce ta je ta harbe wani musulmi ba ka sani ba, ko ka
taho da wata mota a sukwane ka kaɗe
wani ɗan uwanka musulmi ba ka
sani ba, ba ganganci ka yi ba, da kuskure ne, to wannan hukuncinka, shi ne abin
da suratun Nisa'i ta nuna,
(Duk wanda ya kashe mumini da kuskure, to ya 'yanta
baiwa mumina da diyya abar sallamawa ga danginsa, sai dai in sun yi sadaƙa).
[Annisa'iz: 92] Hukunci biyu ne a kanka a lokaci guda: Ka ga wancan ɗaya daga cikin biyu za a yi masa, amma wannan kuma
biyu aka dora
masa. Ka ji wani abu na hikimar musulunci! Shi ya yi
da ganganci, an ce a yi masa ɗaya
daga cikin biyu, kai kuma ka yi da kuskure an ce duka biyun: Na farko shi ne ka
biya diyya. Diyyar nan za ka bayar da ita ga 'yan uwan wanda aka kashe shi ɗin. Na biyu daga cikin hukunce-hukuncen, shi ne ka
yi kaffara ta hanyar 'yantar da baiwa mumina. Idan ka nemi baiwa mumina ka rasa
ta, to shi kenan abin da yake kanka shi ne azumin wata biyu a jere. Idan ka
kashe ɗan uwanka musulmi da
kuskure, ka zo ana maganar diyya, sai 'yan uwansa suka ce ai sun yafe, to shi
kenan yanzu ba abin da ke kanka sai kaffara, diyya ta riga ta faɗi, sai azumin wata biyu a jere. Malamai suka ce,
idan ka fara daga faIkon wata, to ba ruwanka, ƙila
ka iya yin azumi hamsin da takwas shi kenan ka gama wata biyu, in watan ya yi
nukusani, ya yi ashirin da tara, mai zuwa ma ya yi nukusani, ya yi ashirin da
tara. Amma in daga tsakiyar wata ka fara, to dole kwana sittin za ka ƙirga.
Gaɓar,
“....ya rabu da jama'a." tana nufin ya fita daga musulunci. To wanda ya yi
haka, hukuncinsa shi ma a kashe shi.
To waɗannan
su ne hanyoyi guda uku da jinin musulmi ke halatta. Idan ya aikata ɗaya daga cikin dangin al'amuran nan guda uku, to
jininsa ya halatta! Sai dai ban da wannan guda ukun kuma, akwai waɗansu hanyoyin a wani wuri inda jinin mutum musulmi
ke halatta, amma wannan hadisin ya kawo guda uku ne, sai dai ba su kaɗai ba ne. Maganar cewa idan mutum ya kashe mutum
musulmi ɗan uwansa da ganganci
zai dawwama a cikin wuta kamar yadda aya ta cikin suratun Nisa'i ta nuna, da
dama daga cikin malaman da suka gabata cewa sukayi wannan wata razanarwa ce
Ubangiji ya yi, amma ba dan zai cika wannan alƙawari
ba, yana iya yafewa.
Domin ya ce, (Lallai Allah baya gafartawa in anyi
shirka da shi, yana gafarta abin da yake koma-bayan wannan) [Annisa'i: 48]
Kuma
idan Allah ya yi alƙawarin zai yi wa mutum azaba,
sai ya yafe masa bai cika wannan alƙawarin
ba, wannan ba nakasu ba ne ba, ba aibu ba ne, ya zama afuwa ce Ubangiji ya yi.
An saɓa masa amma ya yafe. Idan
ya yi alƙawari
zai yi wa mutum rahama ne, sai bai cika wannan rahama ba, to shi ne za a ce
akwai nakasu, to Allah ba ya saɓa
alƙawarin
rahama, don shi alƙawarin rahama cika shi, shi
ne ke nuna kamala, saɓa
shi tawaya ne da nakasu. Allah kuwa ba ya siffantuwa da nakasu, sai da kamala
koyaushe.
Jazakallahu khairan
ReplyDelete