An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Lallai Allah tsarkakakke ne, kuma ba ya karɓar abu, sai tsarkakakke. Allah ya umarci muminai da
irin abin da ya umarci Manzanni da shi. Ya ce, "Ya ku Manzanni! Ku ci daga
daɗaɗan abubuwa, kuma ku yi aiki na-gari" kuma
(Allah) ya faɗa (lokacin da
yake umartar muminai) "Ya ku waɗanda
suka yi imani! Ku ci daga daɗaɗan abubuwan da muka azurta ku da shi." Sannan
(Annabi ﷺ)
ya ambaci wani mutum, da yake tsawaita tafiya, gashin kansa ya yi gizo, ya yi ƙura,
yana miƙa
hannayensa zuwa ga sama, yana ccwa, "Ya Rabbi! Ya Rabbi!” amma kuma
abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafmsa haramun ne, an ciyar da
shi haram. Ta yaya za a amsa masa (addu'arsa)? (Muslim #1015)
SHARH
Abin da ake nufi da, “....Allah Ta‘ala tsarkakakke
ne...." shi ne kamili ne shi cikin siffofinsa, babu tawaya ko nakasa tare
da shi (ﷺ).
Dukkan wani dangi na tawaya, Allah ya tsarkaka daga barinsa, dukkan dangi na
kamala, Allah ya siffanta da wannan. Dukkan siffar da ke nuna kamala, to Allah
shi ne da mafi cikar wannan siffar: Ilimi kamala ne, to Allah shi ya fi kowa
ilimi; ƙarfi
kamala ne, to Allah ya fi kowa ƙarfi,
adalci kamala ne, to Allah shi ya fi kowa adalci a bayan ƙasa.
Dangane da faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....kuma
ba ya karɓar abu, sai
tsarkakakke....", idan an ce aiki tsarkakakke, to ana nufin abin da ya
cika sharuɗɗa waɗanda shari'a da gindaya a kansa, aikin da aka dogara
da Alƙur'ani
da hadisi dangane da tabbatuwarsa.
Dangane kuwa da faɗinsa
cewa, "....Allah ya umarci muminai da irin abin da ya umarci Manzanni da
shi....", a nan wurin, ka ga Allah ya ce wa Manzanni, "Ku ci daga daɗaɗan
abubuwa...." ya ce kuma da muminai, "Ku ci daga daɗaɗan
abubuwan da muka azurta ku da shi." Irin abin da Allah ya kallafa wa
Manzanni, ya ce lallai su yi, haka ya ɗora
wa bayinsa muminai. Wannan yana nuna mana, dukkan abin da mutum zai yi Allah ya
karɓa, to ya zamanto wannan
abin tsarkakakke, halatacce ne, ya cika sharuɗɗan
da shari'a take buƙata. Kowace irin
ibada, sai ta cika wannan! Idan ibada za a yi ta da dukiya, to ya zamanto
dukiyar da aka yi wannan ibada da ita, dukiya ce ta halal, ba dukiya ce da aka
same ta ta hanyar maguɗi
ba. In za ka yi masallaci, in za ka yi makaranta, in za ka je hajji ko umara,
ko za ka biya wa wani ya je, to ya zamanto dukiya ce ta halal, da guminka ka
samu; ta hanyar .. fatauci, ko ta hanyar kasuwanci, ko mutuwa aka yi aka bar ta
a gidanku, sai ka sarrafa ta wannan tasarrufin, to wannan ya halatta, kuma kana
da lada a kai. Amma in dukiya ta kasance ta “maguɗi
ko haram ce, ko ta ƙwace ce, ko ta
sata ce, ko ta sama dafaɗi
ka same ta, to ko ka bayar da kujera ɗari
ko miliyan, ba ka da lada a wajen Allah. Ko ka ɗauki
kuɗin sata ka je hajji, ko
ka je umara, ba za a karɓa
maka ba, domin "....Allah tsarkakakke ne, ba ya kuma karɓar abu, sai tsarkakakke...." Saboda haka wajibi
ne mutum ya nemi halak cikin dukkan abin da zai yi, sannan ya bayar da dukiya
ta halal. Haka kuma, ta iya yiwuwa abin naka na halal ne, sai dai ba ya da
nagarta, sai ka ɗauka
ka bayar sadaƙa, to Allah ba ya son
irin wannan sadaƙar. Kamar abinci
ya lalace, sai ka ɗauka
ka bayar sadaƙa, ko ka taskance
shinkafa ko masara ko gero a suto, har ya fara lalacewa, ta yadda ko ka kai shi
kasuwa ba zai yi ƙima ba, ba zai
yi daraja ba, wannan Allah ba zai saurare ka ba, saboda Allah Ta'ala mai tsarki
ne, kuma ba ya karɓar
aiki sai mai tsarki. Kuma Allah yana ccwa,
(Ya ku waɗanda
kuka yi imani! Ku ciyar daga daɗaɗan abubuwan da kuka tsururuta, da abin da muka fitar
muku daga cikin ƙasa, kada ku
nufaci lalatacce ku ce daga shi za ku ciyar, alhali ku ba za ku kabe shi ba,
sai kun runtse idanu. Ku sani haƙiƙa
Allah mawadaci ne abin godiya). [Bakara: 267]
Sannan Annabi (ﷺ)
ya ambaci wani mutum da yake tsawaita tafiya: Wasu malamai sun ce tafiyar aikin
hajji ce, wasu kuma sun ce tafiyar umara ce, wasu suka ce a'a! yana cikin
tafiyar datake ta ɗa‘a
ce. Ma'ana dai, wannan mutum yana cikin tafiya, kuma tafiyar ɗa'a ga Allah Ta‘ala, ga gashin kansa duk ya cure da
juna, bai ma samu ya taje gashin kansa ba, duk ya ƙuƙƙulle
saboda halin tafiya, sannan kuma, duk ya yi datti, ya yi ƙura.
Manzon Allah (ﷺ) ya ambaci wannan
mutum ya ce, "....yana miƙa
hannayensa biyu biyu zuwa sama, yana cewa "Ya Rabbi! Ya Rabbi!!"amma
kuma abincinsa haramun ne, abin shansa haramun ne, tufafinsa haramun ne, an
ciyar da shi haram (tun yana yaro).
Ta yaya za a amsa masa (addu'arsa)?" Ma'ana, ai
ba za a amsa masa ba. Sharaɗin
da ake buƙata ga addu'a a yi ta,
a karɓa, ya cika: Ga shi dai
matafiyi ne, ana amsa addu'ar mutumin da yake matafiyi. Saboda haka lokacin
tafiya, hali ne na amsa addu'ar mutum. Ga shi kuma, "....gashin kansa ya
cakuɗe, ya yi ƙura...."
wanda yake nuna yana cikin wahala. Duk mutumin da yake cikin halin tsanani, ana
sa ran a karɓa masa
addu’arsa, don Allah ya ce,
(Lallai a tare da tsanani akwai sauƙi.
Lallai a tare da tsanani akwai wani sauƙi)
[Sharahz5-6].
A nan wurin sauƙi
biyu ne, tsanani ɗaya,
waye zai rinjayi wani? Mutumin da ke cikin tsanani, ana sa ran sauƙi
zai zo masa da wuri. Sannan kuma shi wannan mutumin da Manzon Allah (ﷺ)
yake magana a kansa, ya yi riƙo
da wani ladabi cikin ladubban addu'a, shi ne mutum ya ɗaga hannayensa sama. Annabi (ﷺ)
in yana addu'a, yana ɗaga
hannayensa sama. Hadisai mutawaturai suka zo daga Annabi (ﷺ)
cewa, idan Annabi (ﷺ) yana addu'a yana ɗaga hannu sama, in ya gama addu'a kuma saukewa yake,
ba ya shafa wa a fuska. Ga shi kuma mutumin ya tabbatar wa Allah rububiyyarsa,
bai haɗa Allah da kowa ba, don
yana cewa, ”Ya Rabbi! Ya Rabbi?!" Wato yana tabbatar wa Allah
rububiyyarsa, imani da cewa ba wanda zai cire shi daga wannan abun, sai Allah.
Tsabar tauhidi duk ya kankama, amma me ya kawo cikas aka ƙi
karɓar addu'arsa? Abin da
ya biyo baya shi ne, cewa, "....abincinsa haramun ne, abin shansa haramun
ne, tufafinsa haramun ne, an ciyar da shi haram, ta yaya za a amsa masa
(addu'arsa)?" Ba wai don addu'ar ce bai karanta daidai ba, ya karanta
daidai; ba wai don bai ɗaga
hannu ba, ya ɗaga hannu; ba
wai don bai cancanta ba, ya cancanta, tunda yana cikin tsanani, amma me ya kawo
masa cikas? Sharuɗɗai
sun cika, amma sai aka samu wani abu da ke hanawa. Kamar mutum ne ya cancanci
cin gado ta kowacce fuska, sai wani abu ya zo ya hana shi cin gado: Misali
akwai dangantaka tsakaninsa da mamaci, kuma lallai mamacin ya mutu wannan yana
da rai, ka ga dukkan sharuɗɗai
da ake buƙata sun cika, wannan
musulmi ne, wannan musulmi ne, sai muka bincika sai muka ga wannan ɗan, shi ya kashe mahaifinsa, ka ga ba za mu ba shi
gado ba, tunda shi ya kashe mahaifinsa. Wannan hadisin yana nuna mana yunƙurin
neman halal a cikin dukkanin al’amura: In za mu yi tufafi, ya zamanto halal ne,
haka in za mu ci, ya zamanto halal ne, domin duk inda haramun take, ba ta da
albarka, halal ita ce mai albarka, halal za ka ci ka kwanta lafiya, haram kuwa
idan ka ci, ko ba ta tashi a nan ba, to za ta tashi a can. Saboda haka ya
kamata mutum ya kiyaye wannan. Allah yana cewa;
(Ka ce, "Halal da haram ba su zama ɗaya
ba, ko da yawan harmun ɗin
nan ya burge ka."). [Al Ma‘ida: 100].
Allah ya sakada alheri
ReplyDelete