An karɓo
daga Abu Zarri (shi ne) Jundubu bin Junada, da Abu Abdurrahman (Shi ne) Mu'azu ɗan Jabal (R.A), Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, ."Ka ji tsoron Allah, a duk inda kake, ka bi mummunan aikin da ka
yi da kyakkyawan aiki, sai (wannan kyakkyawan aikin) ya shafe mummunan, ka ɗabi'anci mutane da kyakkyawar ɗabi‘a." Tirmizi (#1987) ya rawaito, ya ce,
hadisi ne hasanun a wani bugun ya ce, hasanun sahihun.
SHARHI
Dangane da faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "Ka ji
tsoron Allah a duk inda kake....", mun riga mun san menene taƙawa.
Ita ce abin da duk aka ɗora
maka, ka yi, abin da duk
aka hana ka, ka bari. Wannan shi ne taƙawa!
Kuma taƙawa
mafi tsadar abu kenan, da Allah ya umarci mutanen farko da mutanen ƙarshe
su yi, Allah ya ce, (Mun yi wasiyya ga waɗanda
muka ba wa littafi gabaninku da ku, da ku ji tsoron Allah.) {Annisa'i: 131] Na
farko da na ƙarshe, duk an umarce su
da taƙawa.
A wani lokaci za a ce, "Ka ji tsoron Allah!" wani lokacin sai a ce,
"Ka ji tsoron wuta!" wani lokacin sai a ce, "Ka ji tsoron yinin
tashin alƙiyama!“ Ayoyin da suke
nuna haka, duk abu ɗaya
ne, ma'anarsu dai tana komawa zuwa ga abu ɗaya:
Ka ji tsoron fushin Allah! Ka ji tsoron uƙubar
Allah! Uƙubar
Allah kuwa, ita ce wuta. Wannan wutar ɗin
yaushe ne ranar shigar ta, ranar tashin alƙiyama,
don haka idan an ce ka ji tsoron wunin, ba wai wunin ba, a’a! abin da zai faru
cikinsa. In an ce ka ji tsoron wuta, ba wai don ita ba, sai don saboda uƙuba
ce da Allah ya tanada don kar ya yi fushi da kai. In an ce ka ji tsoronta, don
shi ne zai yi fushi da kai, ya tilasta ma shiga cikinta. Saboda haka dai duk
abu ɗaya ne, "Ka ji
tsoron Allah a duk inda kake....", ka ji tsoron Allah a gida, a waje, a
ko'ina, ka kiyaye dokar Allah a boye, kamar yadda za ka kiyaye ta a fili, haka
ake buƙata.
A gaba sai Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, in ka yi mummunan aiki, sai ka bi bayansa da kyakkyawa, shi wannan
kyakkyawan zai goge mummunan aikin da ka yi. Dangin abubuwan da suke goge
zunubi guda goma ne, Ibnul ƙayyim
ya ambace su a cikin littafinsa Madaarijus Salikin, cikinsu, akwai tuba. Idan
mutum ya tuba, tuba yana kankare zunubin da ya biyo baya. Allah yana cewa,
(Sai wanda ya tuba ya yi imani ya yi aiki na-gari,
to waɗannan Allah yana canza
munanan ayyukansu zuwa kyawawa, Allah ya kasance mai yawan gafara da jin ƙai)
[Al Furkan: 70]
Akwai yawan istigfari, shi ma yana taimakawa wajen
kankare zunubi, ko da yake da tuba da istigfari suna haɗuwa wuri guda:
Sannan kuma akwai aikata kyakkyawan aiki mai yawa,
wanda har yawansa zai sa a manta da zunubin da ka yi: Akwai ceton masu ceto:
Akwai tsayarda haddi akan mutum. ln kayi laifi sai aka tsayar da haddi akanka,
shikenan an kankare maka wannan zunubin.
Daga
ƙarshen
hadisin, sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "....ka ɗabi'anci
mutane da kyakkyawar dabi‘a.“ da haƙuri,
da juriya, da sauran al'amuran da ake son mutum ya ɗabi'antu
da su.
No comments:
Post a Comment