An karɓo
daga Abu Huraira Abdur-Rahman ɗan
Sakhrin (R.A), ya ce, na ji Manzon Allah (ﷺ)
yana cewa, "Duk abin da na hane ku (da bari), to ku nisance shi. Abin da
na umarce ku da shi, to ku zo da shi (wannan abin) gwargwadon iko. Abin da ya
hallakar da waɗanda suke kafin
ku, yawan tambayoyinsu, da saBawarsu ga Annabawansu."Bukhari (#7288) da
Muslim (#1337) suka rawaito shi.
SHARHI
Wannan hadisi, an karɓo
shi daga Abu Huraira, Iimamin masu hadisi cikin sahabban Annabi (ﷺ).
Sunansa shi ne Abdur-Rahman bin Sakhrin Addausiy. Malamai sun yi
saɓani wajen sunansa, amma wannan shi ne mafi inganci.
Ya musulunta a shekara ta bakwai bayan hijirar Annabi (ﷺ),
amma tare da haka, ya haddace hadisai masu ɗimbin
yawa cikin hadisan Annabi (ﷺ). Abu Huraira ya ce,
da ya zo Madina (da ma ba ɗan
Madina ba ne) sahabbai waɗansu
suna gonakinsu suna noma, waɗansu
suna tafiya kasuwa, ya ce, "Ni kuwa abin da nake buƙata,
in sami abin da zan ci kawai. In na sami abin da zan ci a wannan yinin, sai in
zo in zauna a wurin Annabi (ﷺ), ba na rabuwa da shi,
duk abin da ya faɗa
na riɗe." Har wata rana
Annabi (ﷺ)
ya sa ya shimfiɗa
mayafinsa, da ya shimfida mayafinsa, Annabi (ﷺ)
ya ce, "Daga yau ɗin
nan, duk abin da ka ji daga bakina, ka haddace shi kenan. ɗauki mayafinka ka tafi!" Ya ɗauki mayafinsa ya yafa a jikinsa. Tun daga ran nan
ya ce, "Duk abin da ya fito daga bakin Annabi (ﷺ)
na haddace shi." [Duba Bukhari (#118, 119) da Muslim (#2492)]. Shi Abu
Huraira, ba ya noma, ba ya kasuwanci. Ya ce, yana nan, duk abin da Annabi (ﷺ)
ya faɗa ya riƙe.
Ba don komai ba, sai don saboda ya sanar da al'umma wannan abin. Ya ce,
"Sau da dama mutum zai fito daga masallaci, sai in bi shi ina tambayarsa
fassarar wata aya, in bi shi ina tambayar sa wani hadisi, ba wai don ban san
ayar ko hadisin ba, kila ma na fi shi sani, amma don saboda ko ya yi min tayi,
ya ce, "Zo mu je gidana mu ci abinci." Shi dai ba zai ce masa,
"In zo gidanka in ci abinci?" ba. [Duba Bukhari(#6452)].
Dangane da faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "Duk abin
da na hane ku (da bari), to ku nisance shi... ,wannan da ma, duk abin da
shari'a ta yi umarni iri biyu ne Ko abin da yake umarni ne ko abin da yake
hani. To sai dai malamai suka ce, aikata abin da aka hana, ya fi girman laifi,
sama da ka yi sakaci wajen ƙin
aikata umami. Suka ce hani ba sassauci, tunda Annabi (ﷺ)
ya ce, " Duk abin da na hane ku, ku nisance shi..,." bai ce kar ku yi
shi ba, sai ya ce, "....ku nisance shi." ba ma ku kusanci wurin abin
ba. Amma a wajen umarni, sai ya ce "....to ku zo da wannan abin gwargwadon
iko...." [Dubaz Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajah 1/246]. Asalin sallah
ka yi a tsaye, idan ba ka da lafiya, sai ka yi a zaune, ya halatta, in rashin
lafiyar ya yi tsanani sai a kwance za ka iya yi, sai ka yi a kwancen, ya
halatta. Asalin sallah shi ne ka fuskanci alƙibla.
Amma sai ka zo baƙunta wani garin
da ba ka san alƙibala ba, kuma
ba ka samu wanda za ka tambaya ba, to duk inda ka ga dama ka yi sallah, ya
halatta. Ko da yake akwai malamai da suke cewa ka yi sallah huɗu Ka kalli nan, ka kalli nan, ka kalli nan. Sai dai
a nan, an tsananta da yawa! Abin da shari'a ta wajabta maka, shi ne, ina ne
inda ka nutsu cikin zuciyarka cewa nan ne alƙibla,
ko da ba nan ba ne ka yi sallah, ta wadatar, ba sai ka yi sallah huɗu ba. Haka nan lokacin sallah ya kusa fita, saura kaɗan, ba ka sami ruwan alwala ba, ko ruwan wanka, ba
ka sami ƙasar
da za ka yi taimama ba, sai ka yi sallah a haka, kada ka ce sai ka je nernan
ruwan har lokacin sallah ya fita baka yi ba. Wannan kuskure ne! Allah yana
cewa,
(Haƙiƙa
sallah (ta kasance) a kan muminai, farilla mai ƙayyadajjen
lokaci) [Annisa'i: 103].
Da Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "....Abin da ya hallakar da waɗanda
suke kafin ku, yawan tambayoyinsu....", tambaya a nan, akwai wacce ta
halatta, akwai wacce ba ta halatta ba: Tambaya irin wacce ta halatta, ita ce
irin wacce kake son ka fahimci wani
abu na hukuncin shari'ar musulunci, wanda ka jahilce
shi. Irin wannan tambayar, wajibi ne ka yi ta! Allah ya ce,
(Ku tambayi ma'abota sani, in ba ku sani ba) [Al
Anbiyya: 7]. In ba ka san abu ba, wajibi ne ka tambaya, kafin ka aikata shi
Amma irin tambayar da mutanen Makka suke yi wa Annabi (ﷺ),
sun tambaye shi abin da suka san ba zai iya yi ba, su ce sai ya yi. Kamar yadda
suka riƙa
faɗa a aya ta 90 cikin
suratul Isra'i.
(Suka ce ba za mu yi imani da kai ba har sai ka ɓuɓɓugo
mana da idaniyar ruwa daga ƙasa)
[Isra‘i: 90].
Ka ji abin da suka gindaya: Wai sai an fitar musu da
maremarin ruwa yana gudana a cikinta, da kuma Korama a cikin sahara, inda ba a
tsammanin ganin ruwa; ko kuma ya kasance, ka rufto mana da sama, kamar yadda
kake faɗa; ko ka kasance kana
da gida na zinare da azurfa, bulo ɗin
da simintin, da fentin, da komai da komni na zinare; ko kawai mu ga an turo
maka wata matattakala, ka tattaka kana hawa sama. Suka ce, "Ko da mun ga
kana tattataka wa ɗin
nan fa, ba za mu yi imani da hawan da ka yi sama ba, har sai ka sauko da wani
littafi, ka ba mu muna karanta wa, mun ga an cebkai Manzo ne zuwa gare
mu." To irin wannan tambayar, ita Manzon Allah (ﷺ)
yake nufi da ya ce, "....Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku...." shine yawan
tambayoyinsu. In ka ji an zargi tambaya a cikin nassin Alƙur'ani
ko nassin hadisi, to irin wannan tambaya ake zargi, don ba tambaya ce ta neman
fahimta ba. Haka kuma yana cikin tambayar da malamai ke zargi, shi ne ka
tambayi abin da bai da amfani, ka riƙa
tambaya a kan wasu al'amura da suka faru a baya, wanda bayaninsu bai zo ba ko a
nassi, sai dai an kawo su a jimlace, kai kuma ka dinga neman bayaninsu
dalla-dalla. Kamar alƙaluman da aka yi
takara lokacin da aka kawo Maryam wajen ɗaliban
Zakariyya, kan cewa waye zai riƙe
ta. To sai wani ya zo ya tambaye ka, wannan alƙaluman
na meye? Da kara aka yi su? Karan gero ko dawa? Ko gamba ce? Ko menene? Farare
ne ko baƙaƙe
ne? Yanzu in ka san wannan, me zai ƙara
maka, kuma in ka jahilci wannan, mai zai rage maka? Duk wannan ba su da amfani!
Ko bayanin cewa lokacin da Fir'auna ya bi Annabi Musa da runduna dubu nawa ya
tafi da ita? Sannan wane irin sirdi ya ɗora
wa dokinsa? Sannan dokin baƙi
ne ko fari ne ko ja ne ko wankan tarwada ne? Me za ka ƙaru
a cikin wannan, in an sanar da kai, kuma me za ka yi asara, in ka jahilci
wannan?
Masha Allah, Allah ya saka da alheri 🤲
ReplyDelete