An karɓo
daga Abdullahi ɗan
Umar (R.A) ya ce, "Lallai Annabi (ﷺ)
ya ce, "An umarce ni in yaƙi
mutane, har sai sun shaida babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, (sun
yarda Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, su tsayar da sallah, kuma su bayar da
zakka. Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai
da haƙƙin
musulunci, hisabinsu yana wajen Allah Maɗaukaki."
Bukhari (#25) da Muslim (#22) ne Suka ruwaitoshi.
SHARHI
Da Annabi (ﷺ)
ya ce, "An umarce ni in yaƙi
mutane....", a nan kafuai ake nufi, ba dukkan mutane ba. Wannan wani
salone na larabci, salo ne na Alƙur'ani,
salo ne na hadisi, a
kawo gamammen lafazi, amma ana nufin keɓantanttun mutane, ko a kawo keɓantattun mutane ana nufin gaba ɗaya.
Faɗinsa
kuwa cewa, "....sai da haƙƙin
musulunci...." yana nufin sai sun karya wata dokar musulunci wacce ke sa a
zubar da jinin mutum, to a lokacin sai a zubar da jinin nasu. Wato sai ya zama
haddi ne, ba wai don kasancewarsu kafirai ba, Sai don kasancewar sun taka wani
haddi. Kamar mutum ya kashe ɗan
uwansa musulmi, kisa na ganganci, ka ga akwai haddi a kansa, sai dai idan waliyyan
wanda aka kashe sun ce suna son diyya, to sai a
koma kan diyya a bar ƙisasi.
Fadifisa kuwa, "....hisabinsu yana wajen
Allah." yana nufin shi (Manzon Allah (ﷺ)
zahiri ya sani, bai san baɗininsu
ba. In sun faɗi kalmar
shahadar nan da gangan, a zuciyarsu babu ita, wannan su da Ubangijinsu ne, shi
ne ya san abin da ke cikin zuciya, ni ban sani ba, in sun faɗa da yaƙini
da gaskiya, to wannan Allah ya san abin da ke cikin zuciyarsu na imani, zai
kuma yi musu sakamako gobe kiyama gwargwadon abin da ke cikin zukatansu. Wannan
sai yake nuna idan mutum ya furta kalmar shahada, za ka ɗauke shi a asalin musulmi, har sai lokacin da ya yi
wani abu da k warware ta, sannan ne za cire shi daga wannan asali zuwa ga
wani abin daban. Amma matukar mutum ka gan shi a yau musulmi, ka ce kai musulmi
ne? Ya cc, "Eh! Ni musulmi ne.", to ba ka da damar ka ce da shi aƙidarka
ba ta da kyau, har sai ka ga cikin maganganunsa ko ayyukansa, wani abu ya
bayyana da ke warware musulunci, to a lokacin nan sai ka tambaye shi abu kaza, da
kaza, da ka yi yana warware musuluncin mutum, saboda dalili kaza, da kaza. Amma
ya ce, "Eh! Na sani yana warwarewa, amma duk da haka na yi." To
wannan ya tabbatar wa kansa kafirci. Ko kuma ya ce ban sani ba, sai a yau, ko
ya ce ai abin nan da ka faɗa
yana warware musulunci, ni ban yarda ba, wannan dalilan da ka faɗa ban gamsu da su ba, ina da dalilan da aka faɗa min, wanda nake ganin sun fi naka karfi. To a nan
wurin aiki ne ya same ka wajen gamsar da shi da dalilai, don ka nuna masa naka
sun fi nasa.
Cikin wannan hadisin, akwai wani abu, Annabi (ﷺ)
ya ƙirga,
abubuwa guda uku: (Kalmar shahada, tsayar da sallah, bayar da zakka), sai ya
ce, "....Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare
ni, sai da haƙƙin musulunci...."
Mu kuwa mun riga mun san cewa, kalmar Shahada kaɗai
tana shigar da mutum musulunci. Yanzu idan mutum ya zo ana cikin yaƙi
tsakanin kafirai, sai ya yi kalmar shahada, za ka kyale shi a matsayin ya
musulunta, ba za ka ce a'a! sai ka yi sallah a gabana ko kuwa in kashe ka ba.
Amma dangane da abin da ya sa Annabi (ﷺ)
ya kawo abubuwa guda uku a jere, shi ne sai malamai suke cewa, asali idan mutum
ya zamanto ba musulmi ba ne, sai ya zamanto ya furta kalmar shahada, kalmar
shahadan nan ta biya, ta riga ta wadatar, ta shigar da shi musulunci. Yanzu
idan ya ƙi
yin sallah kuma, sai dai a ce haddi ne, za a kashe shi ne, don haddi ba don
kasancewarsa kafiri ba. Idan mutane suka ƙi
bayar da zakka har aka yaƙe su, to wannan
ana kashe su ne don ladabtarwa, ba don kafirci ba. Don haka farko idan mutum ya
zo zai shiga musulunci, kar ka yi masa dogon sharhin cewa musulunci yana da
rukunai guda biyar, kalmar shahada, da sallah, da zakka, da azumi, da kuma
hajji, ka ce wai sai in ya yarda da su gaba-ɗaya
tukun. Ba haka ake karantarwa ba, abin da kawai za ka bayyana masa, shi ne
ma'anar kalmar shahada. In ka sanar da shi ita, ya yarda, to sannan sai ka ce,
to kuma abu na biyu da ke biyowa shi ne sallah. In ya yi sallah, sai zakka. Da
haka, da haka, za ka isar masa musulunci. Amma lokaci guda, ba ka ɗora wa mutum dukkan waɗannan
abubuwa gaba-ɗaya ba.
No comments:
Post a Comment