An karɓo
daga Abu Muhammad, (shi ne) Hasan ɗan
Aliyyu ɗan Abu dalib, jikan
Annabi (ﷺ)
abin ƙaunarsa,
ya ce, "Na haddato daga bakin Annabi (ﷺ)
ya ce, "Ka ƙyale duk abin da
ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa maka kokwanto." Tirmizi
(#2520) da Nasa'i (#5711) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce, "Hadisi ne mai
kyau ingantacce."
SHARHI
Annabi (ﷺ)
ya ce, "Ka Kyale duk abin da ke sa maka kokwanto, zuwa ga abin da ba ya sa
maka kokwanto." Ma'ana, duk wani abu da yake da kokwanto, ko zai raba
hankali biyu, ka Kyale shi, ka kama abin da ba ya raba hankali biyu, yana mayar
da hankali ne wuri
ɗaya.
Wannan hadisin Imamu Tirmizi ya rawaito shi, haka Imamu Ahmad ya rawaito wannan
hadisin a cikin Musnad, haka Imam Ibnu Hibban Al-Busti shi ma ya rawaito wannan
hadisi. Ma'ana dai hadisi ne ingantacce.
Duk
abin da yake sa maka kokwanto, to ka Kyale shi, ka komo izuwa ga abin da ba ya
sa maka kokwanto. Ka zo yin alwala, ga ruwa guda biyu, wannan ruwan ana tsammanin
akwai najasa a cikinsa, wannan ruwan kuma ana da tabbas ɗin
ba najasa a cikinsa. Wannan wanda ake tsammanin, duk da cewa najasar ba ta
bayyana ba yadda za a gani, amma ana tsammanin akwai ta a ciki, idan za ka yi
aiki da wannan hadisin, ka ga wannan wanda kake da kokwanto, sai ka ajiye shi
gefe guda, ka ɗauki
wancan wanda ba ka da kokwanton. Kai ne kake cikin sallah mai raka'a huɗu,
ka yi raka'a uku, ka tashi kana cikin raka'a ta huɗu,
sai kokwanto ya zo maka, shin wannan raka'ar da na tashi ta huɗu ce,
ko ta uku ce? Ka kasa tantancewa! Yanzu kana da tabbas din raka'a uku, ta huɗu
ce kake da kokwanton cewa wataƙila
ta hudu ce ko ba ta huɗu
ce ba? A nan yadda za ka yi amfani da wannan hadisin, don ka fita daga wannan
ruɗanin da ka samu kanka na
sallah, sai ka yarda cewa wannan ta uku ce, ka kawo ta huɗu.
Shi kenan, ka fita daga cikin kokwanto. Kai ne kake da alwala, ka tabbatar ka
yi alwala kafin ka shigo masallaci, ka shigo masallaci ka yi nafila, kana
karatun Alkur‘ani, sai shakka ta zo maka, shin alwalata ta warware, ko ba ta
warware ba? Samuwar alwala tabbas ne, rashinta ko yanzu kokwanto ne, don ba ka
da tabbas din ta warware, ko ba ta warware ba, sai ka yi aiki da wannan hadisi,
ka ɗauka kana da alwala. Saboda
wannan kokwanto da ya zo maka baƙo
ne, ba zai ture tabbas ɗin
da kake da shi na alwala ba. Haka kuma idan ka canza hukuncin, kana da tabbas ɗin
cewa ka shiga bandaki ka fito, yanzu ka tabbatar ka shiga banɗaki
ka fito, amma ka zo ka zauna har aka yi kiran sallah, sai kuma kokwanto ya zo
maka, sai kake cewa, shin da na je banɗakin
nan na fito ɗazu,
na maimaita alwala ko ban maimaita ba? A nan yaddaza ka yi, sai ka ɗauka
kawai ba ka yi alwala ba, domin rashin yi ɗin,
shi ne asali, sai ka je ka yi. Akwai hadisin da yake taimaka wa wannan, hadisin
da Annabi (ﷺ) yake cewa, "Idan ɗayanku
yana cikin sallah, Shaiɗan
yakan zo ya busa duburarsa, sai mutum ya ji kamar ya yi tusa. Idan ɗayanku
ya sami kansa cikin wannan hali, kada ya fita daga cikin masallaci, har sai ya
ji wari ko ya ji ƙara." [Bukhari (#137)
Muslim (#361)].
Annabi ya Yi Gaskiya
ReplyDeleteEnter your comment... Ubangiji ya karawa annabiiii daraja da sahabban sa
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDelete