An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, wani mutum ya zo, ya ce da Annabi (ﷺ)
"Ka yi min wasiyya." sai ya ce da shi, "Kada ka yi fushi!“ sai
ya yi ta maimaita buƙatarsa, sai
(annabi (ﷺ)) ya ce, "Kada ka
yi fushi!" Bukhari (#6116) ya rawaito.
SHSRHI
Dangane da lafazin 'wasiyya‘ da ya zo a cikin
jumlar, "Ka yi min wasiyya." abin da ake nufi da 'wasiyya', shi ne
wata kalma taƙaitacciya da zan daɗe ina amfani da ita a cikin
rayuwata ta duniya,
wadda za ta ɗora ni a kan
tafarki madaidaici. Da ya ce, "Ka yi min wasiyya.", tsammaninsa
.Annabi (ﷺ) zai rubuta masa
littafi guda, amma sai ya ce masa "Kada ka yi fushi!" Sai ya yi ta
maimaita buƙatarsa ta ɗazu, "....yi min wasiyya." Annabi (ﷺ)
yana cewa "Kada ka yi fushi!" Haka dai Annabi (ﷺ)
ya tsaya bai ce komai ba, ya ƙyale
shi‘. To da aka ce, "Kada ka yi fushi!", ai fushi ba ikonka ba ne,
zuwa yake yi, ba ka san ya zo ba. Ka duba Annabin Allah aka ba shi Attaura, aka
ce da shi, "....riƙe ta da ƙarfi!"
amma da ya zo ya sami kansa a cikin fushi, ya jefar da Attaurar gaba-ɗaya. Yayin da ya huce, sai ya ɗauke ta. To yaya za ka yi, ba za ka yi fushi ba? Ai
ba zai yiwu ba a hana ka abin da ba ya yiwuwa. Don haka sai dai a ce, cewar,
"Kada ka yi fushi!" yana da ma'ana guda biyu: Waɗansu suka ce ma'anar da za mu iya bayarwa wajen,
"Kada ka yi fushi!" shi ne ka siffanta da halaye nagari, kamar
karamci, da afuwa, da yawan haƙuri,
da yawan kyauta, kar ka zamanto marowaci. To idan ka siffantu da wannan
siffofin, su ne za su taimaka maka, su rika rage maka yawan fushi, in ba ka da
su kuwa, dole ka yi fushi. Saboda Annabi (ﷺ)
ya ce, "Kada ka yi fushi!" kamar yana nufin ka siffantu da ɗabi'u nagari, irin ɗabi’un
da suke rage fushi.
Ma‘ana ta biyu suka ce, abin da ake nufi da
"Kada ka yi fushi!" shi ne, kada ka yi aiki da fushi in ya zo maka,
kar ka zartar da hukunci kana cikin fushi. Domin idan fushi ya yi yawa, ƙila
ka zo ka cewa matarka, ka sake ta saki uku! daga baya ka zo kana ta bin malamai
kana fatawa. Don haka duk abin da fushi ya shawarce ka, ka yi, kar ka yi aiki
da wannan abin, ka nisance shi, ka zamanto
mai haƙuri,
mai juriya. [Don ganin ƙarin bayani
duba: Jami'ul Ulum Wal Hikam Na Ibnu Rajab 1/373-374]
Wannan wasiyya ta Annabi (ﷺ)
ta shafi dukkan dangogin ayyuka na alheri. Kamar yadda malamai suka ce, wannan
yana cikin Jawami’ul Kalim da aka ba wa Annabi (ﷺ).
Wato jumla guda ɗaya,
amma za ta ɗauki ma‘ana mai ɗimbin yawa, domin za ta shiga cikin kowane ɓangare na rayuwa. Domin fushi yana iya sa ka yi abu
ba don Allah ba, sai ya zamanto ba ka samu lada ba wajen Allah.
Wane mutum ne yazo wurin manzon Allah (SAW) don niman wasiya?
ReplyDelete