An karɓo
daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Lallai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da kuma ranar ƙarshe,
ya fadi alheri ko ya yi shiru, wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe,
to ya girmama maƙocinsa, wanda ya
kasance ya yi imani da Allah da ranar ƙarshe,
to ya girmama baƙonsa."
Bukhari (#6018) da Muslim (#48) suka rawaito.
SHARHI
Saƙo
uku wannan hadisin yake ɗauke
da su: Kama harshe; kar mutum ya yarda ya furta magana, sai cikin abin da yake
akwai maslaha ta addini ko ta duniya. Maslahar addini,
ita ce abin ya kasance
zikiri ne, ko salatin Annabi (ﷺ) ne, ko karatu ne, ko
hailala ne, ko istigafari, ko tasbihi. Ko kuma ya kasance abu ne da yake da alaƙa
da duniya. Harkar kasuwanci ne za ka ƙulla,
wannan ya halatta ka furta da bakinka. Amma duk abin da ya fita daga wannan,
abin da zai danganci sharri, to kamata ya yi musulmi ya kame harshensa.
Abu na biyu kuwa cikin saƙon
da wannan hadisin yake ɗauke
da shi, shi ne ya kasance mutum ya kula da maƙocinsa:
Maƙocin
nan kuwa, ko da ba musulmi ba ne. Saboda maƙoci
nau'i uku ne; Akwai mai haƙƙi
uku a kanka, akwai mai haƙƙi
biyu, akwai mai haƙƙi
ɗaya. Maƙoci
mai haƙƙi
uku a kanka, shi ne ga shi musulmi, ga shi kuma maƙoci,
ga shi kuma akwai dangantaka ta jini a tsakaninka da shi, wanka ne, ko ƙaninka,
ko ɗan wanka, ko ɗan ƙaninka,
akwai dai alaƙa ta jini tsakaninka da
shi. Ma'ana dai, ga haƙƙin
maƙwabtaka,
ga haƙƙin
musulunci, ga haƙƙi
na dangantaka da ke tsakaninku. Ka ga haƙƙi
uku kenan! Maihaƙƙi
biyu kuma a kanka, shi ne haƙƙin
maƙotaka
da haƙƙin
musulunci, amma ba alaƙar jini
tsakaninka da shi. Mai haƙƙi
ɗaya, shi ne haƙƙin
maƙotaka
kaɗai, don shi ba musulmi
ba ne, ba kuma dangantakar jini tsakaninku. To kowanne daga ciki, ana buƙatar
a kyautata masa. Kowanne daga ciki idan ka yi wani abu na ihsani, ya halatta ka
yi masa: Idan ka fitar da sadaƙa
ta nafila, ko da mutum ba musulmi ba ne, ya halatta ka ba shi sadaƙar
nafila, amma sadaka ta wajibi, ta zakka, ita kuwa dole sai musulmi.
Abu
na uku da wannan hadisin yake ɗauke
da shi, shi ne kyautatawa baƙo
lokacin da ya ziyarce ka, lokacin da ya zo wurinka daga wani gari.
No comments:
Post a Comment