GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 27, 2021

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Uku 13)

Neman Tsarin Wanin         Allah Shirka Ne

 

Da faɗin Allah:

"Lallai daga cikin mazaje na mutane, akwai waɗanda suke neman kariya ko tsari daga wurin mazaje na aljanu. Sai suka kara musu (aljanu) shisshigi da girman kai." (Al-Jinn: 6)

______________

SHARHI

Abin da malaman tafsiri suke faɗa shi ne Larabawa a jahiliyyarsu, idan suka yi tafiya, suka isa masauki, don jin tsoron kada wani abu ya same su, ko dawakansu, ko raƙumansu, sai su ce suna neman tsari da shugaban wannan wuri, ya kare su daga dukkan mai cutarwa a wannan wajen. Suna nufin shugaban aljanun wajen ya kare su daga

sauran aljanun wajen.

Wannan ya sa sarkin aljanun wajen, sai ya riƙa cewa, "Ashe bayan aljanu ma, mutane na tsoro na." Sai wannan ya ƙara masa girman kai. Ka ga a nan Ubangiji ya kawo wannan aya da ba da labarin waɗansu mutane da ke neman tsarin aljan.

Ya uuzuna: Isti'aza ibada ce, don haka ba a nemanta sai a wurin Allah. Shi ne Ibn Kathir yake cewa, ayoyi ne 3 ba su da na 4 cikin Alkur'ani da suke nuna haka. Akwai kangararrun shaiɗan, akwai na bil Adama. Kangararrun bil Adama, mai munin hali, yadda za ka magance mummunan halinsa, shi ne ka yi masa ɗabi'a kyakkyawa. Idan ya yi maka rowa, sai ka yi masa kyauta, in dai yana nan bai canza ba, to dole zai

sauko. Amma kangararren shaiɗan kuwa, babu yadda za ka yi da shi, wannan sai dai ka nemi tsarin Allah da shi. Wannan ya nuna ibada ce Isti'aza. Don haka, dole a nemi tsari a wurin Allah, in dai aka nema wurin aljan, mala'ika, Annabi, ko shaihi, ko wani waliyyi, to an yi shirka. Duk wanda za ka nemi ya kare ka daga abin da kake jin tsoro, to wannan din bawa yake ga Allah. Kuma Allah (SWA) ya yi umarni da isti'aza, kamar yadda ya yi umarni da sallah. Ƙololuwar martaba kafin ka ambaci sauran Annabawa da mala'iku, bayi ne kuma mabukata ne wurin Allah (SWA). Su kansu Annabawa ba su nemi tsari ga kansu ba, sai ga Allah. Annabi Nuhu (AWS) ya nemi tsari ga Allah;

Ya ce 'Ya Ubangjina lalle ne ni ina neman tsari gare ka, kada in tambaye ka abin da ba ni da wani ilimi a kansa. Idan ba ka gafarta mini ba, kuma ka yi mini rahama, zan kasance daga masu hasara." (Hud:47)

Sakamakon da Allah ya yi masa saboda isti'azarsa, shi ne aka yi sakamakon da ya shafi jama'arsa:

"Aka ce da Nuh, sauka cikin jirgi cike da aminci (babu jin tsoro); da albarkatai masu tarin yawa gare ka, har waɗanda suke tare da kai (cikin jirgin), har waɗanda za su biyo baya." (Hud:48)

Annabi Yusuf (ASW) lokacin da matar nan ta nemi ya aikata alfasha da ita, cewa ya yi, Ina neman tsari ga Allah!" Sai Allah (SWA) ya yi masa sakamako da Burhani.

Mahaifiyar Annabi Isa (ASW), lokacin da mala'ika Jibril (ASW) ya zo wurinta, isti'aza ta yi. Da ta yi haka, sai aka ba ta ɗa. Ba wai kyautar ɗan ne ya fi daɗi ba, ɗan ya yi magana yana jariri. Don, idan an ba ta ɗan bai yi magana ba, za a tuhumce ta da zina. Lókacin da ta zo da shi, sai suka tambaye ta ina ta samo ɗa? Sai ta nuna shi. Suka ce, "Yaya za a yi mu yi magana da jariri?" Sai ya yi magana. Ba wai barrantar da ita kaɗai ya yi ba, sai ma da ya ƙara ba su labarin shi manzo ne. Ka ga sakamakon

Isti'aza kenan. Annabi ( SAW) ma an umarce shi da yin isti'aza. Ka dubi Suuratul Falak da Naas. Don a nuna babu wanda ya cancanta a yi isti'aza da sunansa, sai Rabbil Falak, sai Rabbin-Naas. To, wanene a cikin

mala'ika ko Annabi zai zama Rabbil Falak ko Rabbin-Naas ?

********************************************

 

An karɓo hadisi daga Khaulatu 'yar Hakim (RA), ta ce, "Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa, "Wanda duk ya sauka a wani masauki, sai ya ce, (A uzu bi kalimatul-lahit-tammati min sharri ma Khalaƙ ina neman kariya da kalmomin Allah cikakku daga sharrin abin halitta (ma'abocin sharri). Duk wanda ya faɗi haka babu abin da

zai cutar da shi har sai ya bar wurin ya ci gaba." [Muslim #27008]

________________

SHARHI

Haulatu bintu Hakim: Ita ce matar da ta zo ta gabatar da kanta wurin Manzon Allah (SAW) ta ce, ""Na ba ka kaina." Sai Manzon Allah (SAW) ya yi shiru bai ce komai ba, sai wani sahabi ya ce da Manzon Allah (SAW), "Ya

Rasulullah! Idan ba ka da buƙata, mu muna da buƙata." Sai Annabi ya ce.

"Ka kawo sadaki." Ya ce, ba shi da komai. Sai Annabi ya sake cewa, "Ka je ka bincika." Sai ya dawo ya ce ba shi da komai sai mayafinsa. Sai Annabi ya ce, "Ka haddace wani abu daga Alƙur'ani? Ya ce, "Eh!" Sai Annabi ya ce da shi, "Ka je ka karantar da ita. Wannan shi ne sadakinka."(Bukhari)

A uzu bi kalimatul-lahit-tamati min sharí ma khalaƙ:

muna neman tsari da kalmomin Allah cikakku? Shi ne malamai suka ce, kalmomin Allah su ne maganar Allah, kuma maganar Allah siffa ce daga cikin sifofinsa. Idan ka nemi tsari daga maganar Allah, ka nemi tsarī ga Allah (SWA) kenan. Ma'anar cikakku wato, duk inda kalmar Allah take, cikakkiya ce. Kasancewar maganar Allah duk inda ya faɗa ba ya sabawa, shi ya sa ta zama cikakkiya kenan. Amma akwai ruwaya cikin Bukhari, wanda Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab ya kamata a ce ya gabatar da ita. Bisa ka'ida, idan hadisi Bukhari da Muslim sun kawo shi, kamata ya yi a fara gabatar da na Bukhari. Hadisin da ke cikin Bukhari [#3371] na Abdullahi ibn Abbas ne, ya ce, Annabi (SAW) ya kasance yana yi wa Hassan da Hussain isti 'aza, sai ya ce da su, "Kakanku Ibrahim ya kasance yana yin isti'aza ga 'ya'yansa guda biyu, Isma'il da Ishaƙ. Abin da yake cewa

kuwa, A 'uzu bi kalimatullahit-taammati min kulli shaiɗanin wa hamma, wa min kulli ainin lammat. "Wato, ina neman tsari da kalmomin Allah cikakku daga dukkan wani shaiɗan ma'abocin dafi da mai kambun

bakan da ke nufatar mutum da sharri. Mahalush-shahid a nan, shi ne Annabi (SAW) ya ba da umarnin cewa a nemi tsari ga Allah da kalmomin Allah cikakku, wato maganganun Allah (SWA) kenan. Alƙur'ani na cikinsu

da duk wata magana da Allah ya yi, za ka karanta ne babu adadi, ko sau nawa ka faɗa ya yi. Domin abin da Annabi (SAW) bai iyakance masa adadi ba, to ba a yi masa iyaka, kuma abin da ya iyakance, ba a kara masa.

********************************************

 

A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:

1. Tafsirin ayar Suuratul Jinn.

2. Neman tsari ga wani ba Allah ba, shirka ne.

3. Kafa hujja da wannan hadisin Annabi. Domin malaman suna kafa hujja da hadisin cewa kalmomin Allah ba halitta ba ne (sifa ce daga cikin sifofinsa), suka ce (in da maganar Allah halitta ce), to idan aka nemi tsari da halitta, kuma wannan shirka ne.

4. Falalar wannan addu'ar duk da cewa gajeriya ce.

5. Kasancewar abu ana iya samun amfanin duniya, wajen kare sharri ko jawo amfani, wannan ba ya nuna cewa ba shirka ba ne.


(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...