GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Jul 13, 2022

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Hudu14)

 Yana Daga Shirka Neman Taimakon Wanin Allah Ko Roƙon Wanin Allah

________________

SHARHI

Mun riga mun san duk wani nau'in ibada da ake yi wa Allah (SWA), to idan a ka yi wa wani ba Allah ba, to ya zama shirka kenan. A nan Malam ya ce neman tsari wato istigatha" da wanin Allah shirka ne, kenan istigatha' ibada ne wanda ba wanda za a yi wa sai Allah. Kuma kamar yadda Allah ya yi umarni da sallah haka ya yi umarni da istigatha'wato neman tsari, kamar yadda ya ce:

"Idan wani mai zungura daga shaiɗan ya zungureka to ka nemi tsari daga wajen Allah, haƙiƙa shi (Allah) mai ji ne kuma masani." (Fussilat:36)

Don haka neman tsari ibada ce ba a yi da kowa

 sai Allah (SWA). Idan aka nema a wajen wani waliyyi, ko Annabi, ko mala'ika ko aljani to duk an nema wajen wanin Allah, duk an yi shirka. Da mala'iku da Annabawa dukkansu bayi ne na Allah, ayoyi da dama sun tabbatar da haka. Tunda bayi ne su to, suna neman buƙata wajen Allah. Su kansu Annabawa neman tsari da Allah suke yi, ba sa yi da kansu. Annabi Nuhu (ASW) ya nemi tsarin Allah a cikin Suuratul Hud, Allah ya tserar da shi da wadanda suke jirgin ruwa tare da shi albarkacin neman tsarin Allah da ya yi. Haka Annabi Yusuf (ASW) ya nemi tsarin Allah da matar sarki ta neme shi kamar

yadda ya zo cikin Suuratul Yuusuf Haka mahaifiyar Annabi Isa (ASW) Nana Maryam ta nemi tsari da Allah lokacin da mala'ika ya zo mata. To Annabi (SAW) an umarce shi da istigatha a cikin Suuratul Falaƙi da Naas.

Shi ne Ibnul Ƙayyim yake cewa rukunan istagatha'guda uku ne.

a. Abin neman tsarin wato Allah (SWA) kenan kamar yadda muka tabbatar shi kaɗai ne,

b. Abin sharrin da ake neman tsarin Allah daga gare shi, waɗannan su ne abubuwan nan hudu wanda Suuratul Falaki ta yi bayaninsu kamar haka:

Ka ce, Ina neman tsari a wajen Ubangijin safiya. Daga sharrin

abin da ya halitta (ma'abocin sharri), kuma daga sharrin dare,

idan ya yi ɗuhu. Kuma daga sharrin masu tofi a cikin ƙulle-

ƙulle. Kuma daga sharrin mai hassada, idan zai yi hassada."

(Falaƙ:1-5)

Dukkan wani abin sharri yana cikinsu. Na farko tsari daga

dukkan abin da Allah ya halitta na sharri, ba za ka ce dukkan

abin da Allah ya halitta ba, saboda ba duk halittarsa ba ce take da sharri, kamar aljanna ba sharri a cikinta. Sai na biyu, dare idan duhunsa ya zo. Aljanu karfinsu ya fi da daddare a kan rana, sannan an fi jin tsoro da daddare a kan rana. Sai na uku masu tofi cikin ƙulle-ƙulle wato masu tsafi kenan da masu

sihiri. Sai na huɗu mai hassada yayin da zai yi hassadar.

c. Sai na uku shi ne lafazin da manzon Allah ya yi amfani da shi wajen neman tsarin.

****************************************

 

Da faɗar Allah:

"Kada ka roƙi wanin Allah abin da ba ya iya amfanar da kai ko cutar da kai. Idan ka aikata haka, to ka shiga cikin azzalumai (ka zamanto cikin masu shirka kenan.) Idan Allah ya shafe ka da wata cutarwa, babu mai yaye maka (cutar) sai Allah. Idan kuma Allah ya nuface ka da wani alheri, babu wanda ya isa ya juyar da alherin. Ubangiji na isar da alherinsa ga wanda ya so cikin bayinsa. Domin shi mai gafara ne mai jinkai."(Yunus 106-107)

____________________

SHARHI

Wannan ayar tana nuna mana cewa ba wanda yake cuta ko amfanarwa sai Allah (SWA), haka Allah ya umarci Annabi da ya yi shela ya faɗa:

"Ka ce, Ni fa ba zan iya mallaka muku wata cutarwa ko kuma shiriya ba Ka ce, "Ba fa wani wanda ya isa ya tserar da ni daga Allah, kuma ba zan taba samun wata mafaka ba, in ba a wurinsa ba." (Jinn:21-22)

To idan har Annabi ba shi da mukullan, to ba yadda za a yi a samu a hannun wani. Shi ya sa Allah (SWA) ya ce idan har ka aikata haka to ka shiga cikin azzalumai. A nan kuma zalunci yana nufin kafirci. To Allah ya ce kar ka kira wani ba Allah ba, ko mala'ika ne, ko Annabi ne, ko aljani ne, in dai ba Allah ba ne to ba ya halatta ka kirawo shi domin ya amfanar da kai ko ya kare ka daga masifa. Wannan maganar Allah ya fuskantar da ita zuwa ga annabinsa amma abin nufi shi ne zuwa daidaikun al'umarsa tun da Allah ya san annabinsa ba zai yi shirka ba. An jigina magana zuwa gare shi don mu ta tsoratar da mu kwarai da gaske. Don haka kiran wani ba Allah ba, ɗaukar wani haƙƙi ne na Allah kaɗai, ka ba wa wanin Allah, wannan babban zalunci ne da ba sama da shi.

 

****************************

Da faɗinsa:

"Ku nemi arziƙi a wurin Allah kaɗai, kuma ku bauta masa, kuma ku gode masa, gare shi za ku koma." (Al-Ankabuut: 17)

_______________________

SHARHI

Ayar ta zo cikin ƙissar Annabi Ibrahim (ASW) cikin Suuratul Ankabul Allah (SWA) cewa ya yi, "Ku nemi arziƙi wajen Allah kaɗai." Wato wan bai shigo ciki ba. Amma da cewa aka yi, "Ku nemi arziki wajen Allah wannan bai hana ku nema wajen waninsa ba.

******************************

Da faɗinsa:

"Babu wanda ya fi kowa ɓata, sama da wanda yake kiran wanin Allah, wanda ba zai taɓa amsa masa ba har zuwa ranar alƙiyama, Kuma su (waɗanda aka kira) dangane da kiran, gafalallu ne (wato ba su san anyi ba)

_________________

SHARHI

Ƙarshen ayar shi ne:

Idan an tara mutane za su kasance maƙiya gare su kuma za su kafircewa ibadunsu."(Al-Ahkaaf:6)

A ranar kiyama waɗanda suka ɓatar da mutane za su yi tawaye da mutanen da suka ɓatar. Suna cewa mabiyansu sam ba mu yarda da ibadar da kuka yi mana ba, mu ba mu ce ku bautata mana ba, ba mu ce ku roƙe mu ba, ba mu da komai, matattu muke, me ya sa kuka roƙe mu? Wallahi

sai sun faɗi haka ranar tashin ƙiyama! Haka Allah ya kawo wannan ƙissar a cikin ayoyi daban-daban a Alƙur'ani:

Tuna (abin da zai faru) lokacin da waɗanda aka yi wa biyayya, suka barranta daga waɗanda suka yi musu biyayya, (bayan) sun ga azaba, sai dukkan wata dangantaka (da take a tsakaninsu) ta yanke. Kuma waɗanda suka yi biyayyar za su riƙa cewa, "Ina ma muna da damar (a mayar da mu

Duniya), mu ma mu barranta daga gare su (a duniya), kamar yadda suka barranta daga gare mu (a yau)?" Kamar haka ne Allah zai nuna musu ayyukan su, (a matsayin) abin yin nadama gare su. Da ɗai, ba za su zamo masu fita daga cikin wuta ba." (Al-Baƙara:166-167)

Waɗanda aka bi za su barranta daga waɗanda suka bi su don sun ga azaba ƙiri da muzu, sannan dukkan wani sababi da aka sa na kusa wane muridi ne, duk za su yanke a ranar. Su kuma mabiya za su ce ina ma a mai samu duniya  mu yi musu tawaye kamar yadda su wane suka yi ta wayen tun a duniyar, mu ma mu yi musu tawaye tun da yau su ma sun yi mana tawayen. Sai Allah ya ce haka za mu nuna musu aikin su abin damuwa abin baƙin ciki.

A wani wajen Allah (SWA) yake ba da labari, idan an wulla mabiya cikin wuta sai su nuna shugabanni su ce ya Allah waɗannan su suka ɓatar da mu, ninka musu azabar wuta su ne manyan masu laifin. Sai Allah (SWA) ya ce "kowa sai an ninka masa." Don haka duk wanda za ka bi ka tabbatar

ya sa ka bin Allah da Annabi (SAW). Duk wanda ya ce ma rufe ido ka bi ni kar ka yarda. Don babu tsoron Allah a wajen dan bidi'a, abin da yake kallo kawai duniyarsa, ya za a yi ya kare matsayinsa. Masu sufancin da, su suka gina sufancinsu a kan tsoron Allah. Amma sufayan yanzu galibin su karya suke. Sufayen da, irinsu Sahal ibn Abdullahi Tusturi, irinsu

Junaid ibn Muhammad Alkawariri, irinsu Shehu Abdulkadir Aljilani waɗannan duk da gaske suke, tarihinsu da maganganunsu da ayyukansu duk ya nuna da gaske suke yi. Amma sufayen karshen zamani ba wanda yake da gaske cikinsu, ba wanda yake kira kan bin tafarkin Manzon Allah. Suna fakewa ne da Annabi don a bi su su gina kansu.

********************************

 

Da faɗinsa

"Shin wanene yake amsawa wanda yake cikin matsí idan ya kira shi.

kuma ya yaye cuta?"(An-Naml 62)

_______________

SHARHI

Duk waɗannan ayoyin suna nuna cewa, ba za a nemi taimakon kowa ba, ko a nemi kariyarsa, in ba Allah (SWA) ba.

 

********************************

Ɗabarani [Ahmad J5/317] yaruwaito hadisi da sanadinsa

cewa, akwai wani munafuki lokacin Annabí (SAW) wanda yake cutar da muminai. Sai wani sashi na muminai suka ce, "Mu tafi wurin Manzon Allah, mu nemi taimakonsa don ya kare mu daga sharrin wannan munafukin." Sai ya ce, "Ai ba a neman agaji da ni, sai dai a wurin Allah."

_______________________

SHARHI

Wannan hadisi mai rauni ne, amma hukuncin ciki ya tabbata a ayoyın da suka gabata.

**********************************************

A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:

 

1. Kawo addu'a bayan an kawo maganar neman taimako, yana

cikin babin ambaton gamammen abu, bayan an ambaci

keɓantacce.

2. Tafsirin ayar "Kada ka roƙi wanin Allah...."

3. Kiran wanin Allah babbar shirka ce.

4, Mafi nagarta a cikin mutane da a ce zai aikata kuma ya yarda da hakan (kiran wanin Allah), da zai zamanto cikin

azzalumai.

5. Tafsirin ayar da ta biyo bayan wannan.

6. Kasancewar (kiran wanin Allah) ba ya amfani a duniya, tare

da kasancewar hakan kafirci ne.

7. Tafsirin aya ta uku.

8. Neman arziki ba ya dacewa, sai wurin Allah kaɗai kamar

yadda Aljanna ba a nemanta sai wurinsa.

9. Tafsirin aya ta hudu.

10. Babu wani mafi bata (a ban-kasa) sai wanda ya kira wanin

Allah.

11. Shi wanda ake kira gafalalle ne ga kiran mai kira ɗin, bai san yana yi ba.

12. Kiran wani wanda ba Allah ba, zai sanya ƙiyayya ga wanda

ake kira (a gobe ƙiyama).

13. Yadda aka ambaci kiran wanin Allah da cewa ibada ne ga

wanda aka kira din.

14. Wanda ake kira zai bijire wa wannan kiran (da aka yi masa a gobe ƙiyama). Waɗannan al'amura (da aka ambata) su ne suke sanya wanda ya kira wanin Allah ya zamanto mafi ɓata daga mutane.

16. Tafsirin aya ta biyar

17, Wani al'amari mai ban mamaki shi ne ta yadda ko da

waɗanda suke bautar gumaka, sun yi iƙirari cewa babu mai

amsa wa wanda yake cikin tsanani sai Allah. Don haka

suke kiran Allah idan suna cikin tsanani.

18. Yadda Annabi (SAW) yake ba da kariya game da bangon

tauhidi da kuma yadda ladabinsa yake game da Ubangiji.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...