GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Oct 17, 2021

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyu 12)

Yin Bakance Don Wanin Allah Shirka Ne


Da fadin Allah;

"(Muminai nagari) suna cika bakance..(¹) "(Al-Insaan :7)

____________________

SHARHI

Wannan ayar ta nuna bakance ibada ce. In kuwa ibada ce, yin ta ga wanin Allah ya zama

shirka kenan.

********************************************

 

Da fadinsa;

"Lallai duk abin da za ku ciyar na daga ciyarwa, ko abin da kuka yi

bakance na daga dangin bakance, to lallai Ubangiji ya san kun yi... (²) (A-Bakara:270)

____________________

SHARHI

Shi ne Ibn Kathir yake cewa, a cikin wannan ayar akwai alƙawari na sa rai, sannan akwai alƙawari na firgici, wato waɗanda suka yi ciyarwa ko cika bakance da kyakkyawar niyya, to Allah (SWA) ya san da abin, zai ba su lada. Sannan kuma razani da firgici ga waɗanda suka yi ciyarwar ko cika bakancen nan domin wanin Allah, to Allah ya san da abin, kuma zai musu mummunan sakamako a kai.

 

***********************************************

Ya tabbata cikin Sahihul Bukhari, an karɓo hadisi daga Aisha (RA), Annabi (SAW) ya ce, "Wanda ya yi bakancen biyayya ga Allah, to lallai ya bi shi, wanda kuma ya yi bakance zai saɓa wa Allah, to kada ya yi." [Bukhari #6696, Abu Dawud#3289, Timizi #1526]

_____________________

SHARHI

Ta yaya bakance zai zama na sabo? Ko dai mutum ya yi bakance don wanin Allah, ko kuma ya yi bakance don Allah, amma wurin cika bakancen ana saɓa wa Allah. A irin wannan, dole ne cika bakance, amma sai dai ba zai cika shi a wannan wurin ba. Don cika shi a wurin ya zama saɓo kenan. Duk wanda ya yi bakance na saɓo, ba zai cika shi ba, to wannan bakancen ya zama ba shi, sai dai zai yi kaffarar rantsuwa.

 

******************************************

 

A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:

1. Wajabcin cika bakance, (idan ba saɓon Allah ba ne).

2. Idan bakance ya kasance ibada ce, to juyar da shi ga wanin Allah ya zama shirka.

3. Bakancen da aka yi wanda ya ƙunshi saɓo, ba ya halatta a cika shi.


(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...