An karɓo
daga Abu Amrin ko Abi Amrata, Sufyanu ɗan
Abdullahi (R.A) ya ce, "Na ce, "Ya Manzon Allah (ﷺ)!
Faɗa min wata magana a
cikin addinin musulunci, wadda ba zan sake tambayar waninka ba game da
ita." Sai ya ce, "Ka ce, "Na yi imani da Allah." sannan
kuma ka daidaitu." Muslim (#38) ya rawaito.
SHARHI
yana da rukunai guda shida, waɗanda muka yi bayaninsu a cikin hadisi na biyu, a jerin hadisan wannan littafi mai albarka. Sannan kuma da sauran abubuwan da imani ba ya cika sai da su, duk yana cikin, "Na yi imani da Allah...." Daidaituwa kuwa, a nan tana nufin daidaituwa a kan tafarki madaidaici: Kada ka ƙara, kada ka rage kan abin da shari'a ta dora ma, ka nisanci dangogin abubuwan da aka haramta maka, ka yi ƙoƙarin neman halal a cikin dukkanin al'amuran da za ka yi. Wannan shi ne daidaito. Duk mutumin da ya dace da waɗannan abubuwa guda biyu, ga imani ga daidaito, to shi kenan sai aljanna. Shi ya sa Annabi (ﷺ) da kansa, aka umarce shi da daidaito, aka ce masa (Ka daidaita kamar yadda aka umarce ka). [Hud 112].
Thanks
ReplyDelete