An karɓo
daga Abu Mas'ud, Uƙbatu ɗan Amru Al AnsaIriy Albadariy (R.A) ya ce, Manzon
Allah (ﷺ)
ya ce, "Yana daga cikin abin da mutane suka riska daga zancen Annabtar
farko, idan har ka zamto ba ka jin kunya, to ka aikata duk abin da ka so.“ Bukhari(#3483).
SHARHI
Wannan hadisi abin da yake nunawa, kamar yadda
malamai suke nunawa, shi ne cewa wannan hadisi kamar razanarwa yake, ba wai
umami yake ka zama marar kunya ba, a'a! in
dai ka zamanto halinka ne rashin
kunya, je ka ka aikata duk abin da ka ga dama, Ubangiji zai maka sakamako.
Umarni ne amma kamar razanarwa yake, kamar yadda Allah yake cewa( Ku aikata duk abin da kuke so, (ai Allah) yana ganin abin da kuke aikatawa). [Fussilat: 40] Wannan zai zamto razanarwa ne Ubangiji Ta'ala yake. Wannan hadisi Imamul Bukhari ya rawaito shi, haka Imamu Malik ɗan Anas ya rawaito shi a cikin Muwaɗɗa. Da ya tashi rawaito wannan hadisi, sai ya haɗa su babi ɗaya da hadisin Annabi (ﷺ) da ke cewa, "Mu taron Annabawa an umarce mu da jinkirta sahur, kar mu yi sahur, sai ƙarshen dare. An umarce mu da gaggauta buɗa baki, da zarar rana ta faɗi, kar mu tsaya wani abu, mu yi buɗa baki. Sannan, an umarce mu da mu ɗora hannun dama a kan na hagu." sai ya kawo wannan badisi tare da wannan, saboda abin da wancan hadisi yake ɗauke da shi, da abin da wannan hadisi yake ɗauke da shi, wani abu ne da dukkan taron Annabawa sun yi ijma'i a kai, ba wanda ya saɓa. Duk taron Annabawa haka suke gaggauta sahur, su jinkirta buɗa baki, su ɗora hannun dama a kan hannun hagu a cikin sallah. Duk Annabawa ba wanda ya saɓa, duk taron Annabawa sun faɗi wannan kalma, ba Annabin da ya saɓa a kan wannan. Wannan hadisi yana nuna falalar kunya. Malamai sun ce kunya iri biyu ce: Akwai abin da yake siffa ta halitta, wani za a haife shi da jin kunya, to wannan baiwa ce daga Allah Ta'ala. Na biyu kuma akwai kunya wadda yake mutum ne yake yunƙuri ya samu, da ba shi da ita, yanzu yake ƙoƙarin ya koya, to wannan ta fi waccan lada, saboda ba dabi'ar ka ce jin kunya ba, sai ka samu hadisai sun faɗakar da kai a kan ka zama mai jin kunya, sai ka yi yunƙurin za ka zama mai jin kunya da ƙafi da yaji, yau ka yi, gobe ka yi, jibi ma ka yi, har ya zamanto ka saba wa jikinka, ka rinƙa jin kunya. To wannan wata falala ce mai girman gaske, shi ya sa Annabi (ﷺ) ya ga wani sahabi yana yi wa ɗan uwansa wa'azi, kai wane ka fiye jin kunya, sai ya ce da shi, "Kyale shi, ai kunya alheri ce!" [Bukhari (#24) da Muslim (#36)] A wata riwayar wani hadisin daban Annabi (ﷺ) cewa ya yi, "Kunya ba ta kawo komai sai alheri!" [Bukhari (#6117) da Muslim (36)] A inda kunya take zama abin zargi, shi ne ka jahilci wani abu na wajibi da shari'a ta ɗora ma, amma kunya ta hana ka tambaya. A nan ba a yarda ba ka zama mai jin kunya. A babin addini, kana so ka tambayi hukunci, to babu jin kunya. In har kana ganin-ba za ka iya tambaya ba, to sa wani ya tambayar maka, idan ba za ka iya sa wani ba, rubuta ka yi tambaya ɗin, in ba ka son ka fito fili a gan ka. Dole dai ka san yadda za ka yi ka yi tambayar addini. Saboda hadisin Aliyu ɗan Abi Dalib (R.A) ya kasance yana yawan maziyyi, ɗan abu kaɗan zai faru, sai maziyyi ya fita daga jikinsa, sai yake son ya tambayi Annabi (ﷺ) hukuncinsa, amma kuma akwai surukuntaka tsakaninsa da Annabi (ﷺ) don yana auren Faɗima, sai ya ce Mikdad ɗan Aswad, ya ce, "Tambayi Annabi (ﷺ) meye hukuncin mutumin da ke yawan maziyyi?" Shi kuma ya koma gefe, aka ba da fatawa, shi kenan ya ji. [Duba Bukhari (#132) da Muslim (#303) da sauransu].
No comments:
Post a Comment