An karɓo
daga Abu Malik, Haris bin Asim Al ash’ariy ya ce, Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Tsarki rabin imani ne, faɗin
Subhanallahi Walhamdulillahi; tana cika mizani, faɗin Subhanallahi da Alhamdulillahi; suna cika, ko
(kowace ɗaya daga cikinsu) tana
cika abin da ke tsakanin sama da ƙasa;
sallah haske ce; sadaƙa huija ce; haƙuri
kuma haske ne; Alƙur'ani hujja ne
gare ka, ko a kanka. Dukkan mutane suna jijjifi da safe, daga cikinsu akwai mai
zuwa sayar da kansa, ko dai ya 'yantar da kansa ko kuma ya halakar da
kansa." Muslim (#223) ya rawaito.“
SHARHI
Da Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "Tsarki rabin imani ne...." magana mafi inganci dangane da
'tsarki', shi ne abin da
hankula ke zuwa gare shi da zarar an ambaci kalmar
'tsarki’, kamar alwala da wanka da taimama. Waɗannan
su ne ake kira da suna 'tsarki'. cewa tsarki rabin imani ne, akwai maganganu da
yawa a kan hakan: Ko dai mu fassara imani mu ce shi ne sallah, sai ya zamanto
tsarki shi ne rabin sallah. Masu wannan magana suka ce, saboda sallah an sa
mata suna imani a cikin Alkur'ani, (Ai Allah ba zai tozarta muku imaninku ba.)
[Al-Bakara: I43]
Imani a cikin wannan aya ana nufin sallah. Don haka
Bukhari ya kawo wannan hadisi a cikin babin da yake nuna cewa imani shi ne
sallah. Sai suka ce tsarki rabin sallah ne, saboda ba za ka yi sallah ba, sai
da tsarki: Tsarkin nan wanda ya danganci wanka ne, alwala ne, duka biyun ne,
taimama ne, sai dai da tsarki ake yin sallah, sai fa in wani uzuri ya hana ka
dukkan waɗannan.
Imani shi ne ƙuduri
kyakkyawa a cikin zuciya dangane da kaɗaitakar
Allah, da Manzanni da sauran duk abin da ake faɗa.
To ɗan Adam Bangare biyu
gare shi: ɓangaren jiki da ɓangaren zuciya. Imani zai tsarkake ɗaya ɓangaren
na ɗan Adam, wato zuciya,
shi kuma tsarki wanda ya danganci alwala ko wanka zai tsarkake ɗaya ɓangaren
na ɗan Adam, wato gangar
jiki Sai ya zamanto da Imani da tsarki kowanne ya ɗauki rabi kenan!
Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, yawan maimaita lafazin Subhanallahi Walhamdulillahi, yana cika mizanin
awon ayyukan mutum a ranar tashin ƙiyama.
Wannan misali ne Annabi (ﷺ) yake bugawa. Ma'ana,
da a ce waɗannan kalmomi za
a yi halitta da su, da wannan halitta za ta iya cika mizani in an zo auna ta a
kan. mizani a ranar tashin ƙiyama.
Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....sadaƙa
hujja ce...." yana nufin hujja ce bisa ga cewa mutum yana da imani; hujja
ce bisa ga cewa mutum ya amsa umamin Allah; hujja ce bisa ga cewa ya yi yaƙi
da zuciyarsa. Sai kuma ya ce, "....haƙuri
kuma haske ne...." sannan ya ce, "....Alƙur’ani
hujja ne gare ka ko a kanka...." Ma'ana, yayin da duk ka tashi kafa hujja
a musulunce, to ya zamanto ka kafa hujja da Alƙur'ani
ko hadisin Annabi (ﷺ), in ba haka ba kuwa,
Alkur'ani ya zamanto hujja a kanka. Abin nufi, a ranar tashin alƙiyama,
in ba ka bi Allah da ma'aikinsa ba, Alƙur'ani
ya zama hujja a kanka. Sai kuma Annabi (ﷺ)
ya ce, ...Dukkan mutane suna jijjifi da safe...." suna wayar gari da safe,
"....daga cikinsu akwai mai zuwa ya sayar da kansa...." Ma'ana ya
Wayi gari wajen mummunan aiki kenan, akwai kuma wanda zai 'yantar da kansa.
Mutane kala biyu ne Wanda zai wayi gari cikin aikin ɓarna,
to shine mai sayar da kansa; ko wanda zai wayi gari cikin aikin alheri, to
wannan shi ne mai 'yantar da kansa.
جزاكم الله بأحسن خيره في الدنيا والآخرة
ReplyDelete