An karɓ0
daga Abu Abdullahi, Jabir ɗan
Abdullahi Al ansariy (R.A) ya ce, "Wani mutum ya tambayi Annabi (ﷺ)
ya ce da shi, "Ba ni labari idan na sallaci salloli na wajibi, na azumci
watan Ramadan, na halatta halal, na kuma haramta haram, ban ƙara
komai a kan haka ba, shin kuwa zan shiga Aljanna?" Sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "Eh! (za ka shiga aljanna).") Muslim (#15).
SHARHI
Abin da wannan hadisi yake nunawa, shi ne, idan
mutum zai tsaya a kanwajibi kaɗai,
ba tare da ya yi mustahabbi ko ɗaya
a rayuwarsa ba, in dai ya sauke dukkan wajiban da ake
buƙata,
zai samu shiga aljanna. Abin da wannan hadisi yake nunawa kenan! Don abin da ya
zana su ne, azumi da sallah, ya ce, "....idan na sallaci salloli na
wajibi, na azumci watan Ramadan..." shi kenan zan shiga aljanna? Annabi (ﷺ)
ya ce, za ka shiga aljanna.
Akwai hadisin da ya fi wannan fito da abubuwa fili
da ke cikin Sahihul Bukhari. Bukhari ya kawo shi a gurare daban daban, ɗaya daga cikinsu akwai wanda ya kawo a Kitabus Saum
(# 1891) da wani mutum ya zo wurin Annabi (ﷺ),
kansa ko hula babu, ga kansa da ƙura,
wanda hakan yake nuna kamar daga karkara yake, ya zi ya ce, "Me Allah ya
wajabta min na sallah?" Annabi (ﷺ)
ya cc, ”Salloli guda biyar, sai dai in ka ga dama ka yi nafila." Ya ce,
"Me ya wajabta min na zakka?" Ya ce, kaza da kaza, "Sai dai in
ka ga dama ka yi nafila." Ya ce, "Me ya wajabta min na azumi?” Ya ce,
"Ramadan. Sai dai in ka ga dama ka yi nafila." Annabi (ﷺ)
ya ba shi labarin shari'o'in musulunci, ya koyar da shi, ya sanar da shi,
sannan Annabi (ﷺ) ya gama wannan
bayani, sai wannan balarabe ya ce, "To na rantse da wanda ya aiko ka da
gaskiya! Ba zan ƙara ba, ba zan
rage ba." Ma'ana daga wajiban al'amuran da ka gaya min, lallai ba zan rage
ba, amma ba zan yi nafila ko ɗaya
ba. Sai ya tashi ya fita, sai Annabi (ﷺ)
ya ce, "In dai da gaske yake, zai shiga aljanna!" To wannan na nuna
mutumin da yake ya dakata a kan ayyukan wajibi, bai yi mustahabbi ba, wannan ba
za
a zarge shi ba. Imamun Nawawi ya ce, ma'anar,
"....na halatta halal na kuma
haramta
haram...." shi ne na aikata abin da yake halal tare da ƙudurcewa
Allah ne ya halatta min shi a zuciyata, kuma na nisanci haram tare da ƙudurcewa
Ubangiji ne ya haramta min wannan abin.
No comments:
Post a Comment