An karɓo
daga Abu Zarri Algifari (R.A) daga Annabi (ﷺ),
cikin abin da (Annabi) ke rawaitowa daga wurin Ubangijinsa. Lallai Allah Maɗaukakin sarki ya ce, "Ya ku bayina! Na haramta
wa kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a tsakaninku. Ya
ku bayina! Dukkaninku ɓatattu
ne, sai fa wanda na shiryar da shi, ku nemi shiryarwata, ni kuma in shiryar da
ku. Ya ku bayina! Dukkaninku mayunwata ne, sai wanda na ciyar da shi, don haka
ku nemi ciyarwata, ni kuma zan ciyar da ku. Ya ku bayina! Kowannenku tsirara
yake ba tufafi, sai wanda na suturta, ku nemi suturata, zan suturtar da ku. Ya
ku bayina! Kuna yin laifi dare da rana, ni kuma ina gafarta zunubai gaba ɗayansu, ku nemi gafarata, ni kuma zan yi muku gafara
ɗin nan. Ya ku bayina!
Ba ku i'sa ku cutar da ni ba, ballantana ku ce za ku cutar da ni, ba ku isa ku
amfanar da ni ba, ballantana ku ce za ku amfanar da ni. Ya ku bayina! Da a ce
na farkonku da na ƙarshenku, da
mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar wani mutum ɗaya cikinku mafi jin tsoron Allah, hakan ba zai kara
komai a cikin mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na ƙarshenku,
da mutanenku da aljanunku, ku kasance a bisa ga zuciyar mutum ɗaya mafi fajirci, hakan ba zai rage komai dangane da
mulkina ba. Ya ku bayina! Da a ce na farkonku da na
ƙarshenku,
da mutanenku da aljanunku, su tsaya a bigire ɗaya,
kowanne ya roƙe ni, ni kuma kowanne ɗaya daga cikinku in ba shi abin da ya roƙa,
hakan ba zai rage komai daga cikin abin da ke wurina ba, sai fa
gwargwadon abin da allura ta rage idan an tsoma ta
cikin ruwan teku. Ya ku bayina! Kaɗai
ayyukanku ne nake kididdiga su gare ku, sannan in cika muku ladanku. Wanda ya
samu alheri, ya gode wa Allah, wanda ya sami wanin haka, kar ya zargi kowa sai
kansa. Muslim (#2577) yarawaito.
SHARHI
Wannan hadisi ƙudusi
kenan, shi ma wahayi ne daga Allah. Bambancinsa da ayar Alƙur‘ani
shi ne, Alƙur'ani ana karanta shi
a cikin sallah, amma hadisi ƙudusi
ba zai yiwu ka karanta, ka yi sallah da shi ba, dole sai Alƙur'ani.
Duk da cewa kowanne daga Allah (SWA) yake. Ana samun lada ta hanyar tilawar Alƙur'ani
mai girma, an bautar da mu, mu karanta Alkur'ani mu sami lada, amma hadisul ƙudusi
ba haka ba ne. Alƙur'ani an ƙalubalanci
duniya da su kawo irinsa, an yi takara da shi, amma hadisul ƙudusi
ba a yi ƙalubale
da shi ba.
Akwai bambanci da waɗansu
suke faɗa, sai su ce Allah ya
yi alƙawarin
kare Alƙur'ani,
amma bai yi alƙawarin kare hadisul ƙudusi
ba. Wannan kuskure ne! Ubangiji Ta'ala ya yi alƙawarin
kare shari' ar musulunci, shari'ar musulunci kuma ita ce Alƙur'ani
da Sunna Yadda Allah ya yi alƙawarin
kare Alƙur'ani,
haka ya yi alƙawarin kare hadisi.
Dangane da faɗin
Allah (SWA) da ya zo a wannan hadisin cewa, "Ya ku bayina! Na haramta wa
kaina zalunci, kuma na sanya zalunci ya zama abin haramtawa a
tsakaninku...." wannan yana nufin, bai halatta wani ya zalunci wani a
cikinku ba, kada ku zalunci juna. Ubangiji ya haramta wa kansa zalunci a cikin
ayoyi da dama. Zalunci iri biyu ne: Na farko, shi ne zalunci mafi tsanani, wato
shirka, bauta wa wanin Allah. Domin asalin kalmar 'zalunci', tana nufin ka ɗauki wani abu ka sa shi a inda bai dace ba. To
lokacin da duk ka ɗau
wani abu wanda haƙƙi
ne na Allah, shi kaɗai,
sai ka bai wa wani bawa a cikin bayin Allah, to wannan zalunci na ƙarshe
kenan a duniya, kamar ka kirayi wani ba Allah ba. da nufin ya ba ka amfani, ko
ya koreɓmaka wata cuta. Don
haka Allah ya ce, (Kar ka kirayi wani wanda ba Allah ba, wanda ba shi cutar da
kai, ba shi iya amfanar da kai, idan kuwa ka aikata, to kai ka zama cikin
azzalumai.) [Yunus: 106]
Don haka Allah ya ce.
(Haƙiƙa
shirka zalunci ne mai girma) [Lukman: 13]
Na biyu kuma shi ne, zalunci ƙarami,
aikata ayyukan saɓo,
kamar shan giya da zina da caca. Duk waɗannan
zalunci ne, wanda duk ya yi wannan ya zalunci kansa, amma girman wannan bai kai
wancan kashin na farko ba. Wannan zalunci ne wanda in Ubangiji ya ga dama ya
yafe ma laifin da ka yi ɗin,
wannan tsakaninka da shi, in ya ga dama ya ɗanɗana maka azaba gwargwadon yadda ka cancanta, sannan
daga ƙarshe
a cire ka a kai ka aljannah. Don a cikin 'yan aljannah akwai azzalumai, wadanda
sun zalunci kansu, amma dai daga ƙarshe
za a kai su aljannah.
Da Allah (SWA) ya ce, "....Ya ku bayina!
Dukkaninku ɓatattu ne, sai
fa wanda na shiryar da shi, ku nemi shiryarwata, ni kuma in shiryar da
ku...." wani zai ga kamar ya ci karo da wani hadisin daban don ya ce,
"....Dukkaninku ɓatattu
ne, sai fa wanda na shiryar da shi...." amma a hadisin Bukhari [Bukhari
(#1358) da Muslim (#2658)] kuma daga Abu Huraira (R.A) cewa ya yi, "Duk
wani wanda aka haifa, an haife shi ne a kan musulunci." To wannan hadisin
ya ce ana haifar mutum a kan musulunci, ko a kan fiɗira, wannan kuma ya ce, "....Dukkaninku ɓatattu ne, sai fa wanda na shiryar da shi....",
ba cin karo da juna a tsakaninsu. Malamai suka ce, tsarkin yana nan, amma
tsarkin kaɗai ba zai
wadatar ba, sai idan wahayi ya zo an karɓa.
Wahayi kuwa dole sai an koya maka shi, in ka ƙi
karɓar wahayin, to kuma
kana nan cikin ɓata
da ɗimuwa, har sai lokacin
da ka koyi wahayin. Wannan shi ne abin da Allah yake nufi da,
"....Dukkaninku ɓatattu
ne, saiwanda na shiryar da shi...." Haske guda biyu ake buƙata:
Hasken fiɗira, kowa an ba
shi, sai dai zai iya lalacewa, idan mutum ya tsaya a wurin da jahilci ya yi
yawa, sai ya cakuɗe
ya gamu da duhu, ba yadda za a yi ya samu haske, sai in hasken wahayi ya zo,
sai ya
zamanto
haske a kan haske. ' Shi kuwa faɗin
Allah (SWA), “....hakan ba zai rage komai dangane da mulkina ba....” yana nuna
bunƙasar
mulkin Allah Ta'ala kenan. Duk mai mulki yana bunƙasa
ne da dawaki da fadawa, amma Ubangijinmu haka yake shi kaɗai
ba shi da abokin tarayya, ba ya buƙatar
komai. Shi kuma faɗinsa
cewa, ayyukanku ina kiyaye su,"....sannan in cika muku su...." yana
nufin, a nan duniya zai kama ku da azaba. A sakamakon wani zunubi da ka yi, sai
a ɗora maka ciwon kai, don a
kankare maka wannan kuskuren da ka yi jiya ko shekaran jiya ba ka sani ba, sai
ka je ƙiyama
ba ka da laifin komai. Allah ya riga ya tace ka daga zunubi saboda wahalhalun
da ya ɗora maka. Waɗansu
suka ce a'a! wannan hukuncin a lahira ne.
Masha Allah.
ReplyDeleteAbinda yake koyawa
ReplyDeleteAllahu'akbar iname Maka
ReplyDeletefatan alkhairi Allah y kara basira