An karɓo
daga Abdullahi ɗan
Abbas (R.A) ya ce, "Na kasance a bayan Annabi (ﷺ)
wata rana, sai ya ce dani, "Ya kai yaro! Zan sanar da kai waɗansu jumloli: Ka kiyaye (dokar) Allah, sai kai ma ya
kiyaye ka; ka kiyaye (dokar) Allah, za ka samu (Allah) yana yi maka jagora;
idan za ka roƙa, to ka roƙi
Allah; in za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah. Ka sani cewa da al'umma
za su taru kan su amfane ka da wani abu, ba za su iya su amfanarka da komai ba,
sai da abin da Allah ya rubuta maka (cewa naka ne). Idan da al'umma za su taru
kan su cuce ka da Wani abu, ba su isa su cuce ka ba, sai da abin da Allah ya
riga ya rubuta maka. An riga an cire alƙalami,
takardun sun bushe." Tirmizi (#2516) ya rawaito. ya ce, "Hadisi ne
mai kyau ingamtacce."
A Wata riwaya wadda ba ta Tirmizi ba, "Ka
kiyaye dokar Allah, za ka samu Ubangiji a gabanka (yana
maka jagoranci), ka nemi sanin Allah lokacin da kake
cikin yalwa, zai san da kai a lokacin da kake cikin tsanani, ka sani duk abin
da ya kuskure maka, da ma can ba a yi shi don ya
same ka ba, abin da duk ka ga
ya same ka, da ma can ba a yi shi don ya kuskure maka ba. Ka sani cewa cin
nasara yana tare da haƙuri, yayewar
musiba tana tare da baƙin ciki, kuma
lallai a tare da tsanani akwai sauƙi."
SHARHI
"Wannan hadisi an karɓo shi daga Abu Abbas, Abdullahi ɗan Abbas, wato ɗan
gidan baffan Annabi (ﷺ) kenan, ya ce,
"Na kasance a bayan Annabi (ﷺ)
wata rana...." a kan wata dabba. Wannan yana ɗaya daga cikin falalarsa kenan, don adadin sahabban
da Annabi (ﷺ) ya ɗora su a kan dabba yana tare da su, ba su da yawa,
ba su fi mutum goma ba. Wani malami ya waƙe
su. Don haka wata falala ce, Annabi (ﷺ)
ya hau kan dabba, ko ya hau kan rakumi, ko kan alfadari, ko doki, ya ɗora ka a baya, kuna tare da shi, wannan falala ce,
ba kowa ya samu wannan ba. Kuma wannan sai ya nuna yadda Annabi (ﷺ)
ke ƙaskantar
da kai, ya fi kowa fa, amma zai hau dabba, ba shi kaɗai ba, ya ɗora
wani a bayansa.
Manzon Allah (ﷺ)
ya ce, "....in za ka nemi taimako, ka nemi taimakon Allah..." kaɗai, kar ka nema a wajen wani. Taimako iri biyu ne,
haka neman taimako ma iri biyu ne: Ko dai ya zamanto abin da za ka roƙa
ɗan Adam yana da ikon ba
ka shi, wannan babu laifi, ko ya zamanto abin da za ka roƙa,
ba mai ikon yin sa, sai Allah. Kamar saukar da ruwan sama, da warkar da mara
lafiya, da sanya albarka cikin harkar kasuwancinka, da sanya albarka a cikin
harkar nomanka, duk wannan ba wanda zai iya yi, sai Allah, to sai ka roKƙ
Allah shi kaɗai. Haka neman
taimako: In za ka nema, ko dai ya zamanto dan Adam yana da ikon yin sa, kamar,
"Kama nan wurin mu ɗora
kayan nan a mota." ko "Don Allah! Taimaka min ka tura min
motata." Wannan duk ɗan
Adam zai iya yi! Amma dangin taimakon da ba mai iya yi sai Allah, to shi ake
nufi ka roa wajen Allah shi kaɗai.
Fadin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....da
al'umma za su taru kan su amfane ka da wani abu, ba za su iya su amfane ka da
komai ba, sai da abin da Allah ya rubuta maka...." yana nufin, da a ce duk
garin nan su taru sai sun sa ka zama mai arziki, in Allah bai sanya ka mai arziƙi
ba, tun lokacin da aka yi rubutu ba, kana cikin mahaifiyarka, ba za ka taɓa
zama mai arziƙi ba. Sai a riƙa
ba ka abin, amma yana zurarewa; ka samu kuɗin
masu tarin yawa, amma ka kashe, su tafi a shirme. Saboda haka in duniya za ta
taru ta yi maka wani abu mai amfani, ba za su amfane ka ba, sai da abin da aka
rubuta maka can wanda muka karanta a baya. Faɗin
Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....An riga
an cire alƙalami...." yana nufin
an cire shi daga kan takardar, har "....takardun sun bushe...." an
gama komai kenan. Ma'ana, rubutun da aka ce mala'ika ya yi, ya riga ya yi, har
takardun sun bushe, yanzu kawai abin da aka rubuta ne kawai yake gudana, wani
bai isa ya canza wannan abin ba.
Enter your comment...Jazakallahu khairan
ReplyDelete