GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Apr 21, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BAKWAI 7)



Yana Daga Cikin Dangin Shirka Sanya Wani Zobe Ko Zare
Da Makamancinsu Domin Kare Bala'i Ko Magance Shi
SHARHI
__________________________


Wannan babi gabaɗaya, fahimtarsa yana dogara ne da fahimtar alaƙar da ke tsakanin sababi (al-sabab) da wanda yake kawo sababin (almusabbib). Sababi shi ne dukkan wani abin da Ubangiji ya sanya shi, ko ya shar'anta shi, ko ya ƙaddara ana iya amfani da shi don magance kaza. Wanda kuwa yake kawo sababin (Al-musabbib) shi ne Allah din. A shari'ance, shari'a ta yi izini ka yi amfani da shi don magance cuta iri kaza, Ba duka kowane irin magani za ka yi amfani da shi ba, sai wanda shari'a ta ba ka dama. Ba a ɗaukar wani abu a matsayin sababi na 
warkewa daga cuta, sai an yi la'akari da abu uku:
a. Ba ka cewa abu kaza sababi ne na magance cuta, sai idan ya tabbata a shari'ance da ƙaddare (wato an jarraba shi, ba sau ɗaya ba, yana magance cutar) kamar zuma. An jarraba zuma a ƙaddare tana maganin ciwon ciki, sannan Ubangiji ya ba da izini a shar'ance, kuma Annabi ya faɗa a hadisi tana maganin ciwon ciki, aka jarraba, aka gani. Ɗaukar zuma na magance ciwon ciki, ya samu sharadi na cewa ta zama sababi a ƙaddare kuma a shari'ance.
b. Duk abin da aka sa ya zama sababi na warkuwar cuta, to kada ka dogara a kansa shi kaɗai, Kai dai ka yi amfani da shi don Allah (SWA) ya yi izini, amma zuciyarka ta ƙudurce cewa mai warkarwar na haƙiƙi, shi ne Allah (SWA). Idan ya ga dama sai ya zare warkarwar daga maganin, ya sa a wani maganin daban.
c. Ka ƙudurce a zuciyarka duk yadda maganin ya kai ga warkarwa ko amfáni, ba ya yin tasiri sai idan Allah ya yarda ya yi. Waɗannan sharuɗɗai guda uku (3), su ne ake nema wajen riƙon dukkan wani abu ya zama sababi. Waɗannan abubuwa da aka ambata a babi, wato zobe ko wane iri ne, zare, dodon koɗi ko wuri ko ƙaho, hauren giwa da idon mujiya, dukkan waɗannan Ubangiji bai sanya su zama sababi ba, jarrabawa ba ta nuna suna maganin wata cuta ba, kuma shari'a ba ta yi izini na riƙon su don magance wata cuta ba. Saboda haka, duk wanda ya riƙi ɗaya daga cikinsu don magance cuta, to ya yi shirka a ɓangaren Rububiyyah. Idan kuma ya ɗauka a zuciyarsa mai ɗauke cutar shi ne Allah, amma ya riƙi ɗaya daga cikinsu a matsayin sababi, to hukuncinsa ya yi wa Allah ƙarya. Domin ya riƙi sababi da abin da Allah bai sanya shi ya zama sababi ba.
Allah (SWA) bai sanya idon mujiya ya zama maganin ɓarawo a gida ba; Allah bai sanya zobe ya zama maganin baki ko kambun-baka ba; Allah bai sanya wuri ko dodon koɗi ya zama maganin mayu ba, bai sanya haka ba a shari'ance, kuma bai sanya haka ba a ƙaddare. Don haka, kana jingina abin da Allah bai sanya shi ya zama sababi ba.
***************
Da fadin Allah;
"Ku ba ni labarin abin da kuke bautawa ba Allah ba, idan Allah ya nufe ni da cuta, (shin waɗannan allolin) za su iya yaye min cutar? Ko kuma in Allah ya nuface ni da wata rahama, shin za su iya kame rahamarsa? Ka ce da su, "Allah ya ishe ni, a gare shi ne kaɗai masu dogaro suke dogara." (Az-Zumar: 38)
__________________________


SHARHI
Dangantakar ayar da matashiyar maganar, shi ne don a nuna cewa waɗannan ababen ba sa iya ɗauke cuta, kuma ba sa iya kawo amfani. Don haka, wannan ya nuna cewa, babu mai ɗauke cuta ko kawo amfani, sai Allah (SWA). Don haka ka sa zobe ko zare ko idon mujiya ko ƙaho, ka ce maganin mayu ko ɓarawo duk wannan shirka ne.
*****************
An karbo hadisi daga Imran bin Husain (RA) ya ce, "Manzon
Allah (ﷺ) ya ga wani mutum, a hannunsa akwai zobe na tagulla, sai ya ce da shi, "Menene nake gani?" Sai ya ce, "Na sa wannan ne, saboda ciwon hannu (al-wahina)." Sai Annabi ya ce, "Cire wannan zoben! Babu abin da zai kara maka sai cuta da rauni. Da a ce za ka mutu da wannan zoben a hannunka, ba za ka rabauta ba har abada. Ahmad ne ya ruwaito da sanadin da babu laifi a cikinsa. [Al-Musnad J4/445]
____________
SHARHI
Imran bin Husain ibn Ubaid ibn Khalaf Al-Khuza'iy (Abu Nujaid, sahabi ne, haka babansa ma). Wannan hadisin ibn Hibban [Sahihu Ibn Hibban 7/628], da Al Hakim al-Naisaburiy [Al-Mustadarak na Hakim J4/216] da Ibn Majah [#3531] sun ruwaito shi. Sai dai hadisin mai rauni ne. Saboda haka, saƙon da wannan hadisi yake bayarwa, ayar ta wadatar. Annabi yana nuna wannan zoben ba ya amfani, inda hadisin ya inganta.
****************
Akwai hadisin da aka karɓo daga Musnad na Imam Ahmad
[Musnad J4/154], an karɓo daga Ukbah bin Amir (RA), hadisi ne Marfu'i daga Annabi (RA), "Duk wanda ya rataya laya, kada Allah ya cika masa manufarsa, wanda kuma ya rataya wuri, kada Allah ya kwantar masa da hankalinsa."
___________________________
SHARHI
Wannan shi ma hadisin mai rauni ne. [Duba Ad-dha'ifa ta Albani # 1029]

***************

A wata ruwayar hadisin daban na Imam Ahmad,"Wanda duk ya rataya laya, haƙiƙi ya yi shirka."
________________________
SHARHI
Sai dai wannan ruwayar banda Imam Ahmad [Al-Musnad J4/154], haka Imam Hakim al-Naisaburiy [Al-Mustadarak J4/417] ya ruwaito, kuma wannan sahihiya ce. Sheikh Nasiruddeen Albani ya inganta ta a cikin Silsilatul-Ahadisus-Sahiha', shi ne hadisi na 492.
"Wanda ya rataya laya!" Me ake nufi da haka? Ba ana nufin wanda ya rataya ba, ko da mutum nufi ya yi a zuciyarsa cewa laya na da amfani ko da babu a jikinsa, ya yi shirka. Misali ka ga mutum ya sa a motarsa ko a kofar gidansa ko a jikin dabbarsa ko jaririnsa, duk wannan ya rataya kenan.
***************

Ibn Abi Hatim ya ruwaito cewa Huzaifa, ya ga wani mutum
ya rataya wani zare ko ulu, saboda masassara da take damun sa, sai Huzaifa ya yanke zaren, sai ya karanto fadin Allah;
 Duba Tafsirin Ibn Kathir ƙarƙashin ayar [Yusuf:106]

"Mafi yawancinsu ba sa yin imani da Allah face suna masu yin shirka” (Yusuf:106)

Huzaifa ibn Yaman (shi Yaman sunansa Husayl al-Abatiy Haliful Ansar) sahabi ne mai falala, shi Huzaifa ana kiransa Sahib Sirri Rasulillah'. Wannan ruwaya ta ibn Abi Hatim, ta zo a cikin littafin Annahajus-Sadid, cewa ruwaya ce da take bukatar bincike. Ma'ana dai ba ta inganta ba. A cikin dukkan nassoshin da Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab ya kawo a cikin wannan babi, nassi biyu ne suka inganta: Nassin Ƙur'ani da nassin man ta 'allaka tamimatan, ya inganta. Wannan su ne hujja da ya ƙulla babin a kai.


A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Kausasa harshe dangane da rataya zobe da nufin ɗauke cuta
ko hana ta zuwa; ko rataya zare da wannan manufa da makamantansu.
2. An nuna cewa da sahabi zai mutu, wannan abu yana
hannunsa, ba zai rabauta ba, A nan akwai ƙarfafa maganar
sahabbai da suke cewa ƙaramar shirka ta fi manyan zunubai
(kaba'ira) girma.
3. Ba a ba shi uzuri ba kan jahiltar mas'alar.
4. Dukkan dangogin abin da aka faɗa, ba sa amfani a nan
gidan duniya, sai ma cutarwa da suke, saboda faɗinsa, "Ba
za su kara maka komai ba sai dai rauni."
5. Halaccin kausasar harshe wajen inkari ga wanda ya aikata
haka (wato ya rataya wani abu don neman tsari).
6. Bayyana cewa duk wanda ya rataya wani abu, to an jingina
shi ga wannan abin.
7. Bayani cewa, duk wanda ya rataya laya to haƙiƙi ya yi
shirka.
8. Mutum ya rataya wani zare a jikinsa don ya kare shi daga
cutar masassara, shi ma wannan yana daga cikin shirka.
9. Karanta waccan ayar da Huzaifa ya yi, dalili ne da yake
nuna sahabbai suna kawo ayar da take magana a kan shirka
babba don su kafa hujja da ita wajen haramcin ƙaramar shirka. Kamar yadda ibn Abbas ya ambata a cikin ayar Suuratul Bakara.
10. Mutum ya rataya wuri a wuya wai don saboda kambun
baka ko maganin baki, shi ma yana daga cikin shirka yin
hakan.
11. Yin mummunar addu'a ga wanda ya sanya laya; cewa,
kada Allah ya cika masa burinsa, kuma yin addu'a ga
wanda ya rataya wuri; cewa kada Allah ya kwantar masa da
ransa. Ma'ana kada Allah ya kyale shi.

"Duk wanda ya rataya sunan aljanu, ko ya kira wasu ba Allah ba su kare masa masifa ko su jawo masa amfani, to haƙiƙi ya yi babbar shirka. Don ya rataya zuciyarsa ga wanin Allah ya yi masa aikin Allah.


(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...