GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

May 31, 2011

ARBA'UNA HADITH (3) HADISI NA UKU

An karɓo daga Abu Abdurrahman, Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah( ﷺ) yana cewa, "An gina musulunci a kan abubuwa guda biyar: Shaidawa babu abin bautawa bisa ga cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da zakka, da ziyarar ɗakin Allah, da azumin watan Ramadan." Bukhari (#8) Muslim (#16).

SHARHI

"Abdullahi ɗan Umar yana cikin mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisan Annabi (ﷺ). Abin da za mu lura da shi a nan shi ne, a wancan hadisi na biyu da aka tambayi Annabi (ﷺ) musulunci, sai ya
kawo abubuwa guda biyar, kuma su ne dai aka ƙara kawowa a nan. Abin da yake baƙo a nan gurin abu biyu ne: Na farko, a wancan hadisin da aka faɗi kalmar shahada, sai sallah, sai zakka, sai azumin Ramadan, sannan sai hajji ya zamanto shine na ƙarshe. Amma a nan, sai aka kawo kalmar shahada, sannan sallah, sai zakka, sai hajji, sannan aka ce azumi, sai aka kawo azumi ya zamanto a ƙarshe. To a nan wurin babu wani bambanci tsakanin can da nan, domin in aka jeranta abubuwa waɗanda suke iya ƙididdiguwa da harafin wawun, to wannan harafin ya zo ne don tattare waɗannan abubuwa wuri guda, amma ba don nuna wannan na farko ba ne, wannan na ƙarshe. Abu na biyu, a hadisin farko an ambaci waɗancan abubuwa guda biyar, a nan kuma sai ya ce, "An gina musulunci a kan abubuwa biyar...." saƙon da aka isar a nan gurin, ana so a nuna waɗannan abubuwa guda biyar su ne ginshiƙin musulunci, a can gurin kuwa abin da ake so a nuna, shi ne, ayyukan zahiri ana fassara musulunci da su, wato ayyukan gaɓɓai kawai.
Da aka ce ginshiƙai guda biyar ba ya nuna martabarsu ɗaya: Kalmar shahada ta fi kowanne ƙarfi, domin duk wanda ya ƙi kalmar shahada bai yi furuci da ita ba, ba ya zama musulmi. Amma mutumin da ya yarda da kalmar shahada, sai ya zo ya ƙi sallah, waɗansu malamai suka ce ya kafirta. Akwai saɓani a nan, can kuwa ba saɓani. Haka mutumin da ba ya bayar da zakka, yana nan a matsayinsa na musulmi bai kafirta ba, sai dai idan inkarin wajabcinta ya yi, amma rashin bayar da ita, ba ya fitar da shi daga musulunci, ƙila wani ya ce, Allah ya ce,
(Azaba ta tabbata ga mushirikai) Su waye mushirikai a nan, su ne:
(Waɗanda ba sa ba da zakka kuma sun kafirce wa ranar tashin alƙiyama) [Fussilat 7]
Ka ga wannan yana nuna dalilin zamansu kafurai, shi ne ƙaryata ranar tashin aiƙiyama. Waɗanda Abubakar (RA) ya yaƙa, ya yaƙe su ne don ladabtar da su, ba wai don saboda kafirci ne hana zakka ba, a'a! don saboda ya ladabtar da su, su dawo musulunci, kar su karya wani rukuni daga cikin rukunan musulunci.
Musulunci shi ne ayyukan zahiri, imani kuwa ƙudiri ne na zuci, sai dai wani lokaci suna sarkafewa, wannan ya ɗauki ma'anar wannan, kamar yadda za ka gani da dama a hadisin Annabi (ﷺ). Kamar yadda Annabi (ﷺ) yake cewa, "Imani yanki ne ɗaiɗai har sittin da ɗoriya ko saba'in da ɗoriya, mafi girma shi ne, la'ilaha illal Lahu, wanda ya fi zama na ƙasa, shi ne gusar da cuta daga hanyar mutane." [Bukhari (#9) Muslim (#9)]. Wato ka ga ƙusa, ka ɗauke ka jefar, don ka da wani ya taka; ka ga kwalba, ka ɗauke daga kan hanya, wannan wani yanki ne na imani. Ka ga wannan aiki ne na gaɓɓai, ba ƙuduri ba, amma Annabi (ﷺ) ya fassara shi da imani. Don haka suna sarƙafuwa da juna idan sun rabu, in sun haɗu kowanne sai ya ci gashin kansa.

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...