GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Sunday, October 10, 2021

KITABUT-TAUHID (BABI NA GOMA SHA DAYA 11)

Ba A Yanka Domin Allah A Wani Wuri Da Aka Keɓance

Don Yanka Domin Waninsa(¹)

_____________________

SHARHI

(¹)Wannan babin zai yi magana a kan yanka ta ibada, wadda ba ta halatta a wajen da ake yanka don wanin Allah. Misali wajen da mushirikai suke yanka don neman kusanci da gunkinsu, ba ya halatta kai musulmi ka yanka ko da ragon layya ne a wajen! Ragon layya, ragon suna, ko hadaya duk waɗannan ana yin su ne domin Allah. Amma ba ya halatta ka yi waɗannan yankan a wajen da mushirakai suke yin yanka, duk da cewa kai abin da za ka yi ɗa'a ne.

**************************************************

 

Da faɗin Allah,

"Kada ka tsaya a cikinsa (masallaci) har abada…”

(2) (At-Tauba: 107-108)

__________________

SHARHI

 (²)Laa taƙum fihi abadan: Wannan aya na hani ga Annabi (SAW), yin sallah a wani masallaci da munafukai

Friday, October 1, 2021

KITABUT-TAUHID (BABI NA GOMA 10)

                                              Yin Yanka Don Wanin Allah(1)

__________________

SHARHI

(1)Wannan babin zai magana ne a kan ayoyi da hadisai da suke magana a

kan yanka ba don Allah ba. Mutum ya yi yanka ba don Allah ba. To

menene hukuncin hakan? Malamai sukan yi babi irin wannan ba tare da

sun faɗi hukunci ba, ko haram ne, ko halal, ko shirka da sauransu, su

kyale ka, su dogarar da kai da nassin da zai biyo baya. Nassosin da za su

zo, za su nuna maka yanka haƙƙi ne na wa? Idan ya tabbata yanka haƙƙi

ne na Allah (SWA) shi kaɗai, to yin yankan don wanin Allah ya zama

Monday, September 13, 2021

KITABUT-TAUHID (BABI NA TAKWAS 9)

Wanda Ya Nemi Tabarruki Da Bishiya Ko Dutse Da Makamantansu(1)

___________________________

SHARHI

(1)Wannan babin yana magana kan wanda ya nemi tabarrukin wata

bishiya ko dutse, ko makamantansu, kamar mutum ya nemi tabarrukin

Ƙasar kabarin wani shehi ko waliyyi, ko mazaunin wani waliyyi. To

menene hukuncin wannan? Duk wannan yana cikin shirka!

Shin menene 'tabarruki? Kalmar labarruk 'an ciro ta ne daga

Thursday, June 18, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA TAKWAS 8)


                             
                                 TOFI DA LAYA
Ya zo cikin hadisi tabbatacce, daga Abu Bashir al-Ansari
cewa, ya kasance tare da Manzon Allah (SAW) cikin wasu tafiye tafiyensa, sai Annabi ya aiki wani ɗan aike na musamman
kada a kyale wata igiya da aka yi ta da tsarkiya ko abin wuya
tsarkiya a wuyan wani raƙumi sai an cire ta ko kuma kowane abu na wuya sai an cire.
_________________
SHARHI
Wannan hadisi Bukhari [#3005] da Muslim [#2115] ne suka ruwaito shi. Abu Bashir al-Ansariy, aka ce sunansa Ƙais ibn Ubaid kamar yadda ibn Sa’ad ya faɗa a cikin Ɗabakat, amma ibn Abdul Barr ya ce, bincike bai gano mana sunansa ba, an san shi dai da alkunyarsa Abi Bashir al-Ansariy. Malamai suka ce,

Tuesday, April 21, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BAKWAI 7)



Yana Daga Cikin Dangin Shirka Sanya Wani Zobe Ko Zare
Da Makamancinsu Domin Kare Bala'i Ko Magance Shi
SHARHI
__________________________


Wannan babi gabaɗaya, fahimtarsa yana dogara ne da fahimtar alaƙar da ke tsakanin sababi (al-sabab) da wanda yake kawo sababin (almusabbib). Sababi shi ne dukkan wani abin da Ubangiji ya sanya shi, ko ya shar'anta shi, ko ya ƙaddara ana iya amfani da shi don magance kaza. Wanda kuwa yake kawo sababin (Al-musabbib) shi ne Allah din. A shari'ance, shari'a ta yi izini ka yi amfani da shi don magance cuta iri kaza, Ba duka kowane irin magani za ka yi amfani da shi ba, sai wanda shari'a ta ba ka dama. Ba a ɗaukar wani abu a matsayin sababi na 

Monday, April 20, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA SHIDA 6)


Fassarar Tauhidi Da Kuma Kalmar Shahada

Da faɗar Allah;
"Waɗancan Waɗanda (masu shirka) suke roƙon su, su da kansu suna neman kusanci i zuwa ga (Allah) Ubangijinsu, don haka wanene a cikinsu ya fi kusanci i zuwa saduwa da yardar Allah." (Al-Israa":57)

___________________________


SHARHI
Dangane da saukar wannan aya, Abdullah ibn Mas'ud (RA) yake cewa,
"Wata tawaga ce cikin mutane, sai suke bauta wa aljanu. Aljanu suna ba su umarni su bi don samun biyan buƙatunsu na duniya. Ana nan a haka lokaci mai tsawo, sai aljanun suka musulunta, kuma suka cigaba da ɓauta wa Allah. Su kuwa Waɗancan mutane, ba su farga ba, suka cigaba da bauta wa aljanun, su kuma aljanun suna bauta wa Allah. Shi ne Allah ya ce, "Ka ga Waɗancan Waɗanda mutane suke roƙon su, su neman abin da

Sunday, April 19, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYAR 5 )

Kira Zuwa Ga Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah
______________
Sharhi;
Wato idan muka lura jerin babukan littafinnan suna tafiya a tsari. Babin farko Malam ya yi bayani akan menene tauhidi, sannan ya kawo falalar Lauhidi da yadda yake kankare zunubi, sannan sai ya zo babin tsoron afkawa shirka, wanda yana daga kamalar tauhidi mutum ya dinga jin tsoron afkawa cikin shirka. To idan aka samu cikakken tauhidi da kuma cikkaken tsoron faɗawa cikin shirka, to ka zama kamili a karan kanka, saura kuma ka yi ƙoƙarin wane ma ya zama kamili. To shi ne malam ya kawo wannan babi na kira zuwa ga bautawa Allah shi kadai. Wato ka fahimtar da mutane saƙon da ka fahimta.
********************
Da faɗar Allah;
"Ka ce “Wannan ita ce turba ta (musulunci). Ina kira zuwa ga Allah,

FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHAMUD ADAM (R)

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...