Fassarar Tauhidi Da Kuma Kalmar Shahada
Da faɗar Allah;
"Waɗancan Waɗanda (masu shirka) suke roƙon su, su da kansu suna neman kusanci i zuwa ga (Allah)
Ubangijinsu, don haka wanene a cikinsu ya fi kusanci i zuwa saduwa da yardar
Allah." (Al-Israa":57)
___________________________
SHARHI
Dangane da saukar wannan aya, Abdullah ibn Mas'ud (RA) yake
cewa,
"Wata tawaga ce cikin mutane, sai suke bauta wa aljanu.
Aljanu suna ba su umarni su bi don samun biyan buƙatunsu na duniya. Ana nan a
haka lokaci mai tsawo, sai aljanun suka musulunta, kuma suka cigaba da ɓauta wa Allah. Su kuwa Waɗancan mutane, ba su farga ba,
suka cigaba da bauta wa aljanun, su kuma aljanun suna bauta wa Allah. Shi ne
Allah ya ce, "Ka ga Waɗancan Waɗanda mutane suke roƙon su, su neman abin da
zai sada su da Allah suke yi, don haka waye a cikinsu ya fi
dacewa da gaskiya. Wanda ya roki halitta ɗan uwansa, ko kuwa wanda ya roƙi Allah? Kuma suna fatan dacewa da rahamar Allah, suna
jin tsoron azabar Allah." Kamar yadda ya zo a cikin Sahihul Bukhari
(#4715). Amma akwai ruwaya daga Abullahi ibn Abbas (RA) da yake cewa ta sauka
ne a kan mutanen da suke bauta wa salihan bayi, kamar su Annabi Isa, Uzairu,
Nana Maryam da mala'iku. Amma Shekhul Islam ibn Taimiyya ya ce,
"Ayar za ta gasgata a kan waɗannan ma da Waɗanda ba su
ba." Duk wani wanda yake bautar wani salihin bawa, wanda shi salihin bawan
yana bautar Allah, to wannan ayar ta gasgata a kansa. Ya kasance an yi ne a da ko
a yanzu, ko zai zo nan gaba." Duk wani salihin bawa da za a ce wane salihin
bawa ne ko waliyyi ne da me yake samun salahar ko walittakar Da bin Allah ne,
da bin umarninsa, da jin tsoron Allah, da fatan samum rahamarsa ne. Wannan shi
ne zai mayar da shi salihi ko waliyyi. Da zarar an samu tarihin wani bawa da
zai ce shí ba ya jin tsoron Allah, ko ba ya jin tsoron azabarsa, aljannar ma ba
ya so, yana bauta wa Allah ne don shi ne Allah, to wannan ba waliyyi ba ne,
yanzu ƙoƙari
ake ya zama musulmi kenan, domin akwai nau'i na zindiƙanci tattare da shi. Shi ne Ibnul Kayyim yake cewa,
"Siffa uku ce ake so a wurin salihin bawa: (a) ƙololuwar ƙauna zuwa ga
Allah (al-mahabba) (b) fatan samun rahama (c) jin tsoron Allah." Duk
wannan ayar ta haɗa su. Ashe ayar na nuna
mana cewa, aikin ɗa'a shi ne wasila ɗin kenan. Ka riƙi aiki
nagari da imani, jihadi, a matsayin shi ne wasilarka da zai sada ka da rahamar
Allah. Yayin da kake aikin kuma, kada ka dogara da shi, har yanzu kana nan
baynal khaufi war-raja 'a (wato tsoro da sa rai). Duk ibada, sai an gina ta a
kan wannan. Idan ya zamanto kana tsoron azabar ne kaɗai, ba ka fatan samun rahama, har yanzu ba ka zama bawa
nagari ba. Domin ya zamanto kana ɗebe tsammani
daga rahamar Allah, Allah (SWA) kuwa ya ce, "Kada ku ɗebe tsammani daga rahamar Allah." Rahamar Allah (SWA)
tana da yalwa. Domin babu mai ɗebe tsammani
sai kafirai. Faɗin rahamar Allah shi ne zai
sa kada ka ɗebe tsammani Na gaba, dole ka ji
tsoron azabar. Sa rai wajen rahamar, ba tare da tsoron azabar ba, laifi ne.
Haka kuma tsoron azabar, ba tare da sa rai da rahamar ba, shi ma laifi ne. Dole
sai an sami ɓangare biyun.
Menene dangantakar ayar da wannan babin? Shi ne malamai suka ce,
"Tauhidi shi ne yarda da kaɗaituwar Allah shi kaɗai." Wannan yardarm abu ne na zuci da harshe zai furta,
idan harshe ya furta, gaɓɓai suka gasgata ta
hanyar aiki. Wannan aiki da za ka yi, shi ne yake tabbatar da tauhidi ɗin, wanda shi aka sa wa suna a cikin ayar wasila. Sannan
kuma a waje ɗaya, yana ƙara nuna mana alamar tauhidi, shi ne riƙar wasila zuwa wurin Allah. Abin da za ka riƙe ya zama wasilarka zuwa wurin Allah, shi
ne ibada, ba ka riƙi gangar jikin wani mutum ba.
Ibadarka da za ka yi, to wannan shi ne wasilarka ta dacewa da rahamar Ubangiji,
amma riƙar gangar jikin wani mutum, ya zama
kishiyar tauhidi. Domin lokacin da ka riƙi
gangar jikin wani mutum wasilarka, za ka zo ka bauta masa ka ƙyale Allah. Wannan shi ne dangantakar ayar da babin.
********************
Da Faɗin
Allah
"Ka tuna wa al'ummarka yayin da Ibrahim ya faɗa wa
mahaifinsa da mutanensa cewa. "Lallai ni na kuɓuta daga dukkan dangin abin da kuke bautawa, sai wanda ya
ƙirƙiri
halittata." (Az Zukhruf 26-28)
______________
Sharhi
Wannan abin da Annabi Ibrahim (AS) ya fa ɗa, shi
ne, barrantar duk wani abin bautawa da mutanensa suke yi. Lokacin wasu na
bautawa taurari, wasu gumaka da sauransu. To shi ne Annabi Ibrahim ya yi fito
na fito da su, ya ce duk ba zai bauta musu ba, sai dai wanda ya ƙirƙiri halittata, wato
ya halicce ni ba tare da ya ga samfuri a wajen wani ba. Shin menene alaƙar tauhidi da wannan ayar ko tafsirin kalmar? Abin nan da
Annabi Ibrahim ya faɗa shi ne, tafsirin
kalmar shahaɗa. Domin Kalmar shahaɗa ɓangarori
biyu gare ta.
a. Laa ilaaha- Nafyun: Wato korewa kenan. Wannan ya yi daidai da
faɗin Annabi
Ibrahim "Lallai ni na kuɓuta daga
dukkan dangin abin da kuke bautawa.
b. llallaahu-Ithbatun: Wannan shi ne tabbatarwa, kuma shi ya yi
daidai da faɗinsa "sai wanda ya ƙirƙiri halittata.
Korewa ita kaɗai, ba ta mayar da mutum musulmi, sai ya haɗa guda biyun. Wannan shi ne tafsirin kalmar shahaɗa. Ashe
wannan maganar ta Annabi Ibrahim kalmar shahaɗa ce ya faɗa, don haka ƙarshen ayoyin
suka nuna cewa kalma ce mai wanzuwa a cikin zuriyarsa.
*******************
Da faɗinsa;
"(Yahudu da nasara) sun riƙi malamansu da masu ibadarsu a
matsayin abubuwan bauta," (ATauba 31)
_______________
Sharhi
Abin da zai ƙara fito da wannan fili, shi ne hadisin Tirmizi [#3095],
wanda Adiy bin Hatim Aɗɗa'i, da can kirista
ne kafin ya musulunta. Da ayar nan ta sauka, ya zo wurin Annabi (ﷺ) yake cewa,
"Ayar nan ta cikin Suuratut Tauba ta tuhumce mu kan cewa mun riƙi malamanmu da masu ibadarmu ababen bauta ne mun kyale
Allah." Ya ce, "Ko alama ba mu taba riyawa cewar ababen bauta ne gare
mu ba. Ta yaya aya za ta zarge mu da abin da ba laifinmu ba?" Sai Manzon
Allah (ﷺ) ya ce, "Yanzu malamanku ba sa halatta muku haram ku bi su?"
Sai ya ce, "Eh! Da wannan kam." "Kuma ba sa haramta muku
halal?" Sai ya ce, "Eh!" Sai Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ai
wannan kuma ita ce bautar gare su.
Ba wai sai ka durƙusa ka yi masa bauta ba. Daga
lokacin da
malaminka ya halatta maka abin da ka sani a Ƙur'ani
da hadisi karara sun haramta, ka ajiye wannan ka bi shi, ka bauta masa. Ya ce
maka, "Ai babu komai, irinku babu wani abu idan ka yi." Wannan shi ne
malamai suke kira shirka ta ɗa'a. Ubangiji
ya halicce ka don ya umarce ka, ya hane ka, sai wani ya zo ya yi maka umarni da
hani saɓanin abin da Allah ya umarce ka, ko
ya hane ka, kuma ka yi masa biyayya saboda kana ganin ai malaminka ne, kuma ka
san lallai umarnin ya saɓa wa Allah, to shi
ma ka bauta masa, ka haɗa shi kishıya da Allah. Wannan shi ne ma'anar Kalmar
shahaɗa. Idan za ka faɗi kalmar sau miliyan
a rana sau miliyan da dare, yin wannan kaɗai
ka warware kalmar shahaɗar. Saboda aikinka kishiyar abin da kake faɗa ne. Allah bai halicci kowa ba sai don ya bi umarninsa
shi kaɗai Duk wanda ya yi umami ya saɓawa Allah, sai a ajiye masa
umarnin a ƙi bi. Shin yahudu da nasara ne suka riƙi malamansu da masu ibadarsu, ko kuwa sun raba ne?
Yahudu, su ne suka riƙi malamansu abin
bauta, nasara, su kuma sun riƙi masu
ibadarsu (masu bautar cikinsu). Kuma wannan shi ne ya fi rinjaye a wurinsu. (Ƙarin
bayanin ayar zai zo a babi
na 38]
********************
Da faɗinsa;
"Daga cikin mutane akwai Waɗanda suke riƙar wanin Allah
matsayin kishiyoyi ga Allah, za ka ga suna ƙaunarsu kamar yadda ake
ƙaunar Allah." (Al-Bakara 165)
__________________
Sharhi
Andadan: Jam'i ne na niddu.
Idan an ce al-niddu, an ce alshibhu, wato kama, ka kamanta abu ga Allah (SWA).
Ba wai ana nufin kamanta shi da Allah wajen sifa ba, domin ba su ga Allah ba,
bare su kamanta shi da wani ba. Abin da ake nufi shi ne kamanta Allah ta wajen
haƙƙi, shi
ma su ba shi wata dama ta Allah (SWA) shi kaɗai, shi ma su samu irinta su be
shi, sun kamanta shi da Allah kenan,
Me ake nufi da cewa, "Suna ƙaunatar su kamar ƙaunar Allah
Shi
ne malamai suka ce, su waɗannan da suke riƙar kishiyoyi ga
Allah, suna son waɗannan kishiyoyi irin son da suke wa Allah. Ma'ana sai suka
raba soyayyar, rabi suka ba wa waɗannan kishiyoyin, rabi suka ba wa Allah, suna
son su daidai-wa-daida da Allah. Wannan ya zama shirka kenan, domin son Allah,
shi ne ƙololuwa.
Amma ka haɗa soyayyar Allah da ta wani,
mala'ika ne, Annabi Isa ne, Nana Maryam ce, wani salihin bawa ne, duk wannan
shirka ce wadda ake kira Shirkul Mahabbati Waɗansu malamai suka ce, abin da ake
nufi shi ne, suna son kishiyoyi ga Allah, kamar irin son da muminai suke yi wa
Allah. Muminai nagari suna son Allah, so na ƙololuwa,
duk a yayin da suka samu wani abu, za su nuna
cewa Allah (SWA) ne ya ba su. Haka su ma suke yi wa kishiyoyi ga
Allah. Ma'anar ayar guda biyu ce, ko dai ta farkon ko ta biyun. Sai dai ma'anar
farko ta fi bayyana a ayar. Muminai suna son Allah ƙauna ta ƙololuwa shi kaɗai,
ba sa yarda su haɗa shi da wani. Ina ne inda ayar take da alaƙa da matashiyar
magana? Inda matashiyar take, shi ne yadda Allah (SWA) yake cewa, "Ƙololuwar
ƙaunarsu tana tabbata ga Allah." Wannan shi ne yake tabbatar da ma'anar,
laailaaha illallaahu. Malamai suka yi ƙarin bayanin cewa, ita ƙauna, akwai ta
ɗabi’a, wadda galibi zargi ko yabo ba shi da alaƙa da ita. Misali, ɗan Adam
yana son nau'i na abinci, gida, tufafi da sauransu. Wannan ƙauna ce wadda ibada
ba ta da alaƙa da ita ta kai tsaye. Amma irin ƙaunar da ibada take shiga ciki,
ita ce wadda za ta sa ka ji ba ka iya saɓa umarnin wanda kake ƙauna ɗin ta
kowane hali. Wannan ba zai yiwu a yi wa wani irin wannan ƙauna ta ƙololuwa ba,
sai Allah, ta yadda ƙaunar ce za ta sa ba za ka iya saɓa umarninsa ba. Biyayya
ga wanin Allah; ya haramta wa mutum halal ko ya halatta masa haram, shi ne ake
kira Shirkul-Da'a.
Wadda kuma za ka ƙaunaci wani irin yadda za a ƙaunaci Allah, wannan
ita ce Shirkul Mahabbati. Dukkan waɗannan suna rushe tauhidi ne gabaɗaya. Duk
wanda ya yi su, zai wayi gari ba a cikin musulunci ba.
Don haka daidaita Allah da wani wurin ƙauna, shirka ne. Kuma duk
wanda za a ƙaunata, ya zamanto Allah ne ya umarci a ƙaunace shi. Idan ka ƙaunaci
wani don Allah, ka so wani gari ko gida don Allah, duk yana cikin ƙaunar Allah
(SWA), kuma za ka samu lada a kai. Ka so gari don Allah, wato ka fifita Makka
sama da sauran garurruka a cikin zuciyarka sama da garin da aka haife ka saboda
Allah ya fifita ta; ka fifita Maɗina da Masjidul Aƙsa don
Allah ya fifita su. Ka so wasu zamunna, ka fifita kwanaki goman farko na Zhul
Hijja; darare goman ƙarshe na Ramadan a kan
sauran darare, ka fifita daren Lailatul-ƙadr
a kan sauran darare, ka so bayin Allah muminai maza da mata, duk wannan yana
cikin ƙaunar Allah.
****************
Ya zo cikin Sahihi [Muslim #23] daga Annabi (ﷺ) ya ce
"Wanda duk ya ce, "La ilaha illallah," kuma ya
kafirce wa abinda ake bautawa ba Allah ba, jininsa da dukiyarsa sun haramta (a
yaƙe shi
ko a ribace dukiyarsa), kuma hisabinsa yana ga Allah Madaukakin Sarki." Bayanin
wannan babi shi ne abin da zai biyo baya na babi-babi.
__________
Sharhi
Abin da wannan hadisi yake da alaƙa da matashiyar magana,
ma'anar, laa ilaaha illallaahu shi ne ka yarda da bautar Allah shi kaɗai, kada
ya zama kana bauta wa Allah a karan-kanka, amma zuciyarka ta yarda ko an bauta
wa wanin Allah babu komai. To ba ka yi daidai ba. Lallai sai ka yarda da duk
wata ibada da ake yi ba ta Allah ba, rusashshiya ce, kuma kana fatan rushewar
ta, kuma kana bin hanyoyin da za ka rage mabiyanta, da dukiyarka, ko iliminka
ko dabararka. Wannan shi ne, laa ilaaha illallaahun ka ta tabbata. Amma ka faɗi,
laa ilaaha illallaahu sau miliyan, amma ka ce, a kyale 'yan mishan su gina
coci, ku kuma ku gina masallaci!
Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Mafiya Girma Da Mafi
Muhimmanci. Su Ne:
1. Tafsirin tauhidi da ma'anar kalmar shahada, da bayaninta da
al'amura bayyanannu.
2. Daga ciki akwai ayar cikin Suuratul Israa', wanda wannan
ayar ta mayar da martani a kan mushrikai Waɗanda suke kira
salihan bayi A cikin akwai abin da yake nuna cewa kiran
salihan bayi shi ma babbar shirka ce.
3. Haka kuma akwai ayar nan ta cikin Suuratul Bara'a (Tauba),
an bayyana mana cewa, lallai Ahlul kitab sun riƙi
malamansu da
masu ibadarsu a matsayin ababen bauta suka kyale Allah. Kuma
ya bayyana a ciki cewa, ba a umarce su da su bauta wa komai
ba, sai Allah shi kaɗai, Tare da nuna mana cewar, tafsirin ayar
wanda babu rikitarwa a cikinsa, nuni ne dangane da yin ɗa'a ga
malamai ko wasu masu ibada cikin sabo, ba wai roƙon su
aka yi
ba.
4. A ciki akwai faɗin Khalil (AS) ga kafirai da ya ce, "Ni
na
barranta (kuɓuta) daga abin da kuke bauta wa, sai dai wanda ya
halicce ni. Ma’ana wannan bara'a da ya yi, da ƙauna da ya nuna,
shi ne tafsirin 'Shahaɗatu anla'ilaha illallah' Sai (Allah) ya ce "Kuma (Ibrahim)
ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa cikin zuriyarsa. "Sai ya
togace Ubangijinsa abin bauta, Allah ya nuna
5. Mun fahimci tafsirin ayar Suuratul Baƙara
wadda ta shafi
kafirai inda Allah ya ce a kansu, "Sun shiga wuta babu dama
su
fita." Laifinsu suna son kishiyoyin da suke jingina wa
Allah,
kamar yadda ake son Allah shi kaɗai. Ga shi suna son Allah so
mai tsanani, amma wannan bai sanya shigarsu cikin musulunci
ba, to yaya wanda yake son kishiyar Allah sama da Allah? To,
ina ga wanda ba ya son komai, sai kishiyar Allah, kuma ba ya
son Allah?
6. Daga ciki akwai faɗin Annabi (ﷺ), "Wanda ya ce, 'Laa
ilaaha
Illaallaahu 'kuma ya kafirce wa wani abin bauta, ba Allah ba, an
haramta jininsa da dukiyarsa, kuma hisabinsa yana ga
Allah."
Wannan yana cikin mafi girman abin da yake bayyana ma'anar
laa ilaaha illallaahu'. Domin shi Manzon Allah, bai sanya faɗar
kalmar ita kaɗai ba, ta zamanto za ta kiyaye mutum da jininsa da
dukiyarsa. Kai ko da ma a ce ka san ma'anarta, tare da furta
lafazinta, kai har ma da iƙirari da hakan, da ma kasancewar mutum ba ya bauta wa
kowa, sai Allah shi kaɗai, ba tare da abokin tarayya ba, wannan duka ba zai
haramta dukiyarsa da jininsa ba, har sai ya kara a kan haka, da kafirce wa duk
abin da ake bauta wa ba Allah ba. Idan har ya yi kokwanto, ko ya yi inda-inda,
dukiyarsa ko jininsa ba su zama haramun ba. Ka yi mamakin girman wannan mas'ala
da buwayarta, da wannan bayani irin yadda ya fito fili, da hujjar da aka yi
bayani. Shin akwai abin da ya fi ta zama yankan hujja a kan duk wanda yake jayayya?!
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK
JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba
Insha Allah)
Masha allah
ReplyDelete