Wanda Ya Nemi Tabarruki Da Bishiya Ko Dutse Da Makamantansu(1)
___________________________
SHARHI
(1)Wannan babin yana magana kan wanda ya
nemi tabarrukin wata
bishiya ko dutse, ko makamantansu,
kamar mutum ya nemi tabarrukin
Ƙasar kabarin wani shehi ko waliyyi,
ko mazaunin wani waliyyi. To
menene hukuncin wannan? Duk wannan
yana cikin shirka!
Shin menene 'tabarruki? Kalmar labarruk 'an ciro ta ne daga
Al barakatu' ko 'Al-birkatu, yana nuna ma'anar cewa tattaruwar abu wuriɗaya; ga yawa kuma ya taru wuri guda.
Don haka, wurin da ruwa ya taru,
sai su ce masa 'al-birka' Don haka,
duk lokacin da aka ce abu mai
albarka ne, ana nufin yana da alherai
masu tarin yawa. Idan aka ce,
tabarruk ya zamanto neman albarka,
wato neman alherai kenan. To
wannan neman alherin, ba a nemansa,
sai a inda yake. Don haka, albarka
sai an tabbatar da ita a wuri ake
zuwa nemanta.
Duk albarka daga wurin Allah (SWA)
take, ba a jingina wa kowa ita
sai Allah. Don haka, lafazin albarka
ya maimaitu a cikin Alkur'ani har
sau 34 sannan ya zo da siga
daban-daban har guda 8.
1. Barakah 2. Baraknah 3. Burika 4.
Tabaraka
5. Barakat 6. Barakatuhu 7. Mubarakun
8. Mubarakatan.
Duk inda kalmar take, ba a jingina wa
kowa, sai Allah (3). Ibnul
Kayyim, a cikin littafin Bada 'iul
Fawa id ya ce, "A sallama mukan ce,
Assalamu alaikum warahmatullahi
wabarakatuhu! Lafuzza uku ne, ka yi
wa mutum addu'a da shi, salam,
rahama, barakat. An bar waɗancan a
baya don su ne ƙashin bayan tafiya.
Na farko kana iya jingina wa Allah
shi, kuma ana iya jingina wa wanda ba
Allah ba. Duk inda ka ga rahama
ko baraka, ana jingina wa Allah (SWA)
ne kawai. Don haka, shi ne wanda
yake ba da albarkar. Saboda haka,
albarkar sai Allah (SWA) ya rarraba ta. Ya
ba da ita ga wurare, lokuta, wasu
mutane, wasu halittu, wasu halaye, kai
har da wasu hada-hada daga cikin
mu'amalolinmu na yau da gobe.
Albarka ta wuri, sai ya ba da ita ga
wuri uku waɗanda babu sama
da su: Makka, Madina, Masjidul Aksa.
Ya bayar da albarka ga lokuta,
kamar Lailatul Ƙadri goman ƙarshe na
Ramadan, goman farko na Zhul
Hijja, da ranar Arfa. Ya bayar da
albarka ga wasu halittu da muke iya gani
kamar ruwan zamzam. Ya bayar da
albarka ga wasu mu'amalolinmu,
kamar mai sayar da haja da mai saya
suka haɗu a wurin faɗin gaskiya
dangane da cinikayyarsu matuƙar ba su
rabu ba, kuma wani bai ha'inci
wani ba, to sai a sanya albarka a
ciki. Abin da za a sanya albarka a ciki,
ita ce hajar ga mai saye, idan ya zo
da gaskiya, ba don ya cuci mai hajar
ba, sai ya daɗe yana amfanar ta. Shi
kuma kuɗin da ya karɓa na hajar, sai
ya biya masa buƙatu da yawa na
rayuwa, ba tare da sun ƙare da wuri ba.
Kowanne an sa masa albarka. Amma idan
suka yi ƙarya, suka yi maguɗi,
sai a tafiyar da albarkar kasuwancin.
Duk wannan don mu san cewa, duk inda
aka sanya albarka, to
Allah (SWA) ne ya sanya ta. Sai idan
muna da nassin sanya albarka a wuri za
mu yarda cewa akwai ta. Idan an
tabbatar akwai, sannan mu neme ta ta
hanyar da shari'a ta yarda mu nema,
ba ta hanyar da muke so ba.
Don haka, a cikin yan Adam kuwa
mafiya albarka su ne
Annabawa. Dukkansu an yi tabarruki da
su. Lokacin Annabi (SWA),
sahabbai sun nemi albarkarsa, sun yi
tabarruki da majinar da zai tofar,
gumin da yake fitowa daga jikinsa,
gashin kansa da za a aske, ragowar
ruwan alwalarsa, rigar da zai sanya
ya kwabe ta, domin albarkarsa
tabbatacciya ce, shi ne mafi albarkar
masu albarka.
Amma musulmai gabadaya a jumlace suna
da albarka. Sai dai
tantance albarka zuwa ga wane ko
wance, yana bukatar dalili. Kamar ka
ce, musulmai gabadayansu 'yan aljanna
ne, amma tabbatar da aljanna ga
wani daya, ka ce wane ɗan aljanna ne,
ba ka da tabbas. Idan aka yi sa'a
musuluncinsa nagari ne, ya shiga
ciki, amma idan aka yi rashin sa'a bai
zama nagari ba, bai zama musulmi ba.
Akwai bambanci tsakanin faɗin
hukunci gabaɗaya da kuma keɓance shi
ga wani mutum ɗaya. Yana
buƙatar nassi ko dalili. Idan ka ce,
"Malam wane ko shehi ko waliyyi
wane yana da albarka." Wa ya
gaya ma? Da wane nassin ka dogara?
Ballantana kabarinsa? Shin za a yi
tabarruki da ruwan alwala ko majinar
waliyi wane, kamar yadda sahabbai
suka yi wa Annabi (SAW) don neman
Tabarruki?A'a! Don idan ka yi, ta
zama kazanta kenan. Domin ba za ka
kwatanta shi da Annabi (SAW) ba.
Kamar yadda wani mai waka yake cewa,
"Wa ya yi wa yai kamar ka,
wa ya san asali ya naka,
wa ya samu irin rabonka,
tun da Allah ya yabe ka,
duka wanda ya ki ka ma yi gaba."
***************************************************
Da Fadin Allah;
Shin ku ba ni labarin Lata da
Uzza..." zuwa Karshen ayoyin." (An.
Najm:19-23) (1)
_______________
SHARHI
(1)(AI-Lat: Malamai sun yi sabanin
asalinta. Wasu suka ce asalin Al-Lat
kafirai sun kago shi ne daga Allahu.
Wato sai su suka cc, Allahu lafazi ne
muzakkar, sai suka sanya wa sunan
gunkinsu ta mace mu'annath wato
Allat. Magana ta biyu, Allat, sunan
wani mutum ne a jahiliyya, ya
kasance yana hidima lokacin aikin
hajin da jahiliyya suke yi, sai ya samo
garin alkama ya yi wani abin sha mai
kama da kunun zaki ko koko, yana
damawa, ya bayar sadaka ga mahajjata
da ziyarar gumaka. Sunansa Lat!
Da ya mutu, sai suka yi
mutum-mutuminsa suna bauta masa. Wannan
maganar ita ce Bukhari [#4859] ya ruwaito
daga wurin Abdullahi ibn
Abbas.
A-Uzza: Waɗansu malamai suka ce,
kalmar 'uzza, kamar sun yi
ta'annithi ne na Al-Aziz. Al-Uzza sai
ya zama mu 'annath. Amma riwayar
Imam Nasaa'i [Sunan al-Kubra #11548,
J6/474] ta tabbata cewa Annabi
(SAW) ya tura Khalid ibn Walid (R),
bayan bude Makka, ya ce ya je kauyen
da ke tsakanin garin Makka da Ɗa'if,
wani gari mai suna Nakhla, akwai
wani gunki Al-Uzza, ya je ya rusa
shi. Da ya je sai ga wani ɗaki ko bukka
da aka yi ta katako an ɗora shi a kan
itacen magarya guda uku, kamar
murhu, an ɗora shi a kai. Da ya je ya
sare itacen, ya rusa ɗakin, sai ya yi
tafiyarsa. Ya dawo, Annabi ya tambaye
shi abin da ya yi? Sai ya ce ya
rusa ɗakin. Sai Annabi ya ce, 'Har
yanzu Uzza tana nan." Ya dawo ya
sake kawo hari, masu bauta wa Uzza
suka gudu cikin duwatsu. Da ya
farka wannan ɗakin, sai ya ga wata
mace tsirara, ta tsefe gashin kanta, ta
ɗauki ƙasa a tafin hannunta tana
watsawa a ka, ashe ita ce Uzza. Saboda
haka, ya kashe ta, ya ƙona katakon
wurin. Sannan ya koma. Da ya je
Manzon Allah (SAW) ya ce,
"Lallai yanzu ka gama da Uzza."
Shin suna da ikon cutarwa ko
amfanarwa? Wato, bayan an faɗi
shirkarsu, sai aka sake faɗin
ilhadinsu. Domin kafiran Makka suna cewa,
Ubangiji yana da 'ya'ya mata, mala'
iku 'ya'yansa ne, kuma mala'iku
mata ne. Sannan a jahiliyyarsu, ba sa
son 'ya mace sai namiji, don haka
suke jingina wa Ubangiji 'ya'ya mata,
abin da ba sa so. Shi ya sa Allah
yake cewa,
"Yanzu kun zabi 'ya'ya maza ku
jingina wa kanku, sannan ku jingina wa
Ubangiji 'ya'ya mata? Lallai wancan
rabo da kuka yi in da abin haka ne,
ya zama rabo na zalunci. Su waɗancan
gumaka, ba komai ba ne, face
sunaye waɗanda kuke ƙirƙiro su ku da
iyayenku. Ubangiji bai saukar da
wata hujja game da su ba. Ba su
bibiyar komai face zato da son zuciya,
haƙiƙa kuwa shiriya ta je musu daga
wajen ubangijinsu." (Najm:21-23)
A nan Ubangiji (SWA) ya ci gaba da
gaya musu abin da suke riyawa,
cewa, waɗannan gumaka da suke roka,
suke neman tabarrukinsu, duk
sunaye ne, su suka ƙirƙia, su suka
sassaƙa gumakan, suka sa musu suna,
suka ce suna da albarka, kuma suke
neman albarkar! Duk ba ɗaya da
Allah ya saukar da wahayi a kai.
Allah ya ci gaba da cewa su kafiran ba
abin da suke bi, sai dai zato game da
iyayensu. Suna cewa, yanzu abu
kaza, da ba shi da kyau, da wane ya
yi? Yanzu kenan kakana wane bai
kyauta ba? Kyautata zato ga iyaye da
kakanni, shi ya sa su yin wannan
shirkar da tabarruki na ƙarya. Abu na
biyu da ya sa haka, bibitar son
zuciya. Sun kafa wani kamfani da suke
tatsar bayin Allah, da kuma
shugabanci da suka samu, ba sa so ya
rushe. Don haka ba sa son kan
mutane ya waye su daina shirka.
A takaice, dukkan gumakan nan uku,
neman tabarruki ne ya sanya
aka bauta musu. Shi ya sa tabarmukin
nan zai buɗe ƙofa, ko dai ta shiriya
ko ta sharri. Ta shiriya, idan ka nemi
albarka wurin abu mai albarka.
Kuma ita albarka iri biyu ce:
Albarkar samun duniya da albarkar samun
lahira.
Sannan kuma nau'in da ake neman
albarkar shi ma iri biyu ne:
a. Ko dai abin ya kasance lokacin
rayuwar Annabi ne za a yi tabarruki
da shi.
b. Ko kuma abin ya kasance har bayan
rayuwar Annabi.
Abin da ake yin tabarruki da shi
lokacin rayuwarsa, shi ne kamar imani da
Annabi (SAW) da soyayya gare shi, don
a amfana da shiriyarsa da addu'arsa.
Kuma wani sharaɗin na neman albarka
shi ne, idan ka je neman
albarkar waje, za ka neme ta ne ta
hanyar da shari'a ta ba da izini. Misali
idan ka je Makka, za ka nemi albarka
ta hanyar ɗawafi a Ka'aba, sa'ayi
tsakanin Safa da Marwa, shan ruwan
zamzam, kiyaye dokar Allah a
wajen, duk wannan neman albarkar
Makka kenan. Idan ka je Madina,
zuwa masallacin Annabi, yin nafila a
masallacin, zuwa ka yi sallama ga
Annabi (SAW) da yi masa salati, da
zaunawa jin darasi a masallacin, duk
wannan shi ma tabarruki ne da
masallacin. Amma ka shafi bangon
masallacin ka shasshafa a jikinka duk
shirme ne. Haka ma idan ka je
Ka'aba a maimakon dawafi, sai ka
shafi bangon Ka' abar, to shi ma ba ka
sami albarkar Ka'aba ba. Ka ga akwai
albarka a Ka'aba, amma ba ka
neme ta ba, ta hanyar da shari'a ta
yarda.
****************************************************
An karɓo hadisi daga Abi Wakid
Al-Laisiy ya ce, "Mun fita
tare da Manzon Allah (SAW) i zuwa
yaƙin Hunaini, a lokacin ba mu
daɗe daga barin kafirci ba, kuma
mushrikai suna da wata magarya,
suna lazumtar ta, ba sa rabuwa da ita.
Suna rataye makamansu a
jikinta, suna kiranta Mai Maratayai!
Mu ma muna cikin tafiya, sai
muka wuce ta wata magarya, sai muka
ce, "Ya Manzon Allah (SAW)!
Ka sanya mana wata Mai Maratayai
kamar yadda suke da Mai
Maratayai. " Sai Annabi (SAW) ya
ce, "Allahu Akbar! Lallai wannan ita
ce hanyoyin waɗanda suka gabata.
Wallahi kun faɗi irin abin da
Banu Isra'ila suka faɗa wa Musa,
"Ka sanya mana gunki kamar
yadda waɗannan (kauyawan) suke da
gunkinsu." Sai ya ce da su,
"Lallai ku mutane ne
jahilai." Sai Annabi ya ce, *Wallahi da ma sai
kun bibici hanyoyin waɗanda suka
rigaye ku."(1) Tirmizi [#2180] ne
ya ruwaito kuma ya inganta shi.
____________________________
SHARHI
Abi Wakid Al-Laisiy sunansa Al-Harith
ibn Auf, sahabi ne mai falala,
ya mutu shekara ta 68 bayan hijira.
Yaƙin Hunaini; wato bayan Fathu Makka
wajen yaƙar ƙabilar
Hawazin.
... suna kiranta Mai Maratayai!' Wato
idan kafirai za su yaƙi, suna
riya cewa in dai sun rataya makamansu
a nan, suka nemi albarkar bishiyar
idan za su yaƙi, to za su ci nasara.
A nan su mushirikan sun tabbatar da
abubuwa guda biyu da ba su da hujja a
kai. Na farko, tabbatarwa da
bishiyar magarya albarka, na biyu,
hanyar neman albarkar ta rataye
makamansu.
Yanzu mahalush-shahid a nan wurin shi
ne, sun nemi albarkar
magarya, bayan ba ta da ita. Annabi
(SAW) ya nuna wannan abin shirka ne,
ya kwatanta su daidai da mutanen
Annabi Musa (ASW), duk da cewa abin
da Banu Isra'ila suke cewa Musa shi
ne, "Ka sanya mana gunki kamar
yadda waɗannan (ƙauyawan) suke da
gunkinsu." Su kuwa abin da
waɗannan suka ce, "Ka sanya mana
wata mai maratayai." Lafuzzan sun
sha bamban amma ma'anar duka ɗaya ce.
Shi ne malamai suke cewa,
canza suna, ba ya canza zatin abu.
****************************************************
A Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli
Kamar Haka:
1. Fassarar ayar cikin Suuratun Najm.
2. Sanin surar abin da suka
nema.(Wato tabarruki da bishiya)
3. Kasancewar ba su aikata wannan abu
ba.
4. Kasancewar sun nemi kusanci zuwa
ga Allah ta hanyar hakan,
saboda zatonsu (Allah) yana son
hakan.
5. Idan ya zamanto cikin sahabbai an
samu wanda ya jahilci
haka, to wanda zai zo baya shi ne ya
fi cancantar jahiltar haka.
6. Sahabbai suna da kyawawan ayyuka
da alkawari da Allah ya
yi musu na gafara wanda waninsu ba
shi da hakan.
7. Annabi bai ba su uzuri ba ya yi
shiru. Ya mayar musu da
martani nan take da faɗinsa,
"Allahu Akbar! Lallai wannan
tafarkin waɗanda suka gabace ku ne,
da sannu za ku bi
tafarkin waɗanda suka gabace
ku." Sai ya kausasa harshe ga
waɗannan abubuwa guda uku.
8. Babban Abu a nan wanda shi ake
nufi (a bayyana) shi ne abin
da suka nema irin abin da Banu
Isra'ila ne suka nema yayin da
suka ce da Musa, "Ka sanya mana
gunki....
9. Kore dukkan wani abu da aka kore,
yana daga cikin ma'anar
da 'La ilaha illallahu' ta kunsa,
tare da kasancewar abu da
boyuwarsa.(1)
____________________________
SHARHI
(1)Ma'ana ko ka faɗi kalmar shahada,
matuƙar ba ka kore albarka ga abin
da ba shi da albarka ba, to ba ka
tabbatar da haƙiƙanin ma'anarta ba.
****************************************************
10. Annabi (SAW) ya yi rantsuwa kafin
ya ba da fatawa. Domin
Annabi (SAW) ba ya rantsuwa sai idan
akwai maslaha a cikinta.
11. A cikin shirka akwai babba da
ƙarama saboda; ya nuna cewa
abin da sahabbai suka fadɗa ba su yi
ridda ba.
12. Faɗinsa "Ba mu daɗe daga
barin kafirci ba" ya nuna cewar
waɗanda ba farkon shigarsu ba, ba su
jahilci hakan ba.
13. Faɗin, "Allahu Akbar!"
yayin da abu ya ba da mamaki,
saɓanin waɗanda suke ganin makaruhi
ne.
14. Toshe dukkan wata kafar shirka.
Domin
315. Hani dangane da yin
kamanceceniya da mutanen jahiliyya.
16. Ya halatta ka yi fushi a halin
koyarwa idan ta kama.
17. Ɗaukar ƙa'ida gamammiya da faɗinsa,
"Lallai abu ne da ya
maimaitu."
18. Wannan alama ce daga alamomin
annabta kasancewarsa ya
faru, kamar yadda Annabi ya ba da
labari.(1)
_______________________
SHARHI
(1)Annabi (SAW) ya ba da labarin cewa
sai musulmai sun bi tafarkin yahudu
da nasara. Kuma ga shi a yau abin
yana faruwa. Ana gina masallaci a
makabarta, ana neman tabarrukin
kaburbura da sauran sunnonin yahudu
da nasara.
***************************************************
19. Duk abin da Allah ya zargi yahudu
da nasaraa cikin
Alƙur'ani, ya sanar da mu ne don kada
mu aikata.
20. Abu ne tabbatacce wurin sahabbai
cewa, ita ibada ana gina ta
ne a kan umami,(1)Sai ya
zamanto a cikin wannan akwai
faɗakarwa a kan tambayoyin kabari:
Amma tambayar, "Waye
Ubangijinka?" a fili take; amma
tambayar, "Waye
Annabinka? yana daga cikin labarin
gaibi da ya bayar; kuma
tambayar, "Menene
Addininka?" daga faɗarsu, "Ka sanya
mana abin bauta.. har zuwa ƙarshen
ayar.(2)
_________________________
SHARHI
(1)A ina muka fahimci wannan? Lokacin da
sahabbai suka ga bishiyar da
mushirikai suke neman tabarruki, da
addini kawai yadda a ka ga iyaye da
kakanni suke, haka ake yi, da kawai
sai su je kai tsaye su rataya! Amma
sai da suka tambayi umarnin Annabi
(SAW). Saboda sun san ibada sai da
umami ake yi. Sai Annabi ya nuna musu
yin hakan kuskure ne. Ashe ba a
ibada da son zuciya. Ka ga bambanci
muminan da, da na yanzu.
(2)Anan za a ga fikhun Malam, ta inda a
wannan hadisin yake nuna
tabbacin tambayar kabari. Duk
tambayoyin da za a yi, amsarsu sun fito a
hadisin.
*****************************************************
21. Lallai tafarkin yahudu da nasara
abin zargi ne, kamar tafarkin
mushrikai.
22. Duk wanda ya rabu da wata ɓarna,
kuma zuciyarsa ta saba da
wannan ɓarnar, to ba a amintuwa ya
zamanto akwai ragowar
wannan al'ada a zuciyarsa. Saboda faɗinsu,
"A lokacin ba mu
daɗe daga barin kafirci ba"
No comments:
Post a Comment