GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Apr 19, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYAR 5 )

Kira Zuwa Ga Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah
______________
Sharhi;
Wato idan muka lura jerin babukan littafinnan suna tafiya a tsari. Babin farko Malam ya yi bayani akan menene tauhidi, sannan ya kawo falalar Lauhidi da yadda yake kankare zunubi, sannan sai ya zo babin tsoron afkawa shirka, wanda yana daga kamalar tauhidi mutum ya dinga jin tsoron afkawa cikin shirka. To idan aka samu cikakken tauhidi da kuma cikkaken tsoron faɗawa cikin shirka, to ka zama kamili a karan kanka, saura kuma ka yi ƙoƙarin wane ma ya zama kamili. To shi ne malam ya kawo wannan babi na kira zuwa ga bautawa Allah shi kadai. Wato ka fahimtar da mutane saƙon da ka fahimta.
********************
Da faɗar Allah;
"Ka ce “Wannan ita ce turba ta (musulunci). Ina kira zuwa ga Allah,
bisa ga basira nake, ni da wanda ya bi ni, tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ni ba na daga cikin masu shirka.”(Yusuuf:108)
___________
Sharhi;
Basira: Wato gani. ldan kana gani, gani zai iya bambance maka launuka. Don haka, lokacin da kake da lafiyayyen ido, ba ka shakkar launin da kake gani. Haka kuma, basira yana nufin gani na ilimi, wato na zuciya. Don haka, kamar yadda idonka ba ya kokwanton wani launi idan ka gan shi, haka ma zuciyarka ba ta kokwanton abin da kake kira i zuwa gare shi tare da ilimi, musamman abin da ka fahimta. Kuma babu wani ilimi da zai ci sunan basira sai ilimin da wahayi ya tabbatar da shi. Annabi (ﷺ)  yana kira ne a kan abin da wahayi ya zo masa. Idan muka lura da wannan aya, ina ne yake da alaka da matashiyar maganarmu? Matashiyar muganar ita ce, da 'awa ilaa shahaadatu an laa ilaaha illallah. A cikin ayar kuma akwai, ad'u ilallaahi To wannan shi ne yake nuna cewa, mai da‘awa yana kira ne i zuwa ga Allah, ba ga kansa ko waninsa ba. Wannan yana da matuƙar muhimmanci saboda idan kana kira zuwa ga Allah, ko ka rasa wasu abubuwa na jin daɗin rayuwar duniya, to ba ka yi asara ba tun da ba ga kanka kake kira ba, a’a ga Allah kake kira. Don haka rashin cin nasara a duniyance ba zai sa ka ja baya ba don kimarka ba ta ragu ba. Don an zage ka, ko an ci mutumcinka. wannan ba zai sa ka daina ba. Amma idan don kanka kake kira aka zage ka, to ƙimarka ta ragu.
********************
An karbo hadisi daga Abdullalli ibn Abbas ya ce, yayin da, Manzon Allah ya aika Mu'azu zuwa ƙasar yamen. ya ce da shi‘ “Lallai za ka je wurin waɗansu mutanen da aka bu su littafi (yuhudu ko nasara). Ya zama farkon abin da zaka kira su da shi, shi ne su shaida babu abin bautawa da guskiya sai Allah. [Bukhari 1395 da Muslim #19]
__________
Sharhi;
Abdullahi ɗan Abbas (RA) ɗan baffan Annabi (ﷺ)  ne wato Abbas, don haka ɗan wa da ɗan ƙani ne shi da Annabi (ﷺ) . Yana cikin samarin sahabbai, Annabi (ﷺ)  ya bar duniya bai fi shekara ashirin a duniya ba. Yaushe ne Manzon Allah (ﷺ)  ya aiki Mu’az? A cikin shekara ta 10 bayan hijira clkin watan Rabi’ul Awwal da shi da Abu Musal Ash’ari (RA). Mu’az i zuwa garin San'a da sauran ƙauyukan da ke kusa da ita, shi kuma Abu Musal Ash’ari i zuwa garin Adan. Wannan na nuna falalar Mu’az.
********************
A wata ruwayar daban, ya ce masa, “Ka yi kira i zuwa su kaɗaita Allah shi kaɗai. To idan sun bi ka a kan wannan abin, sai ku shaida musu Allah ya wajabta musu salloli guda biyar a kuwane yini da dare. Idan sun yi maka biyayya a kan wannan, to ka sanar da su cewa Allah ya wajabta musu wata sadaƙa (zakka) wadda ake karba daga hannun mawadatansu a mayar da ita i zuwa mabuƙatansu. ldan sun yi maka biyayya a kan haka to lallai ka kiyaye musu daraja daga cikin dukiyoyinsu; ka kiyayi addu'ar wanda aka zalunta domin babu hijabi tsakaninta da Ubangiji"
_____________
SHARHI;
Shi ne malamai suke cewa, wannan yana nuna ilimin Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab. Yana so ya fassara mana menene Shahadatu an laa ilaaha illallaah, maimakon ya fassara ta da larabcinsa, sai ya fassara ta da ruwaya daga cikin ruwayoyin hadisi. 
Da wannan hadisi ne wasu malamai suke kafa hujjar cewa, ashe idan za ka kirayi mutum zuwa ga musulunci, za ka haɗa masa abubuwa gaba ɗaya ne, ko kuwa za ka yi masa ɗaya-bayan- ɗaya? Shi ne suka ce, ɗaya za ka ɗauka wanda ya fi kowanne muhimmanci, wato kalmar shahada. Kamar yadda Annabi (ﷺ)  ya ce, “Farkon abin da za ka kira su da shi, shi ne su shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah.” Wannan na nuna idan za ka kirayi mutum zuwa musulunci, ka fara da kalmar shahada, sannan sauran al’amura su biyo baya. Kuma yana nuna cewa, ana fara da’awa ne a kan tauhidi, sannan wanda ya fi muhimmanci, sannan mai bin sa wurin muhimmanci. Don haka, da’awar da ta kafu a kan Ƙur’ani da hadisi, ita ce ta fi kafuwa da cin nasara. Kuskure ne ka fara da’awa ba a kan tauhidi ba.
Idan an ce da dabba karima, to sai idan ta kasance tana da yawan nono, ko kosasshiya ce, ko yawan gashi ko yawan cin abinci. Duk Wannan siffofin dabbobin da makiyayi ya fi son su ne. Ƙa’ida idan ka zo za ka fitar da zakka, daga cikin abin da za ka fltar, ba za ka fltar da su ba, idan ka tashi za ka fitar ne daga tsakatsakiya, ba wadda ta fi Koshi ba, ba kuma wadda ta fi rama ba.
********************
Ya zo cikin Bukhari da Muslim, daga Sahl ibn Sa'ad, ya ce, Manzon Allah ya faɗa a ranar Khaibar ya ce, “Wallahi zan bayar da tuta gobe ga wani mutum wanda yake son Allah da Manzonsa, kuma Allah da Manzonsa suke son sa, Allah zai buɗe (Khaibar) a hannunsa.” Sai mutane suka kwana suna tattaunawa a daren, cewa shin wannensu ne za a ba wa wannan tuta. Yayin da sahabbai suka wayi gari, sai suka yi sammako zuwa wurin Annabi (ﷺ) , kowannensu yana son a ba shi. Sai Manzon Allah ya ce, “Ina Ali ɗan Abi Ɗalib?” Sai aka ce, ai idonsa ciwo yake, yana gida. Sai ya ce a je a zo da shi. Sai aka zo da shi, Annabi ya yi masa tofi (addu’a ko ruƙya). Nan take ya warke, (kai ka ce wani raɗaɗi bai .kasance tare da shi ba). Annabi ya ba shi tuta ya ce da shi, “Tashi ka tafi (da rundunar yaƙi), amma a nutse, har sai ka sauka a wajensu, sannan ka yi kiran su i zuwa musulunci, sannan ka labarta musu abin da aka wajabta a kansu na haƙƙin Allah a cikin musulunci. Wallahi! A ce Allah ya shiryar da mutum ɗaya ta hanyarka, shi ya fi maka alheri sama da jajayen raƙuma ". Bukhari #2942]
___________*
SHARHI;
Khaibar suna ne na wani gari da ke arewacin Madina a kan hanyar zuwa Tabuka ko Sham. Tsakanin garin da Madina taflyar kilomita 170 ne, mazauna ce ta yahudawa a da can, wuri ne mai yawan dabinai da dausayi.
Lafazin Annas a nan ana nufin sahabban Annabi (ﷺ)  Su duka ko waɗanda suke wurin ake nufi? Waɗanda suke wurin kadai ake nufi, amma an sa musu Annas. Wannan na nuna wani ɓangare na mutane ana iya kiran su da mutane, tare da cewa lafazin Annas ya shafi kowa da kowa; wanda yake wurin, da wanda ba ya nan; musulmai da kafirai. Shin duniya ta kwana ne tana tunanin waye Annabi zai naɗa, ko kuwa sahabban da suka fita suka kwana ne suke tunanin waye Annabi zai naɗa? Sahabban ne kawai. Domin wannan ya nuna Annas, ammun ne. Wato jam’i ne, amma ana nufin wasu keɓantattun mutane al-khas. A ruwayar Muslim, Umar ibn Khaɗɗab (RA) yake cewa, “Ban taɓa neman mulki ba a duniya, sai a wannan ranar. Ba wai don a ce ni ne kwamandan ba, sai don na san idan an ba ni tutar, to abin da aka faɗa na, ‘son Allah da Manzonsa’ to ya tabbata.” Sai dai kada mutum ya kafa hujja da wannan wajen takarar shugabanci. Abin da malamai suke kafa hujja da shi, shi ne duk abin da yake falala ne, to ba a yarda ka fifita wani a kansa ba. Wannan yana daga cikin abin da Imam Suyuɗi ya yi sharhi a kansa a babin ɗa’a. Ba a fifita wani, sai dai ka yi rige don ka fifita kanka a kan neman lada, na a kan samun duniya ba. A wata ruwayar aka ce wanda ya tafi ya taho da shi, shi ne Salmah ibn Al-Ak’wah ko Sa’ad ibn Abi Waƙas, ɗaya daga cikinsu ne ya yi masa jagora ya taho da shi. Duk sahabbai sun san cewa falalar ta Aliyu ce don haka, sai aka kawo shi, Annabi (ﷺ)  ya yi tofi a idonsa guda biyu, ruƙya kenan. Ka ga wannan yana nuna halaccin yin tofi, kuma ya nuna cewa ana iya yi ko da ba a kambun-baka ba ne ko harbin wani abu mai dafi ba. Ya yi masa addu’a, nan-take ya warke, kai ka ce wani raɗaɗi bai kasance tare da shi ba.
“Ka yi kiran su izuwa musulunci, sannan ka labarta musu abin da aka wajabta a kansu na haƙƙin Allah a cikin musulunci.” Nan ne (mahalus-shahid) lnda hujjar take. Shi ne malamai suke cewa, ba kowane irin mutum za ka faɗawa abubuwan da suka wajaba a kansa na addini ba. Hadisin guda biyu ne, ɗaya ya ce ka faɗa, na biyun ya ce kada ka faɗa, to haɗa su za a yi. Wato, idan hali ya kama a faɗa, ga irin mutanen da za a faɗa musu. A hadisin Mu’az, kowanne wuri akwai maganar da ta dace da shi. Wannan shi ne ƙashin-bayan hujja bisa ga cewa, ba ya halatta a fara yaƙar kafurai, sai idan an isar musu da musulunci sun ƙi, sannan sai a yake su. Don haka, da’awa ita ce take riga jihadi. Idan aka fara kiran mutane i zuwa musulunci suka ƙi yarda, sai a ce to su yarda za su ba da jizya a ƙyale su da addininsu. Amma idan suka ce ba za su karɓi musulunci ba, kuma ba za su ba da jizya ba, to sai a yaƙe su. A takaice dai, wannan hadisi na nuna kira zuwa ga musulunci, sannan falalar Ali ibn Abi Dalib (RA).
********************
A Cikin Wannan Babi Akwai Mas’aloli Kamar Haka;
1.   Kira zuwa ga Allah shi ne tafarkin wanda yake bin Manzon Allah (ﷺ) .
_____________
SHARHI;
Mun fahimci wannan a ƙarkashin ayar cikin Suuratul Yusuuf Dukkan mabiyin Manzon Allah (ﷺ)  yana kira ne i zuwa musulunci. Waɗansu malaman suka ce, abin da ya kamata malam ya ce, shi ne, kira zuwa ga Allah, shi ne tafarkin Annabawa gabadaya da waɗanda suka bi tafarkinsu. Ashe ka fahimci musulunci da sunna, ka yi aiki da su, kai kadai, wannan ba ya wadatarwa sai ka kirayi mutane zuwa ga musuluncin da sunnar gwargwadon halinka, matar ka za ka kirawo, ko yayyenka ko ƙannenka, ‘ya’yanka, makotanka. Wani sai ka ga ya fahimci addini, shi ne zuwa wajen karatun tafsir, karatun hadisi, da fiƙihu, amma gidansa zero ba komai a gidansa. Ta yiwu ka gan shi wajen karatu amma ɗansa yana filin kwallo, yana sanye da gajeran wando, ya yi aski irin na arna a kansa! To irin wannan da sauran sa. Yadda yake zuwa masallaci, to haka ya kamata ya sa yaransa a gaba ‘yan shekara 15, I8, 20 su taho tare. Wallahi, lalle ya kumata a gyara wannan, kowa ya tashi ya yi da’awa. Wani zai yi da’awar ne da ilimlnsa, wani da kuɗinsa, wani da duka biyun. Wanda duk ba ya da'awa ta kowacce irin salo, to wannan da sauran sa har yanzu.

2. Faɗakarwa zuwa ga Ikhlasi. Domin da yawan mutane za ka ga mutum yana kira zuwa ga musulunci, to amma a fakaice yana kira ne zuwa ga karankansa.

3. Lallai ita basira, tana cikin farillan abubuwa.
______________
SHARHI;
Basira a nan, ana nufin ilimi mai amfani. Farkon kalmar ilimi, shi ne ilimin musulunci. Sannan ilimin sanin halayyar jama’a, duk zai shiga ciki. Akwai lokacin da za ka san ilimin Alƙur’ani da hadisi, amma ba ka san ilimin mu’ amala da mutane ta yau da gobe ba, ballantana ka san ta yadda za ka kira su zuwa musulunci. Don Annabi (ﷺ)  ya bi salo daban-daban na kira zuwa musulunci. Akwai waɗanda ya kira su ta hikima, wasu ta wa’azi mai kyau, wasu ta jayayya, wasu ta kyauta, wasu tausasa zukatansu. Duk waɗannan daban-daban ne. Ashe da’awa ana bi ta mataki dabamdaban, mu ne muke ɗauka ta wa’azi kawai ake da’awa. Wa’azi ɗaya ne cikin hanyoyi ɗari na da’awa.
4. Abin da yake nuna kyautatuwar tauhidi shi ne kasancewarsa tsarkake Ubangiji daga nakasu.
5. Yana daga munin shirka, kasancewarta zagi ne ga Ubangiji.
6.Yana cikin muhimman mas’aloli, nesantar da musulmi daga masu shirka, ko ƙin zama da su, don kada ya zama ɗaya daga cikinsu’
______________
SHARHI;
Mas’ala ta hudu da ta biyar: Idan ka ɗau wata sifa ta Allah ka ba wa wani, to ka nuna gajiyawar Allah a siffar, don haka ka tauye masa wani haƙƙi nasa. Misali, idan ka ce, wani yana kula da halittu ba Allah ba, ka nuna gajiyawar Allah wajen kula da dukkan halittu. Wannan ita ce munin shirka, abin da malam yake nufi kenan a mas’ala ta biyar. Mas’ala ta shida, mun fahimce ta a karshen ayar babin. Wato faɗin Annabi cewa “...tsarki ya tabbata ga Allah, kuma ni ba na daga cikin masu shirka.” Don haka, dole mutum ya ƙauracewa masu shirka. ”
7. Kasancewar tauhidi shi ne farkon abin da yake wajibi.
____________
SHARHI;
Wannan daga umarnin da Annabi (ﷺ)  ya yi idan an je garin waɗanda ba musulmai ba. Sannan a nan za ka gane fahimtar mai Ahlari da ya ce, farkon abin da yake wajaba ga mukallafi shi ne inganta imaninsa (wato tauhidi). Ashe da tauhidi ake farawa kafin komai. Ka yi ta cewa mutum ya yi zikiri, nafila, bayan ba shi da tauhidi?! Abin da sai in da shi ne, zikirin da hailalar da salatin za su karɓu!
8. (Mai da’awa) zai fara ne da tauhidi kafin komai, har sallah ma.
9. Ma'anar kaɗaita Allah ita ce ma’anar, ‘Laa ilaaha illallaah. ’
10. Tana iya yiwuwa mutum daga cikin waɗanda aka ba wa littafi, amma bai san abin da littafin ya ƙunsa ba, ko ba ya aiki da shi.
11. Idan ka zo koyarwa, ka fara mataki-mataki.
12. (Idan za ka bi mataki-mataki), to za ka fara da mafi muhimmanci, sannan mabiyinsa, sannan mai bin sa.
13. An nuna waɗanda za a ba wa zakka.
14. Lallai malami ya yaye duk wani duhu ga wanda zai ɗauki karatu wurinsa.
__________
SHARHI;
To a ina muka fahimci wannan a cikin babin? Inda Annabi (ﷺ)  ya yi wa Mu’az bayani dalla-dalla yadda zai kira mutane. Ya fara da tauhidi, sannan sallah, da sauransu.
15. Ba a fitar da masu tsada cikin dabbobi, idan an tashi ba da zakka.
16. A tsoraci addu'ar wanda aka zalunta.
17. Labarin da Annabi ya bayar cewa, addu’ar wanda aka zalunta ba ta da hijabi.
18. Abin da yake nuna tsadar tauhidi, wajen tabbatar da shi sai an sha wahala, shi ne abin da ya gudana ga shugabannin manzanni da shugabanin waliyyan Allah (sahabbai) na wahala da yunwa.
___________
SHARH;
Shugabannin waliyyan Allah sune sahabbai. Duk wani waliyyi a bayansu yake. Annabi (ﷺ)  da sahabbansa sun sha wahala sosai a yaƙin Khaibar, Annabi shugaban manzanni ya sha wahala, sayyiduna Ali ya yi ciwon Ido duk don saboda tabbatar da tauhidi. Ashe tauhidi abu ne mai daɗi da sai an sha wahala za a tabbatar da shi.
19. Faɗar Manzon Allah (ﷺ)  na cewa zai bayar da tuta gobe wannan alamace daga cikin amomin annabta.
20. Wata alamar annabtar ita ce tofin da Manzon Allah (ﷺ)  ya yi wa Aliyu a idonsa nan take ya warke.
21. Falalar Ali (RA).
22. Falalar sahabbai ta yadda suke ƙoƙarin samo falala a cikin dare maimakon su shagaltu da busharar buɗe Khaibar.
23. Imani da ƙaddara. Ta yadda falala ta tabbata ga wanda bai neme ta ba, da rashinta ga wanda ya nema.
24. Annabi na nuna ladabi wurin yaƙi na cewa Ali ya bi a hankali.
25. Ana fara kiran mutane ne zuwa musulunci kafin yaƙi.
26. Ana shar‘anta jihadi ga waɗanda aka kiraye su tun kafin a yaƙe su.
27. Kira ga musulunci ana yin sa ne da hikima, kamar yadda ya ce, “Ka ba su labari da abin da yake wajibi.”
28. Game haƙƙin Allah a musulunci.
29. Ladan da yake tabbata ga mutum idan mutum ɗaya ya shiryu a hannunsa.
30. Halaccin rantsuwa a wurin yin fatawa.



(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

1 comment:

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...