Ba
A Yanka Domin Allah A Wani Wuri Da Aka Keɓance
Don
Yanka Domin Waninsa(¹)
_____________________
SHARHI
(¹)Wannan
babin zai yi magana a kan yanka ta ibada, wadda ba ta halatta a wajen da ake
yanka don wanin Allah. Misali wajen da mushirikai suke yanka don neman kusanci
da gunkinsu, ba ya halatta kai musulmi ka yanka ko da ragon layya ne a wajen!
Ragon layya, ragon suna, ko hadaya duk waɗannan
ana yin su ne domin Allah. Amma ba ya halatta ka yi waɗannan
yankan a wajen da mushirakai suke yin yanka, duk da cewa kai abin da za ka yi ɗa'a
ne.
**************************************************
Da faɗin
Allah,
"Kada ka tsaya a
cikinsa (masallaci) har abada…”
(2)
(At-Tauba: 107-108)
__________________
SHARHI
(²)Laa taƙum fihi abadan: Wannan aya na hani ga Annabi (SAW), yin sallah a wani masallaci da munafukai
suka gina, mai suna "Masjidu al-Dhirar, kamar yadda ya shahara a wurin malaman tafsiri da malaman tarihi.Waɗanda
suka gina masallacin, sun gina shi ne ba don neman kusanci ga Allah ba, sun
gina shi ne don su riƙa
haɗuwa su kawowa musulunci cikas, ko su
gayyaci Annabi (SAW)masallacin, su far masa don su kashe shi. Shi ne Allah ya
ce;
"Su ne waɗanda
suka riƙi
masallaci don cutarwa, don su bijire wa Allah da yunkurin raba kan musulmi; don
su mayar da masallacin wata cibiya ga dukkan mai gaba da Allah da Manzonsa; za
ka ji suna rantsuwa cewar babu abin da suka nufata sai aiki nagari. Allah ya
san ƙarya
suke yi. Kada ka tsaya a cikinsa (masallaci) har abada. Lallai masallacin da
aka aza harsashinsa a kan taƙawa
tun ranar farko, shi ne ya fi cancanta ka tsaya ka yi ibada a cikinsa. A
cikinsa akwai mazaje da suke tsarkakewa, Allah yana son masu tsarkakewa."
(At-Tauba: 107-108) Don haka, idan ya kasance masallaci ne, kuma manufar da aka
gina shi ta tashi daga manufar da aka sani, ta koma irin waccan guda huɗu
da ayar ta lissafa:
a. Rikar masallaci don cutarwa.
b. Bijire wa Allah.
c. Yunƙurin raba kan
musulmi.
d. Mayar da
masallacin wata cibiya ga dukkan mai gaba da Allah da Manzonsa. Sai aka hana
Annabi ( tsayawa ya yi ibada. To tun da sallah ma an hana ka yi ta a wurin da
aka gina ba don Allah ba, haka ma yanka ibada ne, ba ya halatta ka yi shi a
wurin da ake yin yanka ba don Allah ba.
Wannan shi ne alaƙa tsakanin ayar da
matashiyar maganar. A nan wajen za ka gane fiƙhun Sheikh Muhammad ibn
Abdulwahab, ya ƙulla
babi, kuma ya kawo aya da take da alaƙa da babin.
*************************************************
An karɓo
hadisi daga Thabit ibn Dhahhak (RA) ya ce,"Wani mutum ya taba yin bakance
zai yanka raƙuminsa
a wani wuri da ake kira Buwana, (wuri ne da yake kusa da Makka). Sai ya tambayi
Manzon Allah (SAW) a kan haka. Sai Annabi ya ce, "Shin akwai wani
gunki na mutanen
jahiliyya da ake bauta wa a wurin? Sai sahabbai suka ce, "A'a! Babu."
Sai ya ce, "Shin akwai wani Idi da mutanen jahiliyya suka saba yi a
wurin?" Sai suka ce, "Babu!" Sai Annabi ya ce, "Tafi ka
cika bakancenka. Lallai babu ciko ga dukkan bakancen
da aka yi shi, in dai
akwai saɓon Allah, ko cikin abin da dan Adam bai
mallake shi ba." Imam Abu Dawud [#3313] ne ya ruwaito shi, kuma sanadinsa
ya kai sharaɗin Bukhari da Muslim.(1)
______________________
SHARHI
(1)Ibn
Hajar ya inganta shi, haka Sheikh Nasiruddeen Albani [Duba Mishkatul Masabih
#3437].
Wannan hadisin na
nuna halaccin yankan raƙuma
don Allah, amma kuma yin sa a wurin da ba ayi don Allah, bai halatta ba. Yanzu,
ga shi wannan mutumin ya yi bakance, amma ya ce sai ya je gari kaza zai yanka,
sai Annabi (SAW) yake bincikar menene ya sa sai ya je wannan garin, shin akwai
wani gunki a wannan gari? Ka ga idan akwai, Manzon Allah (SAW) ba zai bar shi
ba. Shin akwai wani idi ko bikin jahiliyya da ake yi a wannan gari? In dai
akwai, Annabi ba zai bar shi ba. Mahallush-shahid a nan wurin shi ne dukkan
wurin da ake yin saɓon Allah, ba ya
halatta ka je wurin, ko da bauta wa Allah za ka yi.
Shi ne malamai suka
faɗaɗa
wannan, suka ce, yana daga cikin wannan ko kama da haka, yadda aka karhanta
mana sallah lokacin hudowar rana da faɗuwarta.
Annabi (ya ce, domin a wannan lokacin masu bauta wa rana suke faɗuwa
su yi mata sujjada. Duk da cewar lokacin da muke faɗuwa
Allah muke yi wa, amma sai aka hana mu.
Domin a zamanin, idan
muka yi sujjada, za ta yi kamanceceniya da ta masu bautar rana, sai Annabi
(SAW) ya karhanta mana yin sallah a wurin, duk da cewa sallah ibada ce. Wato
kenan, wannan na nuna yanke alaƙa
ta dukkan kamanceceniya tsakanin al'ummar musulmi da wadda ba ta musulmi ba.
Domin al'ummar musulmi, al'umma ce mai cin gashin kanta, ba wadda take rataye
da wata al'umma ba.
Sannan kuma, bakance
ibada ce, kuma kamar yadda ma'anarsa take, shi ne mutum ya lazumtar wa kansa
ibada wadda ba wajibi ba.
Bakance iri biyu ne:
Mu'allak ko Ghair Mu'allak.
a. Mu'allak: Misali,
kana da ɗan uwa a asibiti, ka ce, matuƙar wane ya warke daga
cuta, na yi alkawari tsakanina da Allah, sai na yanka rago, na yi sadaka da
shi. Ka ratayar da sadaƙar
ragon da warakar ɗan uwanka. Ko matarka
tana da juna biyu, ka ce, matuƙar
matata ta haihu lafiya, na yi alƙawari tsakanina da Allah, sai na yi
azumin kwana uku. Ka ratayar da azumtar kwana uku da saukar matarka lafiya. Ba
wajibi ba ne a kanka, amma tana sauka lafiya, ya zama wajibi sai ka yi. Haka,
daga ranar da ɗan uwanka ya tashi daga rashin lafiya,
ya zama wajibi sai ka yanka rago. Irin wannan makruhine a kanka, amma in dai ka
yi, sai ka cika.
b.Ghair Mu 'allak:
Misali, kana zaune sai ka ce, "Na-ji-na-gani, zan yantar da bawana
wane." "Na-ji-na-gani, zan yi azumin kwana uku." Ka lazimtar wa
kanka ba tare da ka rataya shi da wani amfani da kake son samu a duniya ba.
Irin wannan bakancen babu karhanci a ciki.
Cika bakancenka:
Wannan umarni ne, kuma dukkan umarni in dai ya zamanto babu wata ƙarina tare da shi, a
kan ɗauke shi a matsayin wajabci. Ba a cire
shi daga wajabci zuwa wani abu daban, sai idan akwai ƙarina
da ta hana wajabci. To a nan umarni ne na wajabci? Shin lallai ne mutumin sai
ya cika bakancen a wannan wurin? Abu ne guda biyu, bakance kansa, da wurin da
ya ce zai yi bakancen. Lokacin da ya yi tambaya a kan abu guda biyu ne: Yanka
raƙuma
da wurin da zai yanka.
To da Annabi ya tashi
yin tambaya, bai yi a kan raƙuman
ba, sai ya yi ta a kan wurin. Da ya gama gamsuwa da wurin da za a yanka, sai ya
yi umarni a kan cewa, "Cika bakancenka." To wannan umarnin shin ya
shafi har
raƙuman ne tare da wurin
ko kuwa wurin kawai? Ka ga ya shafi duka biyun ne; idan muka kalli raƙuman, ya shafi
wajabci ne, idan kuma muka kalli wurin, ya shafí halacci.
Ba a cika bakance,
idan mutum ya yi bakancen zai saba wa Allan Haka kuma ba a cika bakance cikin
abin da mutum bai mallake shi ba Kamar ka ce, "Idan wane ya warke, sai na
'yanta bawan wane sadaƙaTun
da ba naka ba ne, bai zama bakance ba.
A Cikin Wannan Babi
Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Tafsirin ayar,
"Kada ka tsaya a cikinsa (masallacin) har abada"
2. Sabo yana yin
tasiri a wurin da ake yin sa. Haka ɗa'a
ma tana da
tasiri
3. Juyar da mas'ala
mai rikici i zuwa ga mas'ala mabayyaniya don warware rikicin.( Wato abin da
malam yake nufi a nan, shi ne, da ya ce ba a yanka wajen da ake bautar wanin Allah,
wannan zai wahala a fahimta,
Amma da ya alaƙanta da hukuncin
sallah, wato, La taƙum
fihi abadaa... sai abin ya fito fili.)
4. Mai fatawa ya
halatta ya yi tambaya ga wanda ya yi masa fatawa, idan ya buƙaci hakan. (Mun
fahimci wannan, ta inda Annabi (SAW) ya tambayi wanda ya yi
bakance wasu bayanan
kafin ya ba shi amsa).
5. Kebance wani gari
ko wuri da bakance, wannan babu laifí a shari'a, matuƙar ba wurin sabo ba
ne.
6. An hana cika
bakance a wuri, matukar akwai gunki a wurin na jahiliyya ko da a lokacin babu
shi
7. Hana yanka ko cika
bakance a wurin da maguzawa suka saba yin biki ko idi ko da bayan gushewarsu.
8. Ba ya halatta
mnutum ya cika bakancensa a irin wannan wuri na saɓo,
domin bakancen saɓo ne.
9. Hani dangane da
kamanceceniya da kafirai a cikin idinsu, ko da a zuci mutum bai yi nufin haka
ba.
10.Ba a yin bakance
cikin abin da ya kasance saɓo ne.
11.Ɗan Adam ba ya yin
bakance cikin abin da ba mallakarsa ba ne.
No comments:
Post a Comment