Yin Yanka Don Wanin Allah(1)
__________________
SHARHI
(1)Wannan babin zai magana ne a kan ayoyi da hadisai da suke magana a
kan yanka ba don Allah ba. Mutum ya yi yanka ba don Allah ba. To
menene hukuncin hakan? Malamai sukan yi babi irin wannan ba tare da
sun faɗi hukunci ba, ko haram ne, ko halal, ko shirka da sauransu, su
kyale ka, su dogarar da kai da nassin da zai biyo baya. Nassosin da za su
zo, za su nuna maka yanka haƙƙi ne na wa? Idan ya tabbata yanka haƙƙi
ne na Allah (SWA) shi kaɗai, to yin yankan don wanin Allah ya zama
shirkakenan.
Yanka, iri biyu ne. Akwai yanka da nufin ibada, shi ne mutum ya
kwantar da dabba ya yanka ta, da niyyar neman kusanci da Allah (SWA).
Kamar layya, hadaya, yankan suna ko fidiya, to irin wannan ba a yi wa
kowa sai Allah. Idan wani ya yi irin wannan yankan ga wanin Allah, to ya
yi babbar shirka mai fitar da mutum daga musulunci. Wanin Allah ya
hada da Annabi, mala'ika, shehi, aljani, ko wanene mutukar ba Allah ba
ne. don Labarawa a da, sai su yi ta kiwon dabba, sai ta girma a ƙarshen
shekara su zo su yanka ta ga gunkinsu don neman kusanci da gunkin.
Wannan babbar shirka ce. Har yanzu ma cikin masu karrama waliyyai
akwai masu yin haka, dabbar ma ba a yanka ta sai an je daidai kabarin
waliyyin, don a nuna neman kusanci da waliyyin. Wannan ma babbar
shirka ce ƙarara don bauta ce ga wanin Allah.
Akwai kuma yanka na dabi'a, misali mutum ya yanka kaji, ko
dabba saboda baƙi da zai yi, wannan ba komai, zai sami lada ma na
girmama baƙo.
*************************************
Da faɗar Allah;
"Ka ce, "Lallai sallata, da yankana, da rayuwata da mutuwata na
Allah ne, shi kaɗai Ubangijin halittu, ba shi da abokin tarayya, da
haka aka umarce ni, kuma ni ne farkon musulmi."(Al-An'aam 162-163)
____________________________
SHARHI
Kul inna salati: As-salat tana da ma'ana guda biyu, ta farko addu'a, ta
biyu ibada. Shin sallah da ma'anar addu'a ake nufi ko ibada? Wato wata
sananniyar ibada, ana buɗe ta da kabbara kuma a rufe ta da sallama.
Saboda haka, duk inda aka samu ma'anoni guda biyu, to ana nufin ta
shari'a, domin ita ake gabatarwa sama da ta Larabci. Domin Annabi (SAW)
ya zo ne ya koyar da shari'a ba Larabci ba.
Wa nuskii: Ana nufin ibada. A shari'ance ana nufin yanka.
Sheikhul Islam Ibn Taimiyya a wannan ayar yake cewa, Ubangiji (SWA) ya
haɗa tsakanin manya-manyan ibadu biyu: Mafi girman ibadar gangar jiki
ita ce sallah, sannan kuma mafi girman ibada ta dukiya, ita ce yanka,
domin neman kusanci a wurin Allah (SWA). Amma wasu suka ce zakka ta fi,
Allah ne masani.
Wa mahyaya: Abin da zan gudanar a rayuwata.
Wa mamatii: Kuma abin da zan mutu a kai ina ta yi. Domin ibada
ana yin ta ne har iya rayuwa, ba a dainawa. Shi ya sa Allah (SWA) ya ce
Ka bautawa Ubangijinka har sai yaƙi ni (mutuwa) ya zo ma" (Hijr:99)
Lillahi Rabbil Aalamin: Ya zamanto na Allah ne Ubangijin halitta.
Wabizaalika umirtu: Da haka aka umarce ni. Ya zamanto ibada
gabadayanta ta Allah (SWA) ce. Wannan shi ne Ikhlasi.
Wa ana awwalul muslimina: Kuma ni ne farkon musulmi. Me ake
nufi da farkon musulmi? Ko dai wannan ta zama awwaliyyatul
zamaniyyah ko awwaliyatul ma 'ana wiyyah. Awwaliyatul zamaniyyah shi
ne ya zamanto kafín a samu kowane mutum, Annabi ne farkon musulmi.
Awwaliyatul Ma'anawiyyah, wato kafinsa an yi wasu Annabawa da
al'ummomi da Alkur'ani ya nuna, amma musuluncinsa shi ne ya fi cika da
batsewa. A nan ma'ana ta biyu ake nufi. Domin idan ka ɗauki ma'ana ta
farko, ta saɓa wa ayoyin Alkur'ani. Awwaliyyatul zamaniyya ya nuna
cewa kafin sa an yi wasu Annabawa da al'ummomi da Alkur'ani ya nuna.
Duk inda aka kawo kissa, sai an faɗa wa Annabi (SAW) cewa ba ka nan
sanda abin ya faru, domin a nuna cewa akwai mutane da aka yi kafinsa.
Saboda haka, Annabi ba shi ne farkon mutane ba. Maganar cewa Annabi
shi ne farkon halitta, wannan magana ce mara asali. Hadisin Baihaƙi da
ya nuna haka, hadisi ne mara asali kuma na ƙarya [Duba Silsilatus Sahiha
#458]. Amma hadisi ingantacce, shi ne farkon halitta shi ne alkalami.
Allah ya ce da alƙalamil, "Rubuta duk abin da zai faru a duniya." [Duba
Sahih A-Jami 'us Sagir hadisi #3780] Hakan ya faru tun kafin a halicci
sama da ƙasa da shekara dubu hamsin (50,000) kamar yadda Annabi (SAW)
ya faɗa. Wannan ya nuna cewa ba shi ne farkon halitta ba. Kuma don an
ce ba Annabi (SAW) ba ne farkon halitta, ba ya nuna ba ka yabe shi ba. Allah
ya yi masa baiwa ba adadi wanda ba sai an ƙrƙiro ƙarya an jingina masa
ba sannan za a nuna fifikon Annabi (SAW). Allah ya sa mu gane.
********************************
Da faɗin Allah;
"Ka yi sallah domin Ubangijinka, kuma ka yi yanka domin
Ubangijinka."" (Al-Kauthar 2)
_____________________
SHARHI
Ayar farko da ta biyu, an nuna sallah da yanka haƙƙi ne na Allah (SWA).
Daga waɗannan ayoyi, za mu fahimci cewa domin Allah ne kaɗai ake
yanka, kishiyar haka kuma shirka ce mai fitar da mutum daga musulunci,
kamar masu yin yanka don aljani da kuma bokaye. Wanda galibi da
lokacin siyasa za ka ga ana ta yanka saboda aljani ko boka, don neman
biyan buƙatar 'yan siyasar da ba ruwan su da Allah. Ka ga ana ta yanka
jaki, da dabbobi, har ma mutane manya da yara, da jarirai. Ka ji ana ta
cigiya a filin sanarwa, amma ba a ga mutum ba, an yanka shi. Wannan
duk bauta ce ga aljanin da ya shar' anta yanka. Sai ka ga mutum ya aikata
haka, ya ci dan majalisa, ko gwamna, amma ya fita daga musulunci!
******************
An karɓo hadisi daga Aliyu ibn Abi Ɗalib ya ce, "Manzon
Allah (SAW) ya yi mini magana da kalmomi guda huɗu, "Allah ya
la'anci wanda ya yi yanka domin wanin Allah; Allah ya la'anci
wanda ya zagi mahaifansa biyu; Allah ya la'anci wanda ya ba da
kariya ga mai ɓarna; Allah ya la'anci wanda ya canza iyakoki
ƙasa." Muslim [#1978] ne ya ruwaito.
_____________________
SHARHI
Aliyu ibn Abi Dalib (RA), ɗaya daga cikin Khulafa'ur rashidun, ɗaya
daga cikin Al-ashratul-mubassharuna bil Jannah, kuma farkon wanda ya
musulunta cikin yara kanana, sirikin Annabi (SAW), mijin 'yarsa Faɗima
ya halarci yaƙiin Badar, yana cikin waɗanda suka halarci Bai'atur
Ridhwan kuma ya mutu shahidi, Abdurrahman ibn Muljim ne ya kashe
shi, a cikin watan Ramadan, shekara ta 40 bayan hijra.
Idan an ce la'anta, wato ana nufin korar mutum daga rahamar
Allah. Wato, Ubangiji ya nisantar da shi daga rahamarsa.
Allah ya la 'anci wanda ya yi yanka ba don Allah ba: Ya zamanto
ya yi domin neman kusanci a wurin wanin Allah; ya kasance mutum ne,
aljan ne, mala'ika ne ko ma dai wanene. Shin wanne ne ya fi girman laifi
tsakanin mutumin da ya yi nufin ya yi yanka, a zuciyarsa ba ya nufin
Allah, amma a wajen yanka sai ya ce, Bismillahi' da mutumin da ya yi
nufin yanka a zuciyarsa yana nufin Allah, amma a wajen yanka ya ce,
Bismil-Lat, ko Bismi-Manat' ko Bismi-Uzza?' Na farko dai shirka ya
yi, duk da ya ambaci Allah. Abin da ya yanka, daidai yake da abin da aka
yanka don wanin Allah. Ambatar sunan Allah da ya yi, ba ya kare
wancan. Na biyun kuwa sabo ya yi, yana da laifi, amma bai kai wancan
ba. Amma kuma wanda ya yi yanka domin ya girmama wani da nama,
amma a zuciyarsa ba da nufin ibada ba, don ya ciyar da mutane, wannan
ba zai shiga nan ba, domin da niyyar ihsani ya yi kuma zai samu lada
daidai niyyarsa. Abin da hukunci yake hararowa tsakanin aikin zuci da na
harshe, shi ne maganar zuci, wato niyya.
Allah ya la 'anci wanda ya zagi mahaifansa biyu. Duk lokacin da
aka ce mahaifi, kaka yana ɗaukar mahaifi, kamar yadda kaka mace tana
ɗaukar mahaifiya. Zagin mahaifi da zagin kaka, duk yana shiga cikin
wannan ma'anar. Haka zagin mahaifiya da zagin mahaifiyar uwa, shi ma
yana shiga ciki. Duk da cewa girman haƙƙi, yana tabbata ne ga abin da
yake uba na kai-tsaye, kafin kaka na ɗaya, biyu har na ƙarshe. Abin da
la anta take nufi a nan, zagi. Wato, lafazin la'ana' yana ɗaukar ma'ana
guda biyu: Korewa ga barin rahamar Ubangiji, da kuma zagi.
La'antar da aka jingina wa Allah, la'anta ce ta kore mutum daga
rahamar Allah. Sannan la'antar da ake jingina wa mutum na ɗaukar zagi
ko addu'a da la'anta. Annabi (SAW)ya fayyace abin a sarari cikin hadisi, da
ya ce, yana daga cikin manyan kaba'ira mutum, ya zagi mahaifansa. Sai
sahabbai suka ce, "Ta yaya mutum zai zagi mahaifansa? Sai Annabi ya
ce, "Kamar mutum ne ya zagi mahaifan wani, sai wancan ya rama a kan
mahaifansa." [Bukhari #5973] To ka ga, ba ya halatta yawan zagi.
Allah ya la 'anci wanda ya ba da kariya ga mai ɓarna: AI-Ihdathu
fiddeen, shi ne ƙirƙiro wani abu cikin addinin musulunci. Don haka, mai
bidi'a ake kiransa muhdith. Ko ya zamanto 'muhdith, mutumin da
yake kawo fasadi a cikin ƙasa. Misali, mutum ne yake sayar da barasa, sai
ka ba shi gidan haya; mace ce take zaman banza, sai ka ba ta gidan haya;
mutum ne ya saci kuɗin banki, sai ka je ka tsaya, ka karɓe shi beli. Ka ga
abin da ka yi, ka taimaki mai ɓarna, ko dai mai ɓarna ta fuskar addini, ka
taimake shi wajen yada bidi'a ko kuma mai ɓarna ta fuskar fasadi a cikin
ƙasa, ya ƙirƙiro zunubi, ya sanya mutane su rinƙa yi, ko yana sayar da
barasa, kwaya ko miyagun kwayoyi, ka ba shi mafaka, to la'anta ta hau
kanka. Laifi ne mai girma taimaka wa bidi'a, don shaiɗan ya fi son bidi'a
fiye da aikin saɓo, kamar yadda Sufyan ibn Uyainah ya ce, "Iblis ya fi son
bidi'a sama da aikin saɓo. Saboda galibin aikin saɓo ana tuba, amma
bidi'a kuwa ba a tuba." Domin mai aikin saɓo, ba zai yi inda za a gan shi
ba, amma mai yin bidi'a kuwa, sai ya shiga masallaci zai yi, har sai ya yi
mata alwala wani lokacin." Yanzu waye ake sa ran tuba tsakanin mai
bidi'a da mai saɓo? Shi mai saɓo ya san cewa laifi yake yi, don haka,
yana sa ran zai tuba. Amma kuwa mai bidi'a, shi gani yake yi ibada yake,
yana ganin abin da yake yi ɗin nan mai kyau ne.
Shi mai bidi'a, takara yake da Annabi (SAW), don Annabi zai cewa
mutane, "ku yi sallar walaha akwai lada, raka'atanil fajr ta fi duniya da
abin da yake cikinta, shafa'i da wuturi akwai lada,'wanda ya yi raka'a 12
a yini, na lamince masa shiga aljanna, biyu kafin Azzahar, huđu bayanta,
biyu bayan Magariba, biyu bayan Isha', sai raka 'atanil fajr." Da sauran
ayyuka kamar su salati da hailala da sauransu. To shi ma ɗan bidi'a sai ya
koma gefe ya ƙirƙiro nasa salatin daban, nasa tasbihin daban, nasa zikirin
daban, kuma ya ba su lada irin yadda Annabi ya ba wa nasa lada! Kai har
ma ya fi na Annabin lada! Shi ne Imam Malik ibn Anas yake cewa,
"Wanda duk ya ƙirƙiro bidi'a ya ce kyakkyawa ce, abin da yake nufi
Annabi ya ha'inci aikensa." Don Allah ya ce:
A yau na cika muku addininku.."(Maa'ida:3)
Sai wani ya z0 daga baya, bayan Annabi ya cika risala, kuma sai ya ce ga
wani salati, ko wuridi, ko wani abu kyakkyawa wanda Annabi bai gano
shi ba! Haka kuma ya ba wa ƙirƙirarren salatinsa sharaɗi sama da na
Annabin. Annabi yana ambaton Allah a kowane hali kamar yadda A isha
(RA) ta fada [Abu Dawud #18], ma'ana ko yana da alwala ko ba shi da ita.
Amma dan bidi'a sai ya kawo wani zikiri ko salati ya ce, "ba a yin sa sai
da tsarki na ruwa,' wato sai da alwala, ba a yi masa taimama! Shi ya sa
Allah ya la'anci mai taimakawa bidi'a, to ina ga me yin bidi'ar?!
Ya kamata mutum ya guji bidi'a, tun asalinta don kada ya faɗa
ciki. Duk abin da aka ce bidi'a ne, mutum ya yi ƙoƙarin kaucewa faɗawa
ciki.
Allah ya la 'anci wanda ya canza iyakokin ƙasa: Ma'ana mutum ya
canza iyakokin gonarsa da ta makwabcinsa, ko filinsa da na
makwabcinsa, ko iyakokin gidansa da na makwabcinsa. Duk mutumin da
ya yi wannan Allah ya la'ance shi. Misali an raba fulotai an ba wa kowa,
sai ka zo ka shiga cikin fulotin ɗan uwanka da taku ɗaya, to la'anta ta hau
kanka. To yanzu wanda ya ƙara iyaka ne ake magana a kansa, ina ga
wanda yake cinye wa mutane fulotai? Yanzu akwai mutanen da sun
shahara wajen cinye fulotan jama'a. Akwai wanda zai je ya sami filinka a
bayan gari, kawai ya je ya fara gini! Yaje ya sami ma'aikata maha'inta ya
yi bincike, a wane lokacin aka yanka filin, yaushe aka ba ka filin? Sai ya
sa a rubuta masa wata takardar da ya yi backdating din takardar, ya zamo
ya riga ka mallaka. Yanzu kai takardarka ko kimar takardar kosai ba ta da
ita! Shi wannan ya canza iyakar ƙasa, la'antar Allah ta hau shi. Shi kuma
ma'aikacin gwamnatin ya taimakawa mai ɓarna, shi ma ya shiga la'antar
jimlar baya.
Duk abin da za ka samu a rayuwa, na ƙwace filayen jama'a da
gidajensu, to yaushe ne shekarun da za ka zauna a gidajen? Sai ka ga
mutum ya mutu ya bar fuloti 40 ko 80, duk na wuru-wuru da cuku-cuku
da maguɗi, kuma yanzu hisabi yana jiransa gobe ƙiyama. Idan ka yi
wannan da, abin da zai sa a karɓi tubanka ba istigfari da hailala ba ne.
Wallahi idan kullum za ka yi istigfari miliyan, Ubangiji ba zai yafe maka
ba! Sai ka mayar da fulotin ga mai shi, ko kimar kuɗin fulotin ga mai shi,
idan ba ya nan, to ga magadansa, idan ba sa nan ga magaɗansu. Idan duk
ba ka san su ba, to ka ware kudɗn ka yi sadaka da su, Allah ya kai masa
ladan. Wallahi sai ka yi haka Allah zai yafe ma! Amma istigfarinka da
hailalarka, wallahi ba zai tsamar da kai gaban Allah (SWA) ba, kai da duk
waɗanda suka ɗaure ma gindi.
************************
An karbo hadisi daga Darik ibn Shihab ya ce, Manzon Allah
(SAW) ya ce, "Wani mutum zai shiga aljanna a sanadiyyar ƙuda, kuma
wani mutum zai shiga wuta a sanadiyyar ƙuda." Sai sahabbai suka
ce, "Yaya haka za ta faru, ya Ma'aikin Allah? Sai ya ce, ""Wasu
mutane guda biyu sun wuce inda wasu taron jama'a suke, suna da
wani gunki, ba sa barin kowa ya wuce ta wurin, sai mutum ya
gabatar da wani abu ga gunkin don neman kusancinsa. Sai suka ce
da ɗaya daga cikin waɗannan mutanen biyu ya gabatar da wani abu
ga gunkin nan. Sai ya ce, "Ba ni da komai da zan gabatar." Sai suka
ce da shi, "Ko da ƙuda ne (ka kashe ka gabatar)." Sai ya gabatar da
ƙuda, sannan suka buɗe masa hanya ya yi tafiyarsa." Sai Annabi ya
ce, "Don haka zai shiga wuta! Sai suka ce da ɗayan shi ma ya
gabatar da wani abu, sai ya ce "Babu yadda za a yi na gabatar da
wani abu ga wani ba Allah ba." Sai suka fille masa kai, sai ya shiga
aljanna!" Imam Ahmad ne ya ruwaito. [Cikin littafinsa Azzuhud
Shafi na 22]
_________________________
SHARHI
Darik ibn Shihab, wato Abu Abdullahi Al-Badali al-Ahmusiy. An yi
saɓanin kasancewarsa sahabi, amma galibin malamai sun ce sahabi ne, ya
ga Annabi, sai dai bai samu jin hadisi daga wurin Annabi ba. Ga shi ya
ruwaito hadisi daga Annabi (SAW), ya zama Mursal kenan. Amma ga ƙa'idar
malaman hadisi, Mursal ɗin hadisi daga wurin sahabi karɓaɓɓe ne a
zance mafi inganci. Ya ji hadisin ne daga wurin Salman al-Farisi, shi
kuma daga Annabi, duk da bai ambaci sunansa ba. Imam Ahmad ne ya
ruwaito shi a cikin Kitab al-Zuhud da kuma Abu Nu'aim a cikin littafin
Hilyatul Auliya' [J1/203). Kuma malamai sun yi saɓanin ingancinsa.
Waɗansu malaman suna sahihantar da shi, haka ma Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab yake ɗaukarsa, don ya yi istinbaɗin hukunce-hukunce a ciki.
********************************************
A Cikin
Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Tafsirin ayar, Ƙul inna salati...
2. Tafsirin ayar, Fa salli lirabbika wanhar.
3. Farawa da la'antar wanda ya yi yanka ba don Allah ba.
4. La'antar wanda ya zagi mahaifansa. Yana shiga cikin wannan,
ka zagi iyayen mutum, shi ma ya zagi iyayenka.
5. La'antar wanda ya taimaki mai barna (ko dan bidi'a ko mai
sabo wajen aiwatar da sabonsa). Shi ne mutumin da zai farar
da wani abu wanda hakkin Allah ya zama wajibi a kansa, sai
ya fake da wani zai ba shi kariya don ya sarayar da haƙƙin
Allah a kansa.
6. La'antar mutumin da ya canza iyakar ƙasa. Shi ne iyakoki da
ake don su rarrabe iyakokinka da na makwabeinka; canza
iyakar shi ne jinkirtawa ko shigarwa.
7. Bambance tsakanin la'antar masu saɓo a jumlace da wani
mutum sananne guda ɗaya.
8. Wannan ƙissa mai girma, ita ce ƙissar ƙuda
9.Kasancewar wanda ya shiga wuta, zai shiga ne sanadiyyar
gabatar da abin da bai yi nufi da bauta ba, ya yi haka ne don
ya nisanci sharrinsu.
(A nan ne aka ci gyaran Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab cewa, inda
a ce mutumin nan da ya yanka ƙuda a cikin zuciyarsa, bai yi nufin ibada
ba, amma ya yi don ya tsamar da kansa daga mutanen, wannan ba zai sa
ya rasa imaninsa ba. Domin ga ƙa'ida dukkan mutumin da ya aikata wani
abu don jin tsoron sharrin waɗansu, Ubangiji ba ya kama mutum da
wannan. Ubangiji ya ce "Wanda ya kafircewa Allah bayan imaninsa, sai dai wanda aka tilasta shi
alhalin zuciyarsa ta nutsu da imani, (wannan babu komai a kansa).
(Nah:106)
Wannan shi ne amanar ilimi, don Sheikh Muhammad ibn Abdulwahab ya
yi kuskure a nan to ba za mu bi shi ba. Sai mu roki Allah ya yafe masa, ba
ma yin taƙalidanci. Wannan ita ce da'awar sunna.)
10.Muminai sun gane girman shirka a zukatansu. Saboda yadda
wancan ya haƙura aka kashe shi, bai yarda ya goyi bayansu a
kan abin da suka nema ba, duk da cewa abin da suka nema
aiki ne na zahiri.
11. Wanda ya shiga wuta ɗin musulmi ne, domin da kafiri ne, to
da ba za a ce ya shiga wuta saboda ƙuda ba.
12. A cikin wannan hadisi akwai shaida dangane da wani hadisi
ingantacce da Annabi yake cewa, "Aljanna tana kusa da
ɗayanku sama da hancin takalminsa. Haka wuta ma." [Duba
Sahih Ibn Hibban #661]
13. Gane cewa aikin zuci shi ne babbar manufa, har a wurin
masu bautar gumaka.
Muna godiya
ReplyDelete