TOFI DA LAYA
Ya zo cikin hadisi
tabbatacce, daga Abu Bashir al-Ansari
cewa, ya kasance tare
da Manzon Allah (SAW) cikin wasu tafiye tafiyensa, sai Annabi ya aiki wani ɗan aike
na musamman
kada a kyale wata igiya
da aka yi ta da tsarkiya ko abin wuya
tsarkiya a wuyan wani
raƙumi sai an cire ta ko kuma kowane abu na wuya sai an cire.
_________________
SHARHI
Wannan hadisi Bukhari
[#3005] da Muslim [#2115] ne suka ruwaito shi. Abu Bashir al-Ansariy, aka ce
sunansa Ƙais ibn Ubaid kamar yadda ibn Sa’ad ya faɗa a cikin Ɗabakat, amma ibn Abdul Barr ya ce,
bincike bai gano mana sunansa ba, an san shi dai da alkunyarsa Abi Bashir al-Ansariy.
Malamai suka ce,
abin da hadisin yake nunawa, shi ne su Larabawa a lokacin jahiliyyarsu, irin tsarkiya da take jikin baka, idan za a canza ta yayin da ta tsufa, sai a rataya ta a wuyan dabba, wai mayu ba za
abin da hadisin yake nunawa, shi ne su Larabawa a lokacin jahiliyyarsu, irin tsarkiya da take jikin baka, idan za a canza ta yayin da ta tsufa, sai a rataya ta a wuyan dabba, wai mayu ba za
su kama rakumin ba. Sai
Annabi (SAW) ya tura a cire dukkan wata igiya ta tsarkiya daga wuyan raƙuman
sahabbai. Wannan yana nuna cewa shugaba a cikin al’umma, dole ne ya kula da
addininsu, da ya ga wata ɓarna, sai ya hana da hannunsa. Wannan hadisin sai ya
wakilci hadisin Huzaifa da malam ya kawo a babin baya da muka ce mai rauni ne.
Ga shi Annabi (SAW) ya ce a yanke duk wani abu da yake na shirka kamar yadda
Huzaifa ya tsinke zare a hannun wani.
**********************
An karɓo daga Abdullahi
ibn Mas’ud (RA) ya ce, Na ji Manzon
Allah (SAW) yana cewa,
“Lallai tofi ko karatun ruƙya da rataya laya da maganin soyayya (bi-ta-zaizai)
shirka ne” Imam Ahmad [J1/381) da Abu Dawud [#3883] ne suka ruwaito.
________________
SHARHI
Wannan hadisin
ingantacce ne. Lafazin da ke cikin Abu Dawud [#3883] yana da tsawo, ga yadda
lafazin yake: An karɓo daga Zainab matar Abdullahi ibn Mas’ud ta ce, “Abdullahi
ya gan ni na rataya ulu ko zare a wuya.” Sai ya ce, “Wannan zaren fa?” Sai na
ce, “Wani zare ne na je aka yi min tofi a cikinsa.” Sai Abdullahi ya kwace, ya
tsinka shi, ya ce, Ku iyalan gidan Abdullahi kun wadata da yin shirka” Ya ce, “Na
ji
Manzon Allah (SAW) yana
cewa, “Roƙya, rataya layu da tiwala shirka ne.” (Zainab) ta ce, sai na ce da
shi “Da can idona yana cutar da ni, ina tafiya wurin wani, wane (sai ta ambaci
wani mutum bayahude) idan na je ya yi mini tofi a ido, sai ya daina raɗaɗi.”
Sai Abdullahi ya ce, “Wannan abin da kika gani aikin shaidan ne, shi ne yake
zuwa ya tsokane idonki, sai ki rinƙa jin ciwo yana raɗaɗi Idan kin je wurin
bayahuden, da ya yi tofi, sai shaidan din ya daina zungurar idon Idan an kwana
biyu sai ya sake yi, don ki koma Daga yanzu idan an ƙara tsokane miki, ya ishe
ki faɗin abin da Annabi (SAW) yake faɗa, “Izhabil ba’asa rabban-naas, washfi
antash-shaafi, laa shifaa’a illa shifaa’uka, shifaa’an laa yughaadiru suƙman.
Ma’ana, “Tafiyar da cuta, Uhangijin mutane, ka warkar domin kai ne mai
warkarwa, babu warkarwa sai taka Irin warkarwar da ba ta rage wata cuta. Wannan
shi se sababin zuwan wancan hadisin.
Ar-ruƙaa; Idan an ce ruƙaa
jam’i ne na ruƙya Shi ne tofi ko addu’a. Addu’ar da za a karanta a tofa, da
wadda za a kananta ba tare da an tafa ba, duk ana kiransu da ruƙya Asalin ruƙya
kasha uku ce;
a. Kashin Farko: Ta
zamanto addu’a ce ta Ƙur’ani ko hadisin Annabi(SAW) ingantacce ta hallata a
shari’a. Domin yin ta mustahabbs ne.
b. Kashi na Biyu: A ba
ka wasu addu’o’i waɗanda ba ayoyin Alƙur’ani ba, za ka ji ana kiran sunan wani
aljani ko ana kiran wani shehi. To wannan ya zama shirka ko sunan mala’ika ko
annabi aka kira shirka ne.
c. Kashi na Uku Ita ce
ruƙyar da za a ba ka wani abu mara ma’ana, wanda ba ka san kansa ba, ba Ƙur’ani
ba ne, ba Larabci ba ne, ba kuma Hausa ba ne. wannna shari’a ba ta yarda da shi
ba. Kuma ba za ka iya cewa shirka ne da gaggawa ba. Don haka, hukuncin wannan shi
ne kabira ce daga cikin kaba’ir, domin duk wanda ya yi wannan, ya yi shirme Kamar
yadda ya zo a cikin baitocin waka
lta
ruƙya idan an yi ta da tataccen wahayi biyu,
Wannan
yana cikin shari’ar Annabi
Kuma
babu sabani cikin kirawo abin sunnah,
Amma
duk ruƙyar da ba ka san ma’anarta ba,
Wannan
duk wasiwasinka kake.
Don haka, wani sahabi
ya zo wurin Manzon Allah (SAW) ya ce da shi “A lokacin jahiliyya mukan yi ruƙya.
Shin ya halatta yanzu mu riƙa yi?” Sai Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ku kawo min
in ji irin addu’o’in da kuke yi. Ita dai ruƙya babu laifi in dai babu shirka a
ciki, a je a yi.”(Muslim #2200)
At-tama’im: ‘tama’im’ shi
ne duk abin da za a rataya shi don kare cuta.
Malamai suna kasa ta
kashi 3:
a.
Kashi na Farko: Ita ce wadda aka yi ta
da waɗansu addu’o’i da ake kiran sunan aljanu. Kamar yadda ake cewa, “Ya
damdama-ya’ilu’, da sauransu. Wannan shirka ce ƙarara.
b. Kashi na Biyu: A ba
ka laya wadda aka rubuta wani abin da ba shi da ma’ana. Kamar misali, a yi
hatimi mai gidan dara, a sa
lambobin Larabei da
haruffan Larabei, wanda ba shi da ma’ana ko ta kwabo. Don haka, haramun ne
amfani da irin wannan layar.
c. Kashi na Uku: Layar
da aka yi ta da Aluƙr’ani da hadisi, su kaaɗai aka rubuta. Malamai sun yi
maganganu a kan irin wannan layar tun lokacin sahabbai. Wasu suka ce ta
hallata, wasu suka ce ba ta halatta ba. Amma zance mafi inganci, ba ta halatta
ba. Duk fatawoyin da sahabban da suka gina ta a kan halacci, sun gina ta ne a
kan rashin dalili, bisa ga ijtihadinsu.
At-tiwala: Shi ne
dukkan wani mataki na sihiri da mace za ta yi don ta ja hankalin mijinta, ko
miji ya yi don ya ja hankalin matarsa. A irin wannan, za ka ga mata suna amfani
da matakai iri-iri; wani lokacin su yi amfani da gashin kai, ko wani abin
amfaninsa, wani lokaci abin yana fin haka muni, sukan yi amfani da jinin haila,
ko ruwan tsarki da makamantansu. Wannan duk aiki ne na bokaye.
********************
An karɓo daga Abdullahi
ibn Ukaim, daga Annabi (SAW) ya ce,
“Duk wanda ya rataya
wani abu, to an jingina shi gare shi. Ahmed J4/310 da Timizi #2072]
‘At-Tama’im’
wani abu ne da ake rataya wa yara, galibi waɗanda suke rataya musu, suna kare su
ne daga baki, ko kambun baka. Sai dai abin da za a rataya ɗin nan, idan ya
kasance Alƙur’ani ne, wasu daga cikin mngabata sun yi rangwame cewa a iya
ratayawa.
Sashensu kuna ba su
amince ba. Saboda suna saka wannan cikin
ahubuwan de Annabi ya
hana. Daga cikinsu akwai Abdullahi ibn Mas’ud (RA).
________________________
SHARHI
Laya kashi uku ce ita
ma:
a.Wadda ako rubuta da
sunan aljanu, wannan shirka ce ƙarara,
b.Wadda aka yi da abin
da ba a sani ba, kamar a yi zanen gidan dara. To wannan ma shirk ace.
c.Wadda aka yi da Ƙur’ani,
to wannan sahabbai ma sun yi saɓani.
Ƙa’ida idan sahabbai ko
tabi’ai ko tabi’ut-tabi’una suka yi ijima’i a kan mas’ala, to ya zama wajibi a
bi su a kan mas’alar domin Annabi (SAW) ya ce, “Al’ummata ba za su yi ijima’i a
kan ɓata ba.” [Ibn Majah #3950]
Amma idan suka yi sa ɓani,
sahabbai da sahabbai ko tabi’ai da tabi’ai, to sai a baje maganganun na kowane
sahabi a ga wanne ne ya fi kusa da Ƙur’ani ko hadisi Wanda duk zancensa ya fi ƙarfin
hujja, to nasa za a rinjayar. Kuskure ne a ce duk wanda ka bi ka yi daidai don
sahabbai ne, ko a zabi wanda ya fi sauƙi a bar mai wahala, musammam idan saɓanin
mai karo da juna ne. Misali, ɗaya ya ce haram ne, ɗaya ya ce halal. Ba yadda za
a ce dukkansu daidai ne, ko a ce dukkansu kuskure ne, dole ɗaya daidai ne, ɗaya
kuskure. Mutum ba zai ce, “Tun da dukkansu sahabbai ne, duk wanda na ɗauka
daidai ne ba.” Kuma ƙarin kuskuren shi ne mutum ya ce Annabi ya ce “Saɓanin
al’ummata rahama ne.” [Duba Ad-dha’ifa #57] Wannan ba hadisi ba ne daga Manzon
Allah (SAW). Ba yadda za a yi saɓani ya zama rahama, kamar yadda Abdullahi ibn
Mas’ud ya ce a hadisin Bukhari [Abu Dawud #1960], “Saɓani sharri ne.” Ba yadda
za a
yi saɓani ya zama
rahama tun da sharri ne. Haka kuma ayoyin Ƙur’ani suka nuna illar saɓani da
kuma wajabcin haɗin kai. Don haka nassoshin da muka karanta a baya sun nuna
maganar Ibn Mas’ud ta fi karfi, saboda faɗar Annabi, “Wanda ya rataya laya ya
yi shirka.”
*******************************
Ita ‘Rukya’ ita ce ake
kira tofi ko addu’o’i. Sai dai nassi na
Shari’a ya nuna mana in
dai babu shirka a ciki, a iya yi. Annabi ya ba da dama ko rangwame cewa a iyn
yin ruƙya, don saboda kambun baka ko cizon wani abu mai dafi.
SHARHI
Ruƙya
(wato tofi) kala uku ne:
a. Ta shari’a kumar
Suuratul Fantiha, ƙarshen Suuratul Baƙara, Ayatul Kursiyu ko addu’o’in da
Annubi (SAW) ya koyar a ingantattun hadisai. Wannan ya halatta.
b. Karanta wa mutum
sunan aljanu don magance wani abu. Wannan shirka ce.
c. Sai kuma mutum ya karanta
abin da ba shi da ma’ana, ko babu wanda ya san menene. Wannan ma haramun ne.
*********************************
Amma lafazin ‘At-Tiwala’ wani abu ne da mutane suke yi
su
riya cewa wannan abu
yana sa Wa mace ƙauna a wajen mijinta
ko namiji a wurin
matarsa.
_________________________________
SHARHI
Wannan shi ne kamar
yadda a yau mata suke yin asiri don su mallake mijinsu, sai ya zama sai abin da
suka ce a yi za a yi a gida. Ko kuma wanda maza suke don su sa mace ta so su,
su aure ta ko su yi fasiƙanci da ita. Duk wannan ana amfani da kwalli ko gashi
ko wani abun tsubbu da boka zai bayar. Duk waɗannan shirka ne.
**********************************
Imam Ahmad (J4/108] ya
ruwaito hadisi daga Ruwaifi’ ya ce
Manzon Allah (SAW) ya
ce, “Ya kai Ruwaifi’! Me yiwuwa rayuwa za ta yi tsawo gare ka (bayan na bar
duniya) don haka, ka labarta wa mutane cewa, lallai duk wanda ya tufke gemunsa
ko ya rataya tsirkiya (da nufin kawo amfani ko kare sharri) ko ya yi tsarki da
kashin dabba ko da ƙashi cewa, Muhammad ya barranta da shi (wato ba Annabi, ba
shi).”
__________________________
SHARHI
Ruwaifi sahabi ne na Annabi (SAW).
Tufke gemu: Malamai suka ce, shin yaya
tufke gemu yake? Shi ne suka ce, Larabawan jahiliyya idan mutum ya cika, ya
batse, sai ya tufka gemunsa, ya yi kamar igiya, wato ya kitsa shi. Waɗansu suka
ce, ba wannan ba ne! Abin da ya sa suke yi, wai don gashinsu ya yi laushi ya mike,
kamar gashin kan mata. To wannan birgewa ne a wajensu. Kowane ɗaya daga cikinsu,
Annabi ya barranta da shi. Waɗansu malaman suka ce, ba sa yin kitson, sai idan
za su yi yaki.
Rataya tsarkiya: Wannan
ya gabata cewa zaren da ake yin amfani da shi wajen yin baka. Larabawa sukan yi
amfani da wannan zaren don maganin baki ko mayu. Kuma ƙudurta wannan shirka ne.
Domin jingina amfani ne ga abin da ba shi da amfani. Mai amfanarwa, da ba da
amfani kuwa, shi ne Allah.
Al-Istinja:
Tsarki na hoge. Asali akan yi shi ne da dutse. Idan
mutum yana jin bawali,
kuma bai samu ruwa ba, sai ya ɗauki hoge ya ajiye, idan ya yi fitsari, sai ya
kankare. Ana yi ne da dutse ko hoge, amma ba a yi da kashin dabbobi ko ƙashin
dabbobin. Wani hadisin daban, Annabi ya ce, “Idan kuka tashi yin tsarkin bawali
(istinja), kada ku yi da kashin dabbobi ko ƙashi. Domin wannan abincin ‘yan
uwanku ne cikin aljanu.”[Imam Nasaa’i Alkubra J1/72]
*******************************
An karbo daga Sa’id ibn
Jubair ya ce, “Wanda ya ga lnya a jikin
wani, sai ya je ya cire
ta, ya tsinke ta, kamar ya ‘yantar da bawa ne.” Waki’ ne ya ruwaito [Duba
Almusannaf na Ibmu Abi Shaibah #3524]
______________________
SHARHI
Wannan ruwaya da a ce sahabi ne ya faɗa, duk
da cewa bai danganta ta da Annabi ba, sai a ce yana cikin hadisi marfu’i. Tun
da akwai lokacin da maganar sahabi za a ɗauke ta tamkar Annabi ne ya faɗa, duk
da sahabi bai faɗi sunan Annabi ba. Idan ya zama abin da sahabin ya faɗa, abin da
hankali ba zai iya hararo shi ba, sai da nassi ƙarara, kuma ijtihadi ko istinbaɗi
ba zai iya kalato maka ba, sai nassi daga bakin Annabi (SAW), to
idan sahabi ya faɗi wannan,
ko da bai ce Annabi ya faɗa ba, ana ɗaukarsa a matsayin faɗin Annabi. Kamar
wannan, wato a ce wanda ya yi kaza hukuncinsa kaza. An sani cewa ijtihadi ba ya
shiga cikin wannan, dole sai da nassin hadisi ƙarara in da sahabi ne ya faɗa,
sai ya zama marfu’i. Sai dai kash! Tabi’i ne ya faɗa, don haka, ana kirga shi a
cikin hadisi Mursal, shi kuma yana cikin hadisi mai rauni. Amma wanda ya tsinke
laya ya
jefar, wannan zai dace
da ladan kore mummuna. Sai dai shin za mu ce yana da ladan wanda ya ‘yanta
bawa? Sai mu ce, a’a! Tun da hadisin day a ce haka mai rauni ne. Za mu ce yana
da lada ko da kuwa bai kai na wanda ya ‘yanta bawa ba. Idan mutum ya samu damar
tsinke laya a jikin wani, ba tare da an tayar da zaune-tsaye ba, don ko da
wanne lokaci fiƙihun ‘kore mummuna’ ka lura cewa idan ka canza wannan munkarin,
wani wanda ya fi shi
girma ba zai faru ba, to wannan sai ka yi, amma idan ba haka ba, sai ka kyale.
*********************************
Haka, (Imam Waki’) ya ruwaito
daga Ibralhim ya ce, “sun kasance suna ƙin layu gabaɗayansu, waɗanda aka yi da
Alƙur’ani da waɗanda ba na Alƙur’ani ba.” [Duba Almusannaf na Ibnu Abi Shaibah
#3518]
_____________________________
SHARHI
Ibrahim ibn Yazid
Annakha’i al-Kufiy, ana yi masa alkunya Abu Imran yana cikin manyan malaman fiƙihu
da hadisi, ya mutu a shekara ta 96 bayan hijira, yana cikin tabi’ai.
Su waye suke kin layu
gabaɗayansu? Sahabbai ko tabi’ai? Duk
lokacin da Ibrahim
Annakha’i ya ce, “Sun kasance” to da almajiran Abdullahi ibn Mas’ud yake. Ba
yana nufin tabi’ai gabaɗayansu ba, sai ɗaliban da suka yi karatu tare da shi a
wurin Abdullahi ibn Mas’ud. Wato dai, sun sami fatawa daga malaminsu, Abdullahi
ibn Mas’ud cewa ba za a ɗaura laya ba kowace iri ce. Wanda wannan yana daga
cikin dalilan da ya sa ake rinjayar da maganarsa a kan ta su Aisha (RA). Saboda
Abdullahi ibn Mas’ud yana cikin fuƙaha’us-sahaba.
****************************
A Cikin Wannan Babi
Akwai Mas’aloli Kamar Haka:
1. Fassarar ma’anar
kalmar ‘ruƙa’ da ‘tana’ im’.
2 Fassarar ma’anar
kalmar ‘at-tiwala.
3. Abubuwan nan guda
uku suna cikin shirka, kuma babu wata
togaciya (a kan wanda
ba ta Alƙur’ani ko hadisi ba),
4. Dukkan ruƙya, tofi
ko karanta wa mutum wani abu na
Alƙur’ani, in dai an yi
shi da magana ta gaskiya (don saboda kambun baka ko saboda cizon wani abu mai
dafi) ba ya cikin
shirka.
5. Layar da aka yi ta
da Alƙur’ani, malamai sun yi saɓani shin
tana daga cikin shirka
ko a’a?
6. Rataya tsirkiya a
wuyan dabba, shi ma yana daga yin shirka.
7. Tsananin narko da
aka yi a kan wanda ya rataya tsirkiya.
8. Falalar lada ga
wanda ya tsinke laya daga wuyan wani.
9. Maganar Ibrahim
al-Nakha’i ba ta cin karo da sabanin da
malamai suka yi a kan
hukuncin laya. Saboda abin da yake
nufi da maganarsa
daliban Abdullahi ibn Mas’ud.
(FASSARA DA SHARHI DA
GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba Insha Allah)
Alhamdu lillah
ReplyDelete