Yana
Daga Cikin Dangin Shirka Sanya Wani Zobe Ko Zare
Da
Makamancinsu Domin Kare
Bala'i Ko Magance Shi
SHARHI
__________________________
Wannan babi gabaɗaya,
fahimtarsa yana dogara ne da fahimtar alaƙar da
ke tsakanin sababi (al-sabab) da wanda yake kawo sababin (almusabbib).
Sababi shi ne dukkan wani abin da Ubangiji ya sanya shi, ko ya
shar'anta shi, ko ya ƙaddara ana iya amfani da shi don
magance kaza. Wanda kuwa yake kawo sababin
(Al-musabbib) shi ne Allah din. A shari'ance,
shari'a ta yi izini ka yi amfani da shi don magance cuta iri kaza,
Ba duka kowane irin magani za ka yi amfani da shi ba, sai wanda shari'a
ta ba ka dama. Ba a ɗaukar wani abu a matsayin sababi na
warkewa daga cuta, sai an yi la'akari da abu uku:
warkewa daga cuta, sai an yi la'akari da abu uku:
a. Ba ka cewa abu kaza sababi ne na magance cuta,
sai idan ya tabbata a shari'ance da ƙaddare (wato
an jarraba shi, ba sau ɗaya ba, yana magance
cutar) kamar zuma. An jarraba zuma a ƙaddare
tana maganin ciwon ciki, sannan Ubangiji ya ba da izini a
shar'ance, kuma Annabi ya faɗa a hadisi tana
maganin ciwon ciki, aka jarraba, aka gani. Ɗaukar zuma
na magance ciwon ciki, ya samu sharadi na cewa ta zama sababi a ƙaddare
kuma a shari'ance.
b. Duk abin da aka sa ya zama sababi na
warkuwar cuta, to kada ka dogara
a kansa shi kaɗai, Kai dai ka yi amfani da shi don Allah
(SWA)
ya yi izini,
amma zuciyarka ta ƙudurce cewa mai warkarwar
na haƙiƙi,
shi ne Allah
(SWA).
Idan ya ga dama sai ya zare warkarwar daga maganin, ya sa a wani
maganin daban.
c. Ka ƙudurce a zuciyarka duk yadda maganin ya
kai ga warkarwa ko amfáni, ba ya yin
tasiri sai idan Allah ya yarda ya yi. Waɗannan
sharuɗɗai
guda uku (3),
su ne ake nema wajen riƙon dukkan
wani abu ya zama sababi. Waɗannan abubuwa da aka ambata
a babi, wato zobe ko wane iri ne, zare, dodon koɗi ko wuri ko
ƙaho,
hauren giwa da idon mujiya, dukkan waɗannan
Ubangiji bai sanya su zama sababi ba, jarrabawa ba ta nuna
suna maganin wata cuta ba, kuma shari'a ba ta yi izini na riƙon
su don
magance wata cuta ba. Saboda haka, duk wanda ya riƙi ɗaya daga cikinsu
don magance cuta, to ya yi shirka a ɓangaren Rububiyyah.
Idan kuma ya
ɗauka a
zuciyarsa mai ɗauke cutar shi ne Allah, amma ya
riƙi ɗaya
daga cikinsu a matsayin sababi, to hukuncinsa ya yi wa Allah ƙarya. Domin
ya riƙi sababi
da abin
da Allah bai sanya shi ya zama sababi ba.
Allah (SWA) bai sanya idon mujiya ya zama
maganin ɓarawo
a gida ba; Allah bai sanya zobe ya zama maganin baki
ko kambun-baka
ba; Allah bai sanya wuri ko dodon koɗi ya zama maganin mayu
ba, bai sanya haka ba a shari'ance, kuma bai sanya
haka ba a ƙaddare. Don haka, kana jingina
abin da Allah bai sanya shi ya zama sababi ba.
***************
Da fadin Allah;
"Ku ba ni labarin abin da kuke bautawa ba
Allah ba, idan Allah ya nufe ni da cuta, (shin waɗannan
allolin) za su iya yaye min cutar? Ko
kuma in Allah ya nuface ni da wata rahama, shin za su iya kame rahamarsa?
Ka ce da su, "Allah ya ishe ni, a gare shi ne kaɗai
masu dogaro
suke dogara." (Az-Zumar: 38)
__________________________
SHARHI
Dangantakar ayar da matashiyar maganar, shi ne don a
nuna cewa waɗannan ababen ba sa iya ɗauke cuta, kuma ba sa
iya kawo amfani. Don haka, wannan
ya nuna cewa, babu mai ɗauke cuta ko kawo amfani, sai Allah
(SWA).
Don haka ka sa zobe ko zare ko idon mujiya ko ƙaho,
ka ce maganin
mayu ko ɓarawo
duk wannan shirka ne.
*****************
An karbo hadisi daga Imran bin Husain (RA)
ya ce, "Manzon
Allah (ﷺ) ya ga wani mutum, a
hannunsa akwai zobe na tagulla, sai ya
ce da shi, "Menene nake gani?" Sai ya ce, "Na sa wannan ne, saboda
ciwon hannu (al-wahina)." Sai Annabi ya ce, "Cire wannan zoben!
Babu abin da
zai kara maka sai cuta da rauni. Da a ce za ka mutu
da wannan zoben a hannunka, ba za ka rabauta ba har abada. Ahmad
ne ya ruwaito da sanadin da babu laifi a cikinsa. [Al-Musnad J4/445]
____________
SHARHI
Imran bin Husain ibn Ubaid ibn Khalaf Al-Khuza'iy
(Abu Nujaid, sahabi ne, haka babansa ma). Wannan hadisin ibn
Hibban [Sahihu Ibn Hibban 7/628], da Al
Hakim al-Naisaburiy [Al-Mustadarak na Hakim J4/216]
da Ibn Majah [#3531] sun ruwaito shi. Sai dai hadisin mai rauni ne.
Saboda haka, saƙon da wannan hadisi yake bayarwa, ayar
ta wadatar. Annabi yana nuna wannan zoben ba ya amfani, inda
hadisin ya inganta.
****************
Akwai hadisin da aka karɓo daga Musnad na Imam
Ahmad
[Musnad J4/154], an karɓo daga Ukbah bin Amir
(RA),
hadisi ne Marfu'i daga Annabi (RA),
"Duk wanda ya rataya laya, kada Allah ya cika
masa manufarsa, wanda kuma ya rataya wuri, kada Allah ya kwantar
masa da hankalinsa."
___________________________
SHARHI
Wannan shi ma hadisin mai rauni
ne. [Duba Ad-dha'ifa ta Albani #
1029]
***************
A wata ruwayar hadisin daban na
Imam Ahmad,"Wanda duk ya rataya laya, haƙiƙi
ya yi shirka."
________________________
SHARHI
Sai dai wannan ruwayar banda Imam Ahmad [Al-Musnad
J4/154], haka
Imam Hakim al-Naisaburiy [Al-Mustadarak J4/417] ya ruwaito, kuma
wannan sahihiya ce. Sheikh Nasiruddeen Albani ya inganta ta a cikin
Silsilatul-Ahadisus-Sahiha', shi ne hadisi na 492.
"Wanda ya rataya laya!" Me ake nufi da
haka? Ba ana nufin wanda ya rataya ba, ko da
mutum nufi ya yi a zuciyarsa cewa laya na da amfani ko
da babu a jikinsa, ya yi shirka. Misali ka ga mutum ya sa a motarsa ko a
kofar gidansa ko a jikin dabbarsa ko jaririnsa, duk wannan ya rataya kenan.
***************
Ibn Abi Hatim ya ruwaito cewa Huzaifa, ya ga wani
mutum
ya rataya wani zare ko ulu, saboda masassara da take
damun sa, sai Huzaifa ya yanke zaren, sai ya karanto fadin Allah;
Duba Tafsirin Ibn Kathir ƙarƙashin ayar [Yusuf:106]
"Mafi yawancinsu ba sa yin imani da Allah face
suna masu yin shirka” (Yusuf:106)
Huzaifa ibn Yaman (shi Yaman sunansa Husayl al-Abatiy
Haliful Ansar)
sahabi ne mai falala, shi Huzaifa ana kiransa Sahib Sirri Rasulillah'.
Wannan ruwaya ta ibn Abi Hatim, ta zo a cikin littafin Annahajus-Sadid,
cewa ruwaya ce da take bukatar bincike. Ma'ana dai ba ta
inganta ba. A cikin dukkan nassoshin da Sheikh Muhammad ibn
Abdulwahab ya kawo a cikin wannan babi, nassi biyu
ne suka inganta: Nassin Ƙur'ani da nassin man ta
'allaka tamimatan, ya inganta. Wannan su ne hujja da ya ƙulla
babin a kai.
A
Cikin Wannan Babi Akwai Mas'aloli Kamar Haka:
1. Kausasa harshe dangane da rataya zobe da nufin ɗauke
cuta
ko hana ta zuwa; ko rataya zare da wannan manufa da makamantansu.
2. An nuna cewa da sahabi zai mutu, wannan abu
yana
hannunsa, ba zai rabauta ba, A nan
akwai ƙarfafa
maganar
sahabbai da suke cewa ƙaramar shirka ta fi
manyan zunubai
(kaba'ira) girma.
3. Ba a ba shi uzuri ba kan jahiltar mas'alar.
4. Dukkan dangogin abin da aka faɗa,
ba sa amfani a nan
gidan duniya, sai ma cutarwa da suke, saboda
faɗinsa,
"Ba
za su kara maka komai ba sai dai rauni."
5. Halaccin kausasar harshe wajen inkari ga wanda ya
aikata
haka (wato ya rataya wani abu don neman tsari).
6. Bayyana cewa duk wanda ya rataya wani abu, to an
jingina
shi ga wannan abin.
7. Bayani cewa, duk wanda ya rataya laya to haƙiƙi
ya yi
shirka.
8. Mutum ya rataya wani zare a jikinsa don ya kare
shi daga
cutar masassara, shi ma wannan yana daga cikin
shirka.
9. Karanta waccan ayar da Huzaifa ya yi, dalili ne
da yake
nuna sahabbai suna kawo ayar da take magana a kan
shirka
babba don su kafa hujja da ita wajen
haramcin ƙaramar shirka.
Kamar yadda ibn Abbas ya ambata a cikin ayar Suuratul
Bakara.
10. Mutum ya rataya wuri a wuya wai don saboda
kambun
baka ko maganin baki, shi ma yana daga cikin shirka
yin
hakan.
11. Yin mummunar addu'a ga wanda ya sanya laya; cewa,
kada Allah ya cika masa burinsa, kuma yin addu'a ga
wanda ya rataya wuri; cewa kada Allah ya kwantar
masa da
ransa. Ma'ana kada Allah ya kyale shi.
"Duk
wanda ya rataya sunan aljanu, ko ya kira wasu ba Allah ba su kare masa
masifa ko su jawo masa amfani, to haƙiƙi ya yi babbar shirka. Don ya
rataya zuciyarsa ga wanin Allah ya yi masa aikin Allah.”
(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR
MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba Insha
Allah)
No comments:
Post a Comment