GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Tuesday, November 15, 2011

ARBA'UNA HAADITH (32) HADISI NA TALATIN DA BIYU


An karɓo daga Abu Sa'id, Sa'ad ɗan Malik ɗan Sinan Al-Khudriy (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Ba cuta, babu cutarwa." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2341) da Daraƙuzuni (#228) da waninsu Musnadan. Haka Imamu Malik ya rawaito shi a cikin Muwaɗɗa (J2/sh 746) daga Amru ɗan Yahya daga babansa daga Annabi (ﷺ) Mursalan, bai ambaci Abu Sa'id ba. Amma hadisin yana da hanyoyin da sashinsu yana ƙarfafa sashi.

ARBA'UNA HAADITH (31) HADISI NA TALATIN DA DAYA


An karɓo daga Abu Abbas, Sahlu ɗan Sa'ad Assa'idi (R.A) ya ce, "Wani mutum ya zo wajen Annabi (ﷺ) ya ce da shi "Ya Manzon Allah! Nuna min aikin da idan na aikata shi, Allah zai ƙaunace ni, mutane ma za su ƙaunace ni." Sai (Annabi ﷺ) ya ce, "Ka yi zuhudu cikin lamarin duniya, sai Allah ya ƙaunace ka, kuma ka nisanci abin da ke hannun mutane, sai mutane su ƙaunace ka." Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#4102) da waninsa ta hanyoyi masu kyau.

Tuesday, November 8, 2011

ARBA'UNA HAADITH (30) HADISI NA TALATIN

An karɓo daga Abu Sa'alaba shi ne Jursumu ɗan Nashib (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Lallai Allah Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su, ya sanya iyakoki, kar ku ƙetare su, ya haramta wasu abubuwa, kada ku keta alfarmarsu, ya yi shiru game da waɗansu al’amura don jinƙan ku, ba don mantuwa ba, kar ku bincike su. Daraƙuɗuni ne ya rawaito shi a cikin littafinsa Sunan (J 4 sh 184) da waninsa.

SHARHI
Faɗin Manzon Allah (ﷺ) cewa, "....Allah Ta'ala ya farlanta farillai, kar ku tozarta su...." yana nufin lallai ku tsayar da wannan farillan yadda Allah ya ɗora muku su

ARBA'UNA HAADITH (29) HADISI NA ASHIRIN DA TARA

An karɓo daga Mu'azu ɗan Jabal (R.A) ya ce, "Na ce, Ya Manzon Allah! Ba ni labarin wani aiki da zai shigar da ni aljanna, ya kuma nisantar da ni daga wuta.“ Sai ya ce, "Haƙiƙa ka yi tambaya game da abin da yake mai girma, sai dai abu ne mai sauƙi ga wanda Allah ya sauƙaƙe shi gare shi. Ka bauta wa Allah, ba tare da ka haɗa shi da wani ba, kuma ka tsayar da sallah, kuma ka ba da zakka, kuma ka azumci Ramadan, sannan ka ziyarci ɗakin Allah." Sannan sai (Annabi ﷺ) ya ce, "Shin ba zan shiryar da kai ƙofofin alheri ba? Azumi garkuwa ne, sadaƙa kuma tana shafe kurakurai, kamar yadda ruwa yake kashe wuta, haka sallar mutum a cikin yankin dare. Sannan ya karanta (faɗin Allah), "...gefen jikinsu yana nisantar gurin kwanciyarsu. . . " har ya kai inda (Allah yake cewa ’Ya'amaluun' sannan sai Annabi ﷺ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin kan al'amarin ba, da ginshikinsa da ƙololuwar Samansa?" Sai na ce "Eh!" sai ya ce, "Kan al'amarin (shi ne) musulunci, ginshiƙinsa kuwa salla, ƙololuwar samansa kuwa jihadi." (Sai Annabi  ﷺ) ya ce, "Ba zan ba ka labarin abin da yake mallakar kusan gaba ɗaya ba?" sai na ce "Ba ni labari." sai ya kama harshensa ya ce, "Ka riƙe wannan." Sai na ce, "Shin yanzu za a kama mu da maganar da muka yi?" sai (Annabi ﷺ) ya ce, "Da ma mahaifiyarka ta rasa ka! Akwai abin da yake jefa mutane wuta a kan fuskokinsu (ko ya ce) kan hancinsu, sai sakamakon abin da harshensu ya faɗa." Tirmizi (#2616) ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.

ARBA'UNA HAADITH (28) HADISI NA ASHIRIN DA TAKWAS

An karɓo daga Abu Najih, shi ne Irbadu ɗan Sariya (RA) ya ce, "Manzon Allah (ﷺ) ya yi mana wa'azi, wa'azi mai isarwa, zukata suka tsorata, ldanu suka zubar da hawaye. Sai muka ce da shi, "Ya Manzon Allah (ﷺ)! Kamar wa'azin mai ban kwana? To ka yi mana wasici." Sai ya ce, "Ina muku wasici da jin tsoron Allah, da kuma ji da bi, ko da bawa ne ya zama shugaba a gare ku. Lallai wanda ya rayu a cikinku, da sannu zai ga saɓani mai yawa. Na umarce ku, ku riƙe sunnata, da sunnonin halifofi shiryayyu, ku riƙe ta da hakoranku (fiƙa), ku kiyayi fararrun al'amura, domin kowace bidi'a ɓata ce. Abu Dawud (#4607) da Tirmizi (#2676) suka rawaito shi, Tirmizi ya ce, wannan hadisi ne mai kyau, ingantacce."

ARBA'UNA HAADITH (27) HADISI NA ASHIRIN DA BAKWAI

An karɓo daga Nawas ɗan Sam'an (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Aikin ɗa'a shi ne kyawawan dabi'u, laifi shi ne abin da ya yi kai kawo a zuciyarka, kuma ba ka so mutane su ga kana yin wannan abin." Muslim (#2553) ya rawaito.

An karɓo daga Wabisa (R.A) ya ce, "Na zo wurin Annabi (ﷺ), sai ya ce, "Ka zo ne kana tambaya dangane da ɗa'a?" Sai na ce, "Na‘am!" Sai ya ce, "Ka yi wa zuciyarka fatawa,

ARBA'UNA HAADITH (26) HADISI NA ASHIRIN DA SHIDA


An karɓo daga Abu Hurairata (R.A) ya ce, "Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Dukkan gaɓɓai na mutane akwai sadaƙa a ciki, kowanne yini da rana ke hudowa cikinsa, da za ka sasanta tsakanin mutane biyu, da ke rigima da juna sadaƙa ne, ka taimaki mutum game da dabbarsa, ka ɗora shi a kai, ko ka ɗauki kayansa ka ɗora masa a kan dabbar, sadaƙa ne; kalma daddaɗa sadaƙa ce; dukkan taku da za ka yi tattaki zuwa sallah, sadaƙa ne; ɗauke wani abu mai cutarwa daga kan hanya sadaƙa ne." Bukhari (#2989) da Muslim (#1009) suka rawaito shi!”

FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHAMUD ADAM (R)

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...