GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Tuesday, April 21, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BAKWAI 7)



Yana Daga Cikin Dangin Shirka Sanya Wani Zobe Ko Zare
Da Makamancinsu Domin Kare Bala'i Ko Magance Shi
SHARHI
__________________________


Wannan babi gabaɗaya, fahimtarsa yana dogara ne da fahimtar alaƙar da ke tsakanin sababi (al-sabab) da wanda yake kawo sababin (almusabbib). Sababi shi ne dukkan wani abin da Ubangiji ya sanya shi, ko ya shar'anta shi, ko ya ƙaddara ana iya amfani da shi don magance kaza. Wanda kuwa yake kawo sababin (Al-musabbib) shi ne Allah din. A shari'ance, shari'a ta yi izini ka yi amfani da shi don magance cuta iri kaza, Ba duka kowane irin magani za ka yi amfani da shi ba, sai wanda shari'a ta ba ka dama. Ba a ɗaukar wani abu a matsayin sababi na 

Monday, April 20, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA SHIDA 6)


Fassarar Tauhidi Da Kuma Kalmar Shahada

Da faɗar Allah;
"Waɗancan Waɗanda (masu shirka) suke roƙon su, su da kansu suna neman kusanci i zuwa ga (Allah) Ubangijinsu, don haka wanene a cikinsu ya fi kusanci i zuwa saduwa da yardar Allah." (Al-Israa":57)

___________________________


SHARHI
Dangane da saukar wannan aya, Abdullah ibn Mas'ud (RA) yake cewa,
"Wata tawaga ce cikin mutane, sai suke bauta wa aljanu. Aljanu suna ba su umarni su bi don samun biyan buƙatunsu na duniya. Ana nan a haka lokaci mai tsawo, sai aljanun suka musulunta, kuma suka cigaba da ɓauta wa Allah. Su kuwa Waɗancan mutane, ba su farga ba, suka cigaba da bauta wa aljanun, su kuma aljanun suna bauta wa Allah. Shi ne Allah ya ce, "Ka ga Waɗancan Waɗanda mutane suke roƙon su, su neman abin da

Sunday, April 19, 2020

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYAR 5 )

Kira Zuwa Ga Shaidawa Babu Abin Bautawa Da Gaskiya Sai Allah
______________
Sharhi;
Wato idan muka lura jerin babukan littafinnan suna tafiya a tsari. Babin farko Malam ya yi bayani akan menene tauhidi, sannan ya kawo falalar Lauhidi da yadda yake kankare zunubi, sannan sai ya zo babin tsoron afkawa shirka, wanda yana daga kamalar tauhidi mutum ya dinga jin tsoron afkawa cikin shirka. To idan aka samu cikakken tauhidi da kuma cikkaken tsoron faɗawa cikin shirka, to ka zama kamili a karan kanka, saura kuma ka yi ƙoƙarin wane ma ya zama kamili. To shi ne malam ya kawo wannan babi na kira zuwa ga bautawa Allah shi kadai. Wato ka fahimtar da mutane saƙon da ka fahimta.
********************
Da faɗar Allah;
"Ka ce “Wannan ita ce turba ta (musulunci). Ina kira zuwa ga Allah,

Sunday, April 21, 2019

KITABUT-TAUHID (BABI NA HUƊU 4)


Jin Tsoron Afkawa Cikin Shirka
______________
Wannan babi zai yi magana a kan jin tsoron afkawa cikin shirka. Wato alamar imani ya kankama a jikin mutum shi ne kullum ya ji yana tsoron afkawa cikin shirka, mutum yana taka-tsantsan a magana ko aikin da yake shirka ne. Kar mutum ya amintu ya dinga jin cewa ya tsira ya hau tudun mun tsira daga afkawa cikin shirka.
********************
Da faɗin Allah;
“Haƙiƙa Allah ba ya gafarta wa haɗa shi da wani (shirka), yana gafarta wa abin da bai kai shirka ba, ga wanda ya so. (An-Nisaa:116)
________________
SHARHI;
Wannan aya ta maimaitu har sau biyu a Suuratul Nisaa’i. Menene shirka? Abin da ake nufi da shirka, shi ne kamanta abin halitta da mahalicci.

Wednesday, December 24, 2014

KITABUT-TAUHID (BABI NA UKU 3)


Duk Wanda Ya Tabbatar Da Tauhidi Zai Shiga Aljanna Ba Tare Da Hisabi Ba
_______________
SHARHI;
Wannan babin kamar cukon babin baya ne. Babin baya ya yi bayani akan falalar tauhidi da yadda yake kankare zunubai. Wannan kuma zai yi bayanin cewa, duk wanda ya tabbatar da tauhidi, haƙiƙanin tauhidi, to zai shiga aljanna ba tare da hisabi ba, wato babu ƙididdugar ayyuka, kuma babu azaba. Ana tashi ƙiyama,
sai a kai su aljanna. Allah Ya sanya mu acikinsu. Amin       
            Haƙiƙani tauhidi shi ne, tace shi daga dukkan datti da shirka, wato mutum bai yadda da malamin duba ba, bai yadda da boka ba, dukkan wani abun da yake haƙƙin Allah (SWA) ne ya tabbatar masa Shi kaɗai. Sannan kuma ya tace tauhidi daga dukkan wani dangi na bidi’a ta faɗa a baka, ko a aiki.

Saturday, March 1, 2014

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYU 2)

          Falalar Tauhidi Da Yadda Yake Kankare Zunubai
     Da fadin Allah;
 ”Waɗanda suka yi imani, ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, lallai su ne suke da amintuwa, kuma su ne shiryayyu.” (An'aam: 82)

_________________
SHARHI;
Wannan aya ta zo a daidai inda aka ba da ƙissar Annabi Ibrahim (AS) na muƙabala da ya yi da mutanensa da hana su bautar gumaka, sai ake tambaya cewa, da su mushirikan da Annabi Ibrahim waye a kan shiriya?
Sai Allah ya ba da amsa
a Wannan ayar.
    Idan an ce,

Monday, September 9, 2013

KITABUT-TAUHID (BABI NA ƊAYA 1)


                                       KITABUT-TAUHID
_____________  
SHARHI
Abin da tauhidi yake nufi shi ne kaɗaitawa, Wato daga Kalmar wahhada, Malam a nan ya na nufin Kitabut-tauhidillahi wato llttafin kaɗaita Allah. Kaɗaita Allah, kuma
ta ɓangarori ne guda uku.
  1) Rubuubiyya: Daga kalmar Rabb, wadda ma’anarta shl ne mai halitta da kuma kulawa da halitta ɗin. Tabbatarwa da Allah (SWA) ne kadai ya yi halittu gabaɗaya kuma yake kula da su, shi ne kaɗaita Allah da rububiyya.
  2) Uluuhiyya ko Al-Ilahiya: Daga kalmar A I-ilaallu wato alma ’abuudu wato abin bauta. Amma a shari’a ldan an ce alma’abuudu abin da ake nufi shi ne abin bautawa bautar ta gaske,
Don haka duk wanda aka bautawa ba Allah ba, to ba bautar gaske ba ce. Allah (SWA) kaɗai ake wa ta gaskiya. Shi ya sa kalmar shahada ta ƙunshi ɓangarori guda biyu: Bangare na farko, kwaɓe rigar ilahantaka ga kowa wato Iaa ilaaha. Sal kuma Bangare na biyu illallahu, wato sal Allah (ﷺ)  kaɗai.
 3) Kaɗaita Allah wajen sunayensa da siffofinsa. Dukkan suna ko siffa na Allah, nasa ne, wani ba ya tarayya da shi wajen sunan ko siffar.

********************
Da faɗin Allah Ta’ala;
"Kuma ban halicci aljanu da mutane ba, sai domin su bauta mini."  (Zaariyaa; 56)
__________________________
SHARHI
Malam da ya ce Kitabut-tauhid, sai ya fara da kawo ayoyi da hadisai. Wato ba ra’ayinsa ya kawo ba, zallar gaskiya ce.
        Kalmar ‘aljanu’ a ayar ta haɗa

FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHAMUD ADAM (R)

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...