GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Mar 1, 2014

KITABUT-TAUHID (BABI NA BIYU 2)

          Falalar Tauhidi Da Yadda Yake Kankare Zunubai
     Da fadin Allah;
 ”Waɗanda suka yi imani, ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, lallai su ne suke da amintuwa, kuma su ne shiryayyu.” (An'aam: 82)

_________________
SHARHI;
Wannan aya ta zo a daidai inda aka ba da ƙissar Annabi Ibrahim (AS) na muƙabala da ya yi da mutanensa da hana su bautar gumaka, sai ake tambaya cewa, da su mushirikan da Annabi Ibrahim waye a kan shiriya?
Sai Allah ya ba da amsa
a Wannan ayar.
    Idan an ce,
‘Az-zulmu’ ya kasu kashi biyu, babba da ƙarami.
a. Shirka, babban zalunci ne.
b. Karamin zalunci shi ne mutum ya zalunci kansa, ko ya ƙi yin sallah a kan lokaci ko ya ƙi bayar da zakka. Haka idan mumm ya Zubar da jinin Wani, ko ya ci rnutuncin wani, duk ana ƙirga su a
matsayin ƙararnin zalunci, domin bai kai shirka girma ba.
Shin zalunci ƙarami ake nufi a wannan ayar ko babba? Kamar yadda sahabbai suka tambayi Manzon Allah (ﷺ) , shirka ake nufi, amma ba ya hana ƙaramin zalunci ya shiga ciki. Malamai sun ce Wanda ya yi imani, bai garwaya shi da babban zalunci ba, amma ya gauwaya shi da
ƙaramin zalunci, to yana da imani daidai nasa, Kuma ana yi masa barazana da azaba, amma ba zai dawwama ba.
Bukhari [#3360] ya ruwaito a cikin kitab al-Anbiya, Abdullahi ibn Mas’ud yake ccwa, “Lokacin da wannan aya ta sauka, mu taron sahabbai muka ce da Annabi, “To ai babu mai tsira, domin wanene a cikinmu bai zalunci kansa ba?" Sai Annabi ya ce, “Kun tafi da nisa! Ba wannan zaluncin ake nufi ba, zaluncin da aka nufi shi ne zalunci na shirka. Ba ku ji fadin bawa nagari ba (Luƙman) inda ya ce; “Lallai shirka zalunci ne mai girma” (Luƙman 13)
Don haka, Allah (SWA) yake cewa.
 “Kafirai su ne azzalumai.”(Al-BaRara:254)”
Haka kuma Allah (SWA) ya ce:
“Kada ku bauta wa wanin Allah Wanda ba zai amfanar da kai ba, kuma ba zai cutar da kai ba, idan ka aikata haka, kana daga cikin azzalumai.” (Yunus: 106)
        Ma’ana dai, waɗanda suka yi imani, kuma ba su garwaya imaninsu da zalunci ba, lallai suna da amintuwa a gidan lahira ( ba sub a azaba) kuma sunansu shiryayyu a duniya. Haka mafiya yawan masu fassara suke fassarawa. Wasu kuma suna cewa amintattu a duniya da lahira kuma shiryayyu  a  duniya da lahira
   Duk da cewa, farkon abin da zai faɗa a cikin wannan aya shi ne babban zalunci ba ya hana faɗawar ƙararnin zalunci. Saboda me? Malamai suke cewa, duk Wanda ya yi imani, kuma bai garwaya imaninsa da babban zalunci da ƙaramin zalunci ba, yana da cikakkiyar shiriya. Kuma duk wanda bai garwaya imaninsa da babban zalunci ba, amma ƙaramin zalunci ya shiga, yana da aminci da shiriya dai-dai nasa. Domin mutumin da ya yi laifi, ana yi masa barazana da azaba, sai dai ba zai dawwama a cikin wuta ba, zai iya shiga ayi masa azaba.

********************
   Daga Ubadata ibn Al-Samit Al-Ansari (RA) ya ce, Manzon Allah (ﷺ)  ya ca “Wanda ya shaida cewa babu abin bautawa bisa ga cancanta, sai Allah, shi kaɗai yake, ba shi da abokin tarayya, kuma Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne, kuma Isa bawan Allah ne, kuma manzonsa ne, kuma kalmarsa ce da ya fuskantar da ita ga Maryam kuma Ruhine daga gate shi, kuma aljanna gaskiya ce,
kuma Wuta gaskiya cc, to Allah zai shigar da shi aljanna abisa abin da ya kasance na aiki. [Bukhari #3435 da Muslim #28]
_____________________
SHARHI;
Abin da ake nufi da ‘shaidawa,’ shi ne mutum ya san cikakkiyar ma’anarta yana mai aiki da  ma’anar bai warware ba. Shi ne ma’anar, “Man shahida” A ƙa’ida shahada ba ta cika sai da abu uku. Na farko,  Al-Ilmu (llimi); na biyu, Al-Yaƙin (sakankancewa); na uku, yin aiki da ma’anar. Shahada ba ta ɗaukar ma’anar furuci da baki kaɗai. Shahada ba ta cika sai idan ka san mai ka shaida, sannan gaɓɓanka suka yi aiki da abin da ka shaida, amma shaidar baki kaɗai ba ta sa ka zama mumini. Ma’anar kalmar shahada ta rabu kaso biyu:
   a. Korewa; kore ilahantaka ga wanin Allah.
   b. Tabbatarwa; tabbatar da dukkan ilahantaka ga Allah.
     Yawanci tauhidin da ake tabbatar wa mutane shi ne, ‘Tauhidur Rububiyyah,’ wanda irin su Abu jahil     ma sun yarda da shi. Masu ilmul kalam suna cewa, “Dole ka yi imani da ‘Wahdaniyyatul lahi.” Suna   nufin;
  a. Wahidun fi zatihi - shi kaɗai a zatinsa.
  b. Wahidun fi af’alihi - shi kaɗai cikin aikinsa.
  c. Wahidun fi sifatihi - shi kaɗai a sifofinsa, babu mai tarayya da shi
      a cikinsu.
Abu Jahil ma ya yarda da Wannan, babu ilahantaka a ciki, saboda ba su ce, ‘Wahidun fi Ilahiyyathii’ ba. Saboda haka, gabaɗaya babu manufar turo Annabawa a ciki, amma a wajen a bauta masa shi kaɗai  ne ba su yarda ba.
Shi ya sa aka ce bambancin masu shirkar da, da na yanzu shi ne, masu shirkar da suna yi ne a hali ɗaya, wato a halin yalwa, amma idan suna cikin tsanani, tauhidi gare su. Duk da haka aka ce raba ƙafar da suke
yi bai halatta ba, aka sa musu suna kafirai, kuma aka yaƙee su, aka halatta dukiyarsu, kuma aka maishe su bayi. Amrna masu shirkar yau, a cikin tsanani da yalwa suna kiran wanin Allah. Don haka, shahada ba ta tabbata sai mutum ya tara waɗannan sharuɗɗai uku.
   a. Ilimi: Ya san ma’anarta. Kamar yadda Allah ya ce,
.     “Ka sani, babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah........” (Muhammad: I9) '
   b. Sakankancewa da ma’anar, ‘Laa ilaaha illallahu’.
   c. Yin aiki da ma’anar. Kamar yadda Allah ya ce,   
     “Kuma waɗanda suka kira koma-bayan Allah, ba sa mallakar ceto, sai Wanda ya shaida da gaskiya alhalin suna sane da ma’anarta” (Azzukhruf : 86)
          Wahdahu (shi kaɗai)! Kalmar Wahdahu taukidi ne; kalmar ‘Laa sharika lahu’ shi ma taukidi ne. Ma’anar Wahdahu wato taukidi ne na ‘illallaahu’; kuma ‘Laa sharika lahu’ taukidi ne na ‘Laa ilaaha’. Saboda haka, ‘Wahdahu’ taukidi ne na tabbatarwa (ithbat), shi kuma ‘Laa sharika lahu ’taukidi ne na korewa (annafyu).
         Kuma ya shaida cewa Annabi Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa ne. Waɗannan  kalmomi guda biyu ‘Abdu’ da ‘Rasulu’, ƙarkashinsu ne ake mayar da martani ga masu sako-sako da masu wuce
gona-da-iri. Masu sako-sako su ne yahudawa, waɗanda suka saɓa wa Annabawansu (ma’abota son zuciya). Masu wuce gona da iri su ne nasara, saboda sun mayar da manzanni alloli. Kowanne daga cikinsu laifi ne! Don haka, sai aka ce ‘A bduhu’, don a tabbatar da Annabi yana nan a ma.tsayin bawa, bai kai matsayin ‘Ilaahu’ba, kurna aka ce ‘Rasulu ’, don a nuna fifikonsa a cikin mutane, don a nuna  jakada ne na Allah. Ma’ana babu Wanda ya isa ya facɗ yadda za a yi ibada sai Annabi.
           Ba a son sako-sako da wuce gona da iri. Don abin da ya sa yahadu suka halaka, sun yi saka - sako ne; abin da kuma ya sa nasara suka halaka, sun wuce gona da iri ne. Nasara sun ɗauki Annabawa sun kai su matsayin Allah, suka jingina Annabi Isa, suka mayar da shi (ɗan Allah, ko wani
ɓangare na Allah. Yahudu kuma sun yi jafa’i ga Annabawa, suka ƙi bin umarninsu. Saboda haka, addinin musulunci a tsaka-tsakiya yake, bai yarda da saka-sako ko wuce gona da iri ba. Galibi abin da yake sa wa a wuce gona da iri, shi ne jahilci, sannan abin da yake sa wa ka ƙi yin abin
da ake so ka yi, shi ne son zuciya. Yahudawa suna da ilimi, sai son zuciya, nasara kuwa jahilai ne, don haka duk inda aka kawo su a Alƙur’ani, za a nuna su jahilai ne. Abin da suke yi ba wajabta musu aka yi
ba, amma sai suke da’awar suna da kyakkyawar niyya, don haka aka sa musu suna ‘ɓatattu’(A1-Dhalin). Shi ya sa ake so mu yi ilimi, kuma mu yi aiki da ilimin. Rashin ilimi sai ya sa mu yi bauta da jahilci, ka ga sai mu ɗauki sifa irin ta nasara. Yin ilimi da ƙin aiki da shi, a bi son zusiya, sifa ce ta yahudu. Duk Wanda ka ɗauka ba ka yi aiki da wannan kalma ba.
        Kuma mutum ya shaida cewa Annabi Isa bawa ne na Allah kuma manzonsa ne, sannan kalma ce  ta Allah da ya fuskantar da ita ga Maryam, kuma Ruhi ne daga Allah. Shi ne malamai suke cewa, shin Annabi Isa shi ne kalmar ko kuwa ya samu ne a sanadiyyar kalmar Allah’? Imam Ahmad ibn  Hambal, yake cewa, “Shi Isa ba shi ne kalmar ‘kun’ ba, ya kasance lokacin da aka ce ‘kun’. Don haka ‘kum’ daban, Isa daban, ya samu ne a sanadiyyar fadin kalmar, kuma ruhi ne daga Allah. Wato, yana cikin
rayuka daga cikin rayukan da Allah ya halitta.” Halitta ne shi, na Allah.
       Kuma ya yarda aljanna gaskiya ce. Ka yarda akwai ta yanzu da abin da Allah ya halitta na dangin ni’ima a ciki.
     Kuma ya yarda wuta gaskiya ce. Ka yarda akwai wuta da abin da aka tanada na azaba a cikinta. Wanda duk ya yarda da waɗannan, Ubangiji zai shigar da shi aljanna a gwargwadon abin da ya kasance a kai
na aiki.
      Me ake nufi da, “Za a shigar da shi aljanna a gwargwadon abin da ya kasance a kai na aiki?” Shi ne malamai suke cewa, “Ko da yake ‘yan aljanna sun yi tarayya cikin sunansu na ‘yan aljanna, to aljanna darajoji ce. Kowa zai shiga gwargwadon darajarsa.” Shi ne Manzon Allah yake cewa, “Idan za ku roƙi Allah aljanna, to ku roƙe shi aljannar Firdausi, domin ita cc can ƙarshe kuma mafi tsadarta.” [Bukhari #2790].

********************
Kuma daga gare su [Bukhari #425 da Muslim #657] daga hadisin Itban cewa, “Lallai Allah Ya haramta wuta ga Wanda ya faɗi, ‘La’ilaha illal lahu’ yana neman yardar Allah da ita.”
________________
   SHARHI;
Abin nufi a nan shi ne faɗar ta da ikhlasi, kuma mutum ya faɗe ta, tare da sanin ma’anarta, sannan ba ya shakka wajen ma’anarta, kuma yana cikakken son abin da ta koyar. Faɗa a baki kawai ba zai wadatar ba sai an haɗa dukkan sharaɗanta guda bakwai. To duk Wanda ya faɗe ta da waɗannan sharuɗɗai to Allah zai haramtawa wuta shi. Sanadiyyar da Annabi ya faɗi Wannan, wata rana ana zaune a wurin Itban ibn Malik, wani rnutum ya taho, sai waɗansu suke cewa ai munafuki ne. Sai Manzon Allah ya ce, “Kada  ku ƙara faɗar haka, ai Allah ya haramta wa wuta duk Wanda ya ce ‘Laa ilaaha fllallaah’ yana neman yardar Allah da ita.”
********************
An karɓo daga Abu Sa’id Al-Khudri.(RA) daga Manzon Allah (ﷺ)  ya ce, “Musa ya ce, “Ya Ubangijina! Ka sanar da ni wani abin da zan riƙa ambatonka da shi, kuma na roƙe ka da shi.” Sai. ya ce,
“Ya Musa! Ka faɗi, ‘La ilaha illallahu’” Sai ya ce, “Ya Ubangiji! Ai dukkan bayinka suna faɗin haka.” Sai ya ce, “Ya Musa! Da sammai ‘bakwai da duk Wanda yake cikinsu ba ni ba, da kuma kassai bakwai,
suna kan hannu guda na sikeli, kuma ‘La ilaha illallahu’ tana ɗaya hannun, da ‘La ilaha illallahu’ ta rinjaye su.” Imam ibn Hibban [#6218] ne ya ruwaito kuma Imam Hakim ya ce hadisi ne sahihi.
__________________
SHARHI;
Bincike ya nuna cewa, wannan hadisin mai rauni ne. Amma kuma akwai hadisai guda biyu da za su isar da saƙon da wannan hadisi yake so ya isar.
       Hadisi na ɗaya shi ne hadisin Abdullahi bin Amru bin As, Wanda Imam Ahmad ya ruwaito, Annabi Nuhu (AS) mutuwa ta zo masa, don haka sai ya ce da ɗansa, “Abin da zan yi maka wasici da shi, shi ne, ka yawaita faɗin ‘La ilaha illallahu.’Abin da ya sa na ce maka haka, shi ne da a ce saman bakwai da ƙasan bakwai gabaɗaya za a tattara su da abin da yake cikinsu, a ɗora a sikeli da ‘La ilaha illallahu’ ta rinjaye  su a ɗaya ɓangaren.”[Ahmad #7101]
         Sannan akwai hadisi na biyu, shi ne Hadisul Biɗaƙah, hadisin da Imam Tirmizi ya ruwaito shi kuma ingantacce ne. A dunkule, abin da hadisin yake cewa shi ne, ranar alƙiyama za a zo da wani mutum gaban
Allah domin a yi masa hisabi, Za a kawo manya-manyan takardu na irin Iaifukan da ya yi a duniya har guda casa’in da tara (99), babu abin da yake ciki sai ɓarna. Ubangiji ya tambaye shi ya ce, “Shin rnala’iku da suke rubuta aiki sun zalunce ka?” Sai ya ce, “Ya Ubangiji! Ba su zalunce ni ba laifin da na yi suka rubuta.” Sai Allah ya ce da shi, “T kana da tacewa?” Sai ya ce, “Ya Ubangiji ba ni da tacewa.” Sai Ubangiji ya ce, "Ka manta kana da wani kyakkyawan aiki a wurinmu.” Sai a ɗauko wata ƙaramar takarda, sai a ce, da shi “Kyakkyawan aikin naka yana cikin awannan ‘yar takardar.” Sai a bude takardar, babu abin da yake ciki sai ‘La ilaha illallahu Muhammadur-rasulillahi ’. Sai ya ce, “Yaya za a yi ƙaramar takardar nan ta rinjayi waɗannan?” Sai Ubangiji ya ce, “A sanya  ta a kan sikeli.” Sai ta rinjayi waɗancan, sai ya shiga aljanna [Tirmizi #2639, Ibn Majah #4300]. Wannan hadisi ne ingantacce.
            A taƙaice, waɗannan hadisai guda biyu na ɗauke da saƙon da wancan hadisi yake ɗauke da shi a babin falalar tauhidi. Duk da cewa idan muka kawo wannan hadisi na ibn Hibban, hadisi ne mai rauni ta
fuskar ruwaaya, amma akwai hadisai ta fuskar matani waɗanda suke ɗauke da sakonsa. Dukkan Wannan na nuna. mana falalar tauhidi ne da kuma cewa tauhidi idan ya tabbata a zuciyar (ɗan Adam na iya sawa a kankare zunubansa.
    
********************
    Daga Tirmizi [#3540] ya ce hadisi ne mai kyau, daga Anas ibn Malik (RA) ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ)  yana cewa, “Allah ya ce, “Ya kai ɗan Adam! Da a ce za ka zo wurina da cikin ƙasa na laifi, sannan ka gamu da ni gobe ƙiyama ba ka yi tarayya da ni wurin ibada ba, da na kawo maka kwatankwacinta na gafara.”
______________
SHARHI;
Abin da ake so mutum ya fahimta a waɗannan hadisai shine, ana so ya fahimta a mahanga ta Ahalus-Sunnah wal-jama’ah. Kada irin abin da waɗannan hadisai suke dauke da shi ya sa Shaiɗan ya yi maka raɗa, ya sa ka kwanta, ka ƙi yin ibada da aiki nagari. ldan ka yi wannan, to ka zamto ka amintu da makarin Allah. Don haka, ba a amintuwa da makarullahi, so ake ka yi aiki ka tabbata a kan haka. Don shiga aljanna daban, samun bene na sama daban, aiki ne zai taimaka ka samu wannan. Ba a son kana
da matsayin da za ka samu bene na goma, ka tsaya a bene na ɗaya. Ya kamata ka ƙara himma, ka zage dantse.
     Na biyu, ka fahimci cewa Annabi (ﷺ)  Wanda shi ne shugaban halitta, an ba shi buɗ  mabayyani, an gafarta masa zunubansa na da, da wanda zai yi nan gaba, idan har zai yi din. Allah ya cika ni’imarsa gare
shi, ya yi masa alkawarin nasara da shiriya. Tare da haka yake tsayuwar dare, ƙafarsa take tsattsagewa ta kumbura a sakamakon ƙiyamul-laili. Duk da wannan matsayin har Aisha (RA) take cewa da shi, “Yaya za ka riƙa wahalar da kanka, bayan an gafarta maka?” Sai ya cc, “To, ba Zan zama bawa mai godiya ba‘? ”[Bukhari #4837, Muslim #2860] irin wannan fahimtar aka so ka yi wa waɗannan hadisai. kada ka yi fahimta ta irin waɗanda za su amince da ‘makarul-lahi ’. Kana ganin ai tun da ba na shirka, to mun hau tudun-mun-tsira, ba sai na yi ƙiyamul-laili ba, ba sai na yi zikiri da salatin Annabi ba. Bayin Allah nagari ko da wane lokaci ƙara himrna suke yi wajen bin Ubangiji, suna kusantar kabari, suna ƙara aikin alheri kuma suna rokon Allah ya ƙara musu rahama. So ake kullum ka ƙara aikin alheri har ka bar duniya. Haka kuma kar ka ji hadisan da suke razanarwa a kan aikin saɓo, waɗanda suke nuna da ka yi aikin saɓon za ka shiga wuta, irin waɗannan ba a so ka fahimce su irin yadda Khawarij suka fahimce su. Khawarij yadda suka fahimci waɗannan ayoyi da hadisai shi ne, duk Wanda ya aikata aikin saɓo ya mutu, zai shiga wuta
ya dawwama a ciki ba fitowa! Idan ka yi haka ka zamto cikin waɗanda suke ɗebe tsammani da rahamar Ubangiji  Kuma Allah ya ce kar a ɗebe tsammani daga rahamarsa duk yawan saɓon muturn. Amfanin hadisan raharna, mutum ya sa rai, hadisan azaba mutum ya tsorata. Idan mutum yana cikin halin tsoro da sa rai, to kullum zai dunga aikin alheri.
        Wannan duk yana nuna mana falalar tauhidi. Idan tauhidi ya ginu,
to aiki ya ginu. In ba tauhidi, to komai ya rushe.

********************
Acikin Wannan Babi Akwai Mas’aloli Kamar haka;
1.           Yalwar falalar Ubangiji.
__________
Sharhi;
Ta yadda za ka yi saɓo mai yawa ga Allah, amma falalarsa ta sa a yafe maka saɓon. Kullum abin da za ka ƙudurce ka sani, shi ne, yalwar falalar Ubangiji  ta fi azabarsa yawa.
2.           Yawan ladan da tauhidi yake da shi wurin Allah.
3.           Tauhidi yana haifar da kankarewar zunubai.
4.           Mun fahimci tafsirin aya ta cikin Suuratul An’am.
5.           Lura da al’amura biyar (5) ɗin da ke cikin hadisin Ubada ibn Samit.
6.           Idan ka haɗa tsakanin hadisin ltban da abin da ya biyo bayansa, zai bayyana gare ka ma’anar, ‘La ilaha illallahu’­sannan kuma za ka gane kuskuren waɗanda suka ruɗe.
_________
Sharhi;
Wato ma’anarta idan ka haɗa hadisan, shi na, babu abin bautawa da gaskiya, sai Allah (SWA)
     Idan ka tambayi wani yanzu ma’anar kalmar, sai ya ce; ai babu sarki sai Allah, babu mahallaci sai Allah, ba mai azurtawan sai Allah, har yanzu bai san ma’anarta ba. Saboda da wannan ne ma’anarta, da Annabi (ﷺ)  bai zare takobi ya yaƙi su Abu Jahil da su Abu Lahab ba. Saboda duk sun yarda da wannan. A ina ne ba su yarda ba? Shi ne, Wajen babu abin bautawa da gaskiya sai Allah. Abin da ba su yarda ba shi ne cure bauta ita kaɗai a jinginawa Allah, in da za a bautawa Allah, kuma a bautawa gumakansu, to za su yarda ko da a ce bautar Allah za ta fi yawa. Amma a ce Allah shi kaɗai, to wannan shine abin da suka musa, kamar yadda Allah ya ba da labarinsu:
 “Shin ya sanya ababen bauta duka su zama abin bauta guda ɗaya? Lalle wannan haƙiƙa abu ne mai ban mamaki.”(Saad:5)
Ma’ana, yanzu dukkan alloli a manta da su gaba ɗaya, a ce a wajen ɗaya za a dogara, shi za a roƙa, da sunansa kaɗai za a yi rantsuwa, idan za 'a faɗ shi za a kira? Yanzu Wannan za a yi? To shine suka ƙi yarda. Amma sun yarda Allah a ba shi nasa, wasu ma a ba su wani kason. Don haka sai suka rabu gida biyu, suka raba ƙafa.
 “To a lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, suna kiran Allah suna masu tsarkake addini gare shi, to a lokacin da ya tserar da su zuwa ga ƙasa, sai ga su suna shirka.”(Ankabuut:65)
Haka su Abu Jahil suka dinga yi, idan suna cikin tsanani sai a kira Allah shi kaɗai, idan ana cikin yalwa sai su kira gumakansu. Ta haka za ka gane irin hadarin da mutanenmu suke ciki. Sun yarda da Allah (SWA) ne yake kashewa, yake rayawa, karnar yadda su Abu Jahil sun riga su yarda da wannan. Sun yarda a bautawa Allah, amma ba shi kaɗai ba. Sai shaiɗan ya ba su dabara, bautar da za su yi ga wanin Allah, sai su ƙi kiran ta da suna ibada, sai su kira ta tawassuli ko ceto. Su ce ai abubuwan da muke kira, su ne masu ceton mu wajen Allah, su ne ‘yan fada a wajen Allah. Har ka ji suna ba da misali da sarki da fadawa ko gwamna da masu tsaronsa wai yanzu za ka je wajan sarki ne kai tsaye ba fadawa?! Ka ga sun kwatanta Allah da sarki! Sai su ce yadda kake son abu wajen sarki ka kama ƙafa da fadawa, haka  idan kana son abu Wajen Allah sai ka kama ƙafa da waliyyai da salihai da khuɗubai. Suna hada Allah da sarki ko
gwamna, sun manta da gwamna da sarki, duk gajiyayyu ne. Lokacin da ka je ziyara wajen sarki ko gwamna, bai san da me ka zo masa ba. Ka zo ka cuce shi ko ka taimake shi? Don haka sai ya samu masu tsaro da za su kare shi daga wani sharri. Tare da haka ga masu tsaron wata rana za a harbe shugaban kuma a yi juyin mulki! To yanzu haka Allah yake‘? Allah tsoron juyin mulki yake da zai sa waliyyai su yi gadinku yadda ba za ku iya yi masa komai kai tsaye ba‘?! Ya kamata mutane su fahimci wannan.
Wallahi duk rigimar da Annabi (ﷺ)  ya yi da su Abu Jahil, ba wai don ba su yarda da Allah ba ne. A’a, sun yarda da Allah, ayoyi da dama sun ba da shaidar haka. Kuma sun yarda a bauta masa, sai dai ba shi kaɗai ba. To haka ma yau, masu bin ɗariku, sun yarda a bautawa Allah amma ba shi  kaɗai ba. Sai suka canza wa ibadar suna kamar yadda su ma su Abu Jahil suka canzawa bautar da suke yi wa gurnakansu suna zuwa ‘neman kusanci’ kamar yadda aya ta ce:}
 “Kuma waɗanda suka riƙi waɗansu (gumaka) majiɓinta lamari ba shi (Allah) ba, (suna cewa) ‘ba mu bauta musu ba face domin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja.” (Zumar:3)
Haka Abu Jahil zai ce, ai ba bauta musu muke ba, neman kusanci muke ta hanyarsu. To haka yanzu za ka ji suna faɗa, ai waliyyai ba bauta musu muke ba, neman kusanci rnuke yi! Kai wallahi ta wanni fannin ma har gwanda su Abu Jahil! Saboda su sun yarda Allah ne yake komai. Amma na yanzu, sai su ce ma, ruwan sama waliyyi ne yake kawo shi, arziki, waliyyi ne, haihuwa waliyyi ne, kashewa da rayawa duk waliyyi ne. Idan ka talauce sai a ce waliyyi ne ya yi fushi da kai. Wanda Abu Jahil ma bai yarda da wannan ba! To ina hankulan mutane suke? Wallahi ba yadda za a yi abubuwa su gyaru, sai an fahimci tauhidi.
7.           Faɗakarwa dangane da sharaɗn da ke cikin hadisin Itban.
8.           Kasancewar Annabawa suna buƙatar tanbihi wato faɗakarwa a kan falalar, ‘La ilaha ilallahu.’
9.           Faɗakarwa dangane da yadda (kalmar tauhidi), take rinjayen dukkanin halittu, tare da cewa da yawa daga cikin masu faɗar kalmar za a ga mizanunsu ya yi ƙasa.
10.     Nassi ƙarara cikin hadisi, cewar yadda sama take guda bakwai, lallai ƙassai su ma bakwai ne.
11.     Haƙiƙa a cikinta akwai masu rayuwa (sammai).
12.     A cikinta akwai tabbatar da siffofin Allah saɓanin Al’ash’ariyya.
___________
SHARHI;
Wato wannan ya zo a hadisin farko na nuna kalmar Allah  su Asha’ira sun yi tawilin siffofin Allah. Cikakken bayani a kan siffofin Allah zai zo a babi na 40.
13.     Idan ka san hadisin Anas, to ka san faɗin Manzon Allah (ﷺ)  cikin hadisin ltban da ya ke cewa, “Lallai Allah ya haramta wuta ga duk Wanda ya ca, ‘La ilaha illallahu’ yana neman yardar Allah da ita.” Cewa ma’anarsa ya bar shirka ne, ba wai ya faɗa da harshe kawai ba ne.
___________
SHARHI;
Wato hadisin Anas ibn Malik sai ya nuna ba wai kawai ka faɗi Kalmar shahada da baki shi kenan, wuta ba za ta taɓa ka ba, a’a, ta na nufin rashin yin shirka, saboda nassin cikin hadisin Anas (RA) ɗin inda yake cewa “...Da a ce za ka zo wurina da cikin ƙasa na laifi, sannan ka gamu da ni gobe ƙiyama ba ka yl tarayya da ni wurin ibada ba...” Wannan sai ya nuna ashe kullum ka fadi kalmar shahada sau miliyan, matufiar ka yi shirka kamar rantsuwa da wanin Allah, kiran wanin Allah idan za ka faɗi, to ta rushe!
14.     Kulawa da kasancewar Isa da Muhammad, tsira da aminci ya tabbata a gate su, bayi ne na Allah, kuma manzaninsa ne.
15.     Keɓantar Isa (AS) da kasancewarsa kalmar Allah.
_____________
SHARHI;
Wato samuwarsa ta kasance daga kalmar Allah cewa, ‘kun’ kasance Isa, sai ya zama. Wannan falala ce ta Annabi Isa (AS). Kamar yadda Allah (SWA) ya halicci Annabi Adam (AS) da hannayensa kamar yadda aya da hadisai suka tabbatar.
 “(Allah) ya ce ‘Ya Iblis me ya hana ka, ka yi sujjada ga abin da na halitta da hannayena biyu?” (Saad:75)
16.     Sanin kasan cewarsa ruhi ne daga Allah.
17.     Sanin falalar yin imani da aljanna da wuta.
18.     Sanin faɗin Manzon Allah (ﷺ) , “…..a kan abin da ya kasance na aiki.”
19.     Sanin cewa mizani yana da tafuka biyu ne.
20.     Sanin tabbatar da siffar fuska ga Allah.(6)
___________
SHARHI;
Ana tabbatarwa da Allah siffa ta fuska kamar yadda ya tabbatarwa kansa. Ayoyi da dama cikin Alƙur’ani sun tabbatar da siffar kamar.
“Fuskar Ubangijinka ce ma’abocin girma da karramawa. kaɗai za ta yi saura (Ar-Rahman:27)
"Sai dai neman Fuskar Ubangijinsa Maɗaukaki." (Al-Lail:20)
Wasu suka ce a nan, ana nufin zatin Ubangijin gaba ɗaya, amma wannan tawiline. Dole  ka yarda Ubangiji yana da fuska, saboda ya tabbatar a ayoyin da aka kawo. Shin fuskar irln ta  wanece‘? A’a! ba haka ba ne saboda ƙa’idar
“Ba abin da ya yi kamanceceniya da shi, kuma shi ne mai ji, mai gani.”(As-Shura; 11)
Kasancewar ka tabbatarwa da Allah  fuska, ba ya nuna ka kamanta shi da wani, sai dai  idan ka yi wannan ƙudurin a zuci. Idan matambayi ya tambaye ka, ya ya fuskar take? Sai ka ce, ba ka sani ba, don Allah bai yi bayanin yadda take ba. Sannan kuma ba ta kama da dukkan ababen halitta. Wannan shi ne ƙa’idar Ahlussunna waljama’a. Amma idan ka yi tawili, ka ce wai zati ake nufi, yanzu kana tuhumar Allah da zaurance?! Zai ce zati, ya ce fuska‘? To yanzu sai kai da aka halitta a ƙarshen zamani za ka zo ka yi bayanin siffar Ubangiji! Ya kamata mutum ya gane kuskuren da ke clkin tawili, Allah ya saukar  da nassi kuma ya ce;
 “Lallai shi zance ne mai rarrabewa” (Ɗaariƙ;13)
Da sauran ayoyi da suke nuna Alƙur’ani a bayyane yake, kuma mai shiryarwa ne, amma duk da haka a ce sai ka yi tawili?! Zahirin aya ta ce kaza, amma kai ka ce ba haka Allah (SWA) yake nufi ba! Yanzu abu biyu ka jawowa kanka. Na farko, ka ce ba haka Allah yake nufi ba. Na biyu, ana bin ka bashin kawo me ake nufi a wajen. Kuma da ka ce, kaza Allah yake nufi, to wa ya gaya maka hakan ake nufi? Wa ya yi ma wahayi ya faɗa ma‘? Me ka dogara da shi? Yanzu da ka rushe na farko Wanda Allah yake nufi, ka kawo naka, wani ma zai rushe nakan ya kawo wani daban, wani ma ya kawo wani, duk ciki wa zai iya kayar da ɗan uwansa Wajen rigimar tabbatar da ma’anar? Wanda duk zai kayar da kowa, shi ne wanda ya ce,
dukkan waɗannan fassarorin ƙarya ce! Ma’anar ayar shi ne abin da Allah (SWA) ya faɗa a zahiri. Kun ga wannan yana da hujja ƙarara wadda ita ca ayar. Wannan shi ne illar da ke cikin tawili. Duk Wanda ya rusa


musulunci ta hanyar tawili ne. Nasara ta fuskar tawili suka ƙirƙiro kiristanci, duk Wanda ya halaka, galibi ta hanyar tawili ne. Allah ya tsare mu. Amin.

(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...