Duk Wanda Ya Tabbatar
Da Tauhidi Zai Shiga Aljanna Ba Tare Da Hisabi Ba
_______________
SHARHI;
Wannan babin kamar
cukon babin baya ne. Babin baya ya yi bayani akan falalar tauhidi da yadda yake
kankare zunubai. Wannan kuma zai yi bayanin cewa, duk wanda ya tabbatar da
tauhidi, haƙiƙanin tauhidi, to zai shiga aljanna ba tare da hisabi ba, wato
babu ƙididdugar ayyuka, kuma babu azaba. Ana tashi ƙiyama,
sai a kai su aljanna.
Allah Ya sanya mu acikinsu. Amin
Haƙiƙani tauhidi shi ne, tace shi
daga dukkan datti da shirka, wato mutum bai yadda da malamin duba ba, bai yadda
da boka ba, dukkan wani abun da yake haƙƙin Allah (SWA) ne ya tabbatar masa Shi
kaɗai. Sannan kuma ya tace tauhidi daga dukkan wani dangi na bidi’a ta faɗa a
baka, ko a aiki.
To wannan kuma ba zai yiwu ba said a karatun yau da gobe. Domin ba yadda za ayi mutum ya san dukkan bidi’o’in da suke garinsu. Dole sai da karatu mutum zai ji wannan abu bidi’a ne sai ya daina. Yadda kullum kake nisantar bidi’a, haka tauhidinka yake ƙara haske, kana ƙara tace shi da wanke shi, har ka shiga cikin waɗanda suke tabbatar da tauhidi.
To wannan kuma ba zai yiwu ba said a karatun yau da gobe. Domin ba yadda za ayi mutum ya san dukkan bidi’o’in da suke garinsu. Dole sai da karatu mutum zai ji wannan abu bidi’a ne sai ya daina. Yadda kullum kake nisantar bidi’a, haka tauhidinka yake ƙara haske, kana ƙara tace shi da wanke shi, har ka shiga cikin waɗanda suke tabbatar da tauhidi.
**************************
Da faɗin Allah; “Lallai
Ibrahim ya kasance jagora, mai ƙanƙan da kai ga Allah, mai karkata zuwa ga
gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirka ba.”( An- Nahl:120)
____________
SHARHI;
Wannan ayar ta yi bayanin suffofi
guda huɗu, wanda duk ya suffanta dasu, kamar yadda annabi Ibrahinm (ASW) ya
suffanta dasu, to ya tabbatar da tauhidi, haƙiƙanin tabbatarwa.
Ummatun; Wato shugaba
abin koyi. Ba ka zama shugaba abin koyi, sai ka tara dukkan suffofi abin yabo,
ka nisaci dukkan siffofi ababen ƙi gwargwadon hali. A cikin ajin farko na
alma’aruf, shi ne tauhidi, sannan ibada, kyawawan ɗabi’u, mu’amala da sauransu.
A cikin munkari abin da ya fito a ajin farko, itace shirka, bidi’a da saɓo.
Wanda duk ya suffantu da wɗannan halaye, to zai zamto Umma, wato abin koyi, a
ban-ƙasa, ko da shi kaɗai ne. An rawaito daga Abdullahi ibn Abbas, ruwayar Ibnu
Abi Hatim ya ce, “A lokacin annabi Ibrahim banda shi, babu kowa musilmi a
ban-ƙasa, har sai lokacin da ya yi hijira suka haɗu da Annabi Luɗ (ASW), sannan
Ubangiji Ya ba shi ‘ya ‘ya. Daga nan ne aka fara samun musulmi” [Duba Tafsirin
Ibn Abu Hatim tafsirin suuratun Nuhl 9/127] Lokacin da aka kawo ƙissar za’a
halaka Annabi Ibrahim, a sa shi a wuta shi kaɗai ne, ba a ce za a sa su tare da
wani ba. Domin shi kaɗai ne musulmi kuma saƙon da aka aiko wa al’umma, suka ƙi
karɓa, shi kaɗai ya karɓa, ya zama al’umma.
Ƙanitan-lillahi: Sheikhul Islam ibn
Taimiyya ya ce, ‘Alƙunut’ shi ne dimantar ɗa’a. Babu yadda za a ce ka dimanci ɗa’a
awa ashitrin da huɗu, sai dai abin da ake nufi shine a sami kasha tamanin ko
casa’in cikin ɗari. Annabi Ibrahim(ASW) kuwa zai iya samun kasha ɗari, domin
shi ma’asumi ne kuma Annabi n. amma wanda ba Annabi ba, to ba zai iya dimantar ɗa’a
ba. Sai daya ya zamanto alherinka ya yi yawa. Tunda ba zaka iya tsarkake kanka
daga zunubi ba, to ka zamanto irin mutanen da idan sun yi zunub, ba sa dawwama
a kai. Ya zamanto da ka yi zunubi, sai ka dimanci istigfari, sai ka samu gafarar Ubangiji, ka dimanci ɗa’a, yawan
sallar dare, istigfari da salatin Annabi.
Hanifan: Ibnul Ƙayyim y ace,
“Mutumin day a fuskanci Allah (SWA), kuma ya kawar da kai daga dukkan
abin da ya zama dangin buƙata na irin wanda ɗan Adam ba ya iya ya, ka
fuskanci Allah das hi. Dukkan abin da
yake haƙƙi ne na Allah, wato ibada kenan, kowace iri ce ka nufaci Allah (SWA)
da ita, to idan ka yi haka, ka zama ‘hanif’, kuma haka ake so mutane su zama
‘hunafa’a’.
Wa lam yaku minal mushrikin: Bai
kasance da masu shirka ba. Me ake nufi da haka? Wato ba ya yin shirka, kuma bai
goyi baya ba. Ko da ba yin shirka, sai
ya zamto ba ka goyi bayan a yi ba. Wannan rashin goyon bayan a yi, zai ɗauki
mataki daban-daban. Wataƙila kana da ƙarfin da za ka hana, to sai ka hana ɗin,
ko kana da ƙarfin da za ka iya hanawa da hannu, to ka yi hakan. Wataƙila ba ka
da dama, sai dai ka ƙiabin a zuciya, sai ka yi ko kuma ka ta shi daga wurin ka
koma inda ake tauhidi tsantsa, ko mai
jin daɗin da kake yi a wurin. Tauhidi bay a yiwuwa sai ka ƙi shirka, sai ka yi
fito-na-fito da mai yin shirka. Kada ka ce zaka zauna da mutanan da suke
shirka. Haka Annabi Ibrahim (ASW) ya yi da mutanensa da mahaifinsa ahalin da
suka shiga na shirka. Ya yi musu wa’azi sukaƙi ji, sai ya yi hijira, sakamakon
haka Allah (SWA) Ya saka masa da ‘ya ‘ya duka Annabawa, Isma’il da Is’haƙa. Don
haka duk wanda ba zai sake wurin bautar Ubangiji ba, wajibi ne ya canza wuri.
Idan unguwa ce ko gari ko ƙasa ce, ya canza wata. Don haka ba a yanke hijira
ba, daga nan har ƙiyama,tana nan.
********************
Da faɗinSa;
“(Bayina nagari) su ne waɗanda ba sa yin
shirka da Ubangijinsu” (Al- Muminun:59)
________________
SHARHI;
Asali shiraka iri biyu ce: Akwai babbar
shirka (Shirkul Akbar); it ace take ɗaukar mutum daga musulunci, ta kai shi
wajen musulunci. Wato, bautwa wanin Allah, ko ka roƙi wani, ka yi sallah ko
azumi don wani, ka yi bakance saboda wani, irin abin da ake yi don Allah, amma
sai ka yi don wani. Waɗannan duk nau’ika ne na shirka.
Akwai shirka ƙarama (Shirkul Agar);
misali riya, kamar yadda Manzon Allah (ﷺ) ya fassara. Menene riya? Asalin abu ka yi shi
don Allah, amma sai ka kyautata abin don wani ya yaba, ko da ba don wannan ba,
ka iya yin aikin, amma ganinsa sai ka kyautata don ya ce ya yi, ko ka yi don ka
munana wa wane, to wannan ya zamo ba don Allah ba tsantsa. Wannan shirk ace
ƙarama. Ba ta mayar da mutum kafiri,sai dai dukkan aikin da irin wannan shirka
ta shiga ya lalace, Allah ba zai karɓi wannan aiki ba, kamar yadda Allah ya ce,
“Ni na wadata da a haɗa ni da abokin tarayya. Duk wanda ya aikata aiki, sai ya
haɗa ni da wani, (yana son na ba shi lada, kuma yana son wane ya bas hi ), ni
wadatacce ne, sai na bar wa wancan ɗin shi kaɗai,”[Muslim #2985,Ibn Majah
#4202]. Wannan riya da take shiga cikin aiki, ta zama ƙaramar shirka, ko ta
lalata aiki. Malamai suka ce yaushe ne za ta lalata aiki kuma yaushe ne ba za
ta lalata ba? Don akwai bambancin riya da ta shiga daga farkon aiki har ta kai
ƙarshe, akwai bambanci a kan riyar da ka yi zango a cikin aikin, ka yi rabi,
sai wani ya gani, sai ka kyautata masa rabin. Farko, kana yi don Allah, amma a
tsakiya sai wani ya ga kana yi, sai ka kyautata masa rabi. Duk malamai sun yi
magana a kan wannan; Musamman Hafiz Ibn Hajar Askalani a cikin sharhin hadisin
Innamal a'amaalu binniyat-wa Innama likullim-ri’im maanawa, a cikin Fathul
Bari, [ƙarƙashin hadisi na ɗaya] Haka kuma, Imam Ibn Rajab al-Hambali a cikin
sharhin da ya yi wa ‘Arba ’una Hadithan, [ƙarkashin hadisi na ɗaya] ya yi
sharhi mai kyau a ciki. A taƙaice dai, riya ƙaramar shirka ce. [Don ƙarin
bayani duba Fassara da Sharhin Arba’una Hadithan, na Sheikh Ja’afar Mahmoud
Adam, ƙarƙashin hadisi na ɗaya.]
Haka kuma, rantsuwa da
wanin Allah, amma ba ta fitar da mutum daga musulunci, kamar yadda malamai suka
yi bayani. Domin wani ya zo ya rantse da Annabi da mala’ika Jibrilu, ya ce, “Na
rantse da Annabi, na rantse da mala’ika J ibrilu, na rantse da kabarin Nana
Fatima!” Ka ga ya yi shirka, amma ƙarama, bai fita daga musulunci ba. Musulmi
ne amma yana ƙaramar shirka. Domin Manzon Allah ya ce, “Duk wanda yake son yin
rantsuwa, to ya rantse da Allah, ko ya yi shiru.” [Bukhari #6108,627O Muslim
#1646] lrin wannan shirkar daidai take da kaba'ira, babban laifin da akwai
zunubi na nan tuli, har sai idan mutum ya tuba a kankare shi, ko idan yana da
wani abin da zai sa a kankare zunubin cikin dangin abubuwa goma sha biyu da
Ibnul Kayyim ya yi bayaninsu a cikin littafin, ‘Madarijus-Salikin bayna manazilu
lyyaka na’abudu wa-Iyyaka nasta'in idan ba haka ba, za a kama shi da azaba.
Haka kuma, kuka na
mutuwa ma shirka ce ƙarama. Haka dukkan kaba’ira a wurin wasu malaman, shirka
ce ƙarama. Wasu suna cewa, ba za a ce dukkanninsu ba. sai idan Annabi (ﷺ) ya tabbatar cewa shirka ne, ko ya sanya musu
suna aI-kufur ko al-shirk, kuma muka ga cewa, bai kai al-shirkul-akbar ba, sai
mu sa masa al-shirkul Asgar ko al-kufurul-Asgan Kamar yadda Annabi (ﷺ) ya nuna cewa, kukan mutuwa irin wanda ake yi
ana ambaton ayyukan mamaci, ya sanya masa suna kafirci. Haka kuma, alfahari da
ƙabila ko da gari ko yare, su ma duk Annabi (ﷺ) ya sa musu suna kafirci. To, amma duk ana sa
su a cikin ƙaramin kafirci ko ƙaramar shirka.
To, tauhidi ba a tace
shi, sai idan mutum ya nisanci Shirkul Akbar da shirkul Asgar, to zai shiga
aljanna ba tare da hisabi da azaba ba. Wanda ya nisanci Shirkul akbar, amma
yana Shirkul Asgar zai shiga aljanna, amma zai iya yiwuwa da hisabi. Don
haka Allah Y ace;
“Waɗanda ba sa shirka
da Ubangijinsu” (Al-Muminun:59)
A takaice dai, ana kore
dangin shirka ne, kowanne iri. Ana nufin muminai ba sa kowanne irin shirka
babba da ƙarama. Kuma suna nisantar kaba’ira, sai dai wani lokaci su faɗa ciki
su tuba.
********************
An karbo daga Husain
ibn Abdurrahman, ya ce, “Na kasance a wurin Sa’id bin Jubair, sai ya ce, “Waye
a cikinku wanda ya ga tauraron da ya faɗo da daddare?” Sai na ce da shi ‘ni’
Sai na ce, “Ku saurara! Ba fa sallah nake ba lokacin da na gan shi, sai dai
kunama ce ta harbe ni.” Sai ya ce, “Me ka yi (da kunama ta harbe ka)?” Sai na
ce, “Na yi tofi (ruƙya) ne.” Sai ya ce, “Wa ya ce ka yi tofi?” Sai na ce, “Wani
hadisi ne da Sha’abiy ya faɗa mana.” Sai ya ce, “Me ya faɗa muku?” Sai na ce,
“Ya ba mu hadisi daga Buraidata bin Husaib (Ibn Haris al-Aslamiy) ya ce, “Ba a
yin tofi sai idan kambun baka ya samu mutum, ko wani abu mai dafi ya harbe ka
da ƙarinsa.” Sai ya ce, “Duk wanda ya yi aiki da abin da ya ji, to ya kyauta.
____________
SHARHI;
Sa’id bin Jubair babban
tabi’i ne, ɗaya daga cikin ɗaliban Abdullahi bin Abbas. Ya mutu shekara ta 59
bayan Hijira. Hajjaj bin Yusuf ne ya kashe shi don zalunci.
“Wa ya ce ka yi
tofi?" Sai na ce, “Wani hadisi ne da Sha’abiy ya faɗa mana.” Wannan sai ya
nuna duk abin da mutum zai yi a musulunci sai yana da hujja ta shari’a. Sannan
kuma, hujjar kowa shi ne, hadisin Annabi (ﷺ) . Ba a kafa hujja da cewa ‘malam
wane ya ce...’ sai dai fadar Annabi (ﷺ) .
AI-Ain shi ne
kambun-baka. Kambun-baka yadda yake kuwa, Ubungiji yana halittar wasu mutane da
tasiri ko a idonsu ko a harshensu, ta yadda idan suka ga abu ya burge su, ko
suka ƙawata abin da bakinsu, idan ya burge su, kawai sai abin ya faɗi. Galibi
ba da niyya suke yi ba, wasu ma ba su san sun yi ba, sai daga baya a faɗakar da
su. Wasu kuwa sukan gane sun yi. Dukkan wanda wani ya kalle shi, aka gane, kuma
ya faɗi, sai a yi masa tofi. Mafi girman abin da za ka yi masa tofi da shi, shi
ne Suuratul Faatiha.
Hanya ta biyu, hadisin
da Imam Malik ya rawaito a cikin Muwaɗɗa, hadisi ne ingantacce na Sahl Bin
Hunaif. Wani sahabi ya kwaɓe yana wanka, sai wani ɗan uwansa ya gan shi, sai ya
ce, “Kai! Yau na ga wani mutum mai kyan fata." Kurum sai ya faɗi Aka ɗauko
shi aka kawo shi wurin Annabi (ﷺ) . Annabi ya tambayi abin da ya faru. Suka ce,
mun ji wane ya ce kaza, kawai sai muka ga ya faɗi. Sai Annabi ya ce, “Don me
sashinku zai kashe sashi?" Sai ya ce, “Ya Annabin Allah! Babu abin da na
yi, ga abin da na ce jikinsa ya burge ni, na ce, “Kai! Allah ya ba wa wane jiki
mai kyau.” Sai Annabi (ﷺ) ya ce, “Ina ma
ka ce, ‘Barakallahu fi ka!”-Allah ya ba ka kyakkyawar fata. Da ka faɗi haka, da
bai kamu ba. To zo ka yi alwala.” Sai ya yi alwala a kasko, amma bai zubar da
ruwan ba, sai aka je aka yayyafa wa wannan mutumin, sai ya tashi [Muwadda
#1679]. Wannan ita ce hanya ta biyu ta maganin kambun-baka. Hanya ta farko
kafin faruwarsa, ta biyu, bayan faruwarsa.
Ruƙya: To a wannan
hanya ta biyun, za ka iya yin rukya, saboda nassin hadisin..lta kuma ruƙya wato
tofi, ana yi ne da ayoyin Alƙur’ani mai girma da kuma addu’o’i da suka inganta
daga bakin Annabi (ﷺ) , addu’o’in ba su ƙunshi shirka ki bidi’a ba. Wanda zai
yi karatun ruƙyar (tofi) ya samu wasu halaye gwargwadon haka: Na farko mutumin
da yake da cikakken tauhidi, don shi zai sa ya sami yaƙinin cewa idan an
karanta za ta yi amfani. Kuma ya san cewa, ba karatunsa ba ne zai kawo sauƙin,
a’a, Allah (SWA) ne zai kawo sauƙin, karatun nasa, sababi ne. Na biyu ya zamto
ya iya karatun dalla-dalla. Sannan addu’ar da zai karanta, ba ta ci karo da
tauhidi ba, ba kuma ta bidi'a ba, tsantsar addu’a ce daga bakin Annabi (ﷺ) . Ba
kuma ƙur’ani za a canza ba, ya ce a faro daga Yasin mai rubas (wato
da-baya-da-baya), ko a ce karanta Yasin, idan ka zo mubim na farko sai ka koma
daga farko sai kuma ka je mub'in na biyu, haka-haka har ka sauke surar. Wannan
duk kaucewa turbar Annabi (ﷺ) ne. Nau’i
ne na sihiri, don ba Alƙur’ani daidansa ake karantawa ba.
Sannan abin da ake so
shi ne hucin bakin mai karatun yana samun wajen ciwon, ba wai yawu dinsa ba.
Sannan za ka iya yin addu’ar sau ɗaya, ko biyu ko yadda ka ga buƙatar yin. Wani
idan ya yi sau ɗaya ya wadatar, wani sai ya yi sau biyu, wani uku ko bakwai, ko
goma. Ya danganci ƙarfin imanin mutum.
Don haka, akwai
bambanci tsakanin kambun-baka da maita. Domin mai kambun-baka ba da niyya yake
yi ba, shi kuwa maye, matsafi ne, kuma da niyya yake kama mutum. Domin mayu
suna amfanuwa idan sun yi maita, shi kuwa mai kambun-baka, ba ya amfanuwa da komai
idan wani ya faɗi. Sannan galibin mayu za ka ga ba sa sallah! Da mayu, da
bokaye da ‘yan tsibbu galibi za ka ga aljanu sun shar’anta musu rashin yin
sallah, saboda haka ne shi aljani zai biya musu bukatunsu, zai sato musu kuɗi,
ko ya shiga tsakanin miji da mata Idan mutum yana so a raba wani miji da mata,
sai ya sa aljani ya dunga yawo da wani wari ko ɗoyi kusa da matar, ta yadda da
mijin ya z0 kusa da ita sai ya ji warin, sai ya ɗauka matarsa ce. Nan ko aljani
ne, ba a ganinsa. Haka zai ta yi har sai mijin ya saki matar. Duk waɗannan
(masu duba, da tsibbu, da mayu) duk mushirikai ne. Amma a yau a ƙasar Hausa, su
ne malamai. Ka ji wani ɗan siyasa yana cewa, ‘ai na je wajen wani malami’ nan
ko wajen mushiriki ya je! Buƙatar shi ne, bokan, ko ɗan duban ya musulunta ba
ma ta maganar malinta ake ba. -
Sai dai muna da hadisin
da Abdullahi ibn Abbas ya ba mu daga Annabi (ﷺ) ya ce, “An bijiro min da al’ummomi, sai na ga
wani Annabi, tare da shi akwai mutane (waɗanda ba su fi uku zuwa tara ba). Na
ga wani Annabin tare da shi akwai muturn ɗaya tal, wani Annabin mutum biyu ne
tare da shi. Haka kuma na ga wani Annabin babu kowa a tare da shi. Ina nan a
haka, sai aka nuno min wani duhu-duhu mai girma. Sai na yi zaton al’ummata ce,
sai aka ce da ni, “Wannan Musa ne da al’ummarsa.” Sai na duba, sai na ga taron
mutane masu yawa, sai aka ce da mi, “Waɗannan su ne al’ummarka, a cikinsu akwai
mutum dubu saba’in za su shiga aljanna ba tare da hisabi ko azaba ba.” Sannan
sai ya miƙe (ﷺ) ya shiga gidansa, sai
mutane suka yi ta tattaunawa a kan waɗannan da za su shiga aljanna. Wasu suka
ce, “Watakila su ne waɗanda suka aboci Manzon Allah (ﷺ) ” Wasu kuma suka ce,
“Wataƙila su ne waɗanda aka haife su cikin musulunci, ba su yi wa Allah shirka
ba.” Suka rinka faɗin abubuwa, Sai Annabi (ﷺ) ya fito zuwa gare su, suka ba shi labarin
tattaunawarsu, sai ya ce, “Su ne waɗanda ba sa neman a yi musu tofi, kuma ba sa
yin sakiya, kuma ba sa camfa tafiyar tsuntsaye (wajen aikata wani abu, ko ƙin
aikatawa), kuma suna dogara ne ga Allah shi kaɗai.” Sai Ukkashatu bin Muhsin ya
tashi ya ce, “Ka roƙar min Allah ya sanya ni cikinsu.” Sai (Manzon Allah) ya ce
“Kana cikinsu.” Sai wani mutum daban shi ma ya miƙe ya ce, “Ka rokar min Allah
ya sanya ni cikinsu.” Sai ya ce, “Ukkashatu ya riga ka.(¹)[Bukhari #5752]
_____________
SHARHI;
(¹) Wasu malamai suka
ce, “Yaushe ne aka bijiro wa Annabi al‘umma?" Wasu suka ce, a lokacin da
Annabi ya yi Isra’i, wasu kuwa suka ce, a mafarki, domin mafarkin Annabawa
gaskiya ne.
“...Wani Annabin babu
kowa a tare da shi...” Wannan shi yake nuna ashe gaskiya ana gane ta ne ta
hanyar nassi ba ta yawan mabiya ba! Yanzu ga shi duk iya wa’azi na Annabi, amma
mutanen da suka yi imani ba su fi mutum tara ba. Wani kuma mutum biyu, wani ɗaya,
to wani ma babu! Tare da haka wannan ya Kwacewa Annabawan gaskiyarsu? Don haka
kar ka ruɗu da taron yuyuyu, a’a, taron masu hujja!
Laa yastarƙuna: Ba sa
neman a yi musu tofi. Idan abu ya kama na yin tofi, sai dai su yi da kansu ko
su ƙi yi. Akwai ruwayar da ta ce, “Laa yastarƙuna wa laa yarƙuna. ”cikin
Muslim. Ibn Taimiyya ya ce, “Mai ruwaya ne ya ƙara wannan kalma, asalin abin da
Annabi ya ce, laa ce, laa yastarƙuna bai ce ba laa yarƙuna. Domin idan an
ce, laa yarkuna-ba sa yi, ba za su yi wa kansu ba, kuma ba za su yi wa waninsu
ba. Amma idan aka ce, laa yastarƙuna-ba sa neman a yi musu. Ta iya yiwuwa su yi
wa wani ko kansu, amma su nemo wani su ce ka yi mini, ba za su yi ba, saboda
idan su kai haka sun roƙi wani abu a wajen wani ba Allah ba. Sai dai su yi
shiru.
Wa laa yaktawuna: Ba sa
yin sakiya. Wani abu ya kama, sai an yi sakiya kafin a samu sauƙi, kamar maruru
ko wani abu. Dangane da sakiya, hadisai sun nuna Annabi (ﷺ) ya yi, ya yi wa wani, waɗansu kuwa sun nuna
Annabi ya hana kuma ya yi izini da a yi, kamar yadda Ibnul Kayyim ya faɗa a
cikin littafin Zadul-Ma’ad [4/58], ya ce, “Abubuwa guda huɗu hadisan suke
nunawa. Annabi ya yi, ya hana, ya nuna ba ya so, ya yi izini da a yi.” Duk
hadisan ba sa cin karo da juna. Abin da yake iya fltowa fili a nan, shi ne
aikatawarsa a aikace, don ya nuna halacci ne; haninsa a nan, ba ya nuna
haramci, sai dai barin sa shi ne ya fi kyau; cewar ba ya so a yi, yana nuna
rashin yin sa ya fi yin sa; barin wani ya yi, yana nuna halaccinsa. Don haka,
idan mutum wani abu ya kama shi na a yi masa sakiya, idan ya yi sakiya bai yi
laiil ba, sai dai ya rage wa kansa falala, amma don ya yi, bai yi zunubi ba
Wa laa yata ɗayyaruna:
Asalinsa sun ciro shi ne daga kalmar Aɗɗair. Don Larabawa sun kasance suna
camfa tsuntsaye a wajen tashinsu ko kukansu, sukan camfa kukan wasu tsuntsaye.
Idan mutum zai yi tafiya ko zai kulla kasuwanci ko auratayya, da daddare, sai
ya ji kukan mujiya, sai ya fasa, babu alheri kenan. Ko kuma da sassafe sai ya
zo ya sami tsuntsaye kafin su tashi, ya sami bishiyarsu, ya karkaɗa reshensu
don su tashi. Da sun tashi, aka yi sa’a suka yi dama, to akwai sa’a kenan. Idan
aka yi rashin sa’a suka yi hagu, sai ya fasa, don babu sa’a cikin abin kenan.
Duk wannan yana cikin at-taɗayyur. To, abin yana iya cigaba, ya zamanto ko da
ba da tsuntsaye aka yi amfani ba, shi ma ya zama cikin attaɗayyur: Shi ne
misali, ka wayi gari, sai aka yi rashin sa’a ka fara haɗuwa da kuturu, sai a ce
an yi rashin sa’a, ko ka ci karo da makaho, sai ka ce, “ai yau ba sa’a, tun da
aka ci karo da makaho.” Ko mutum yana kasuwanci kuma harka tana garawa, sai ya
auro mace. A ranar da ta tare, washegari sai aka kama motarka da kaya a cike,
sai ya jingina wa matar. Ya ce dama tana da harara-garke. Sai a ce, ai tun da
ya auro matar yake ta samun matsala. Ga shi yana ciwon kai, rannan an kama
motarsa, kuma yana tafiya ya buge wani a mota. Don haka, duk yadda aka yi matar
nan ce. saboda haka, sai ya sake ta hankali zai kwanta. Wannan ma duk da ba da
tsuntsaye aka yi ba, amma zai shiga cikin ma‘anar. Jingina wani abu na alheri
ko kishiyarsa ga tsuntsaye ko wani mutum, ya zama Ar-taaɗayyur. To su waɗannan
bayin, laa yata ɗayyaruna-wato ba sa camfi. Sai dai akwai hadisin Aisha (RA) da
ya zo wanda yake nuna cewa, idan ma har akwai shu’umci a cikln wani abu, to a
cikin abubuwa uku ne; doki, gida, mata. Hudisin yana cikin Sahihul Bukhari
(#2858, Muslim #2225]. Wannan ba yana nuna cewar za a iya yi ba ne. Sai dai
Annabi (ﷺ) ne yake ba da labarin abin da
Larabawa suke yi na shu‘umci a zamanin jahiliyya. Sukan jingina wa abubuwu da
dama su camfa su, amma galibi sun fi yi a kan waɗannan abubuwa uku.
wa laa rabbihim
yatawakkalun: Ga Ubangijinsu kaɗai suke dogara. Dama ldan har an samu ragowar
ukun, to lallai ga Allah kaɗai za a dogara.
Waɗansu malamai suka yi
tattaunawa a kan me ya sa Annabi bai roƙa wa wannan mutumin ba? Sai wasu suka
ce, duk da cewa adadin yana da yawa. Annubi ya ƙi haka ne don ya rufe ƙofa.
Kada kowa ya tashi, shi ma ya roƙa, ko da kuwa bai cika Sharaɗin ba.
Don haka wannan hadisin
ya tara abubuwa guda huɗu waɗanda sai ka cika sharuɗɗansu sannan za ku shiga
cikin waɗanda za su shiga aljanna ba hisabi ba azaba.
********************
A Cikin Wannan Babi
Akwai Mas’aloli Kamar haka;
1. Gane
matsayin mutane a cikin tauhidi
2. Ma’anar
tabbatar da haƙiƙanin tauhidi.
“Shi
ne nisantar shirka da bidi'a da nisantar abinƙi.”
3. Yabo
daga Maɗaukaki ga Annabi Ibrahim, da cewa bai kasance cikin masu shirka ba.
4. Yadda
Allah ya yabi shugabannin waliyyan Allah saboda sun nisanci shirka.
5. Barin
neman a yi ruƙya da sakiya yana nuna tace tauhidin mutum.
6. Kasancewar
abin da yake faɗa, cewa ba sa yin tofi, sakiya da camfi, shi ne cikakken
tawakkali.
7. Zurfin
ilimin sahabbai da suka gano cewa ba a samun matsayi a wurin Allah, sai da
aiki.
__________
SHARHI;
Mun fahimci wannan,
ƙarƙashin hadisin ta yadda, da Annabi (ﷺ) ya ce mutum dubu sabu’in za su shiga aljanna
ba azaba, ba hisabi, sahabbai ba su ce, waɗannan ‘ya’yan Annabi ba ne, ko
‘ya’yan shehi wane, ko waliyyi wane, a’a sai suka jingina abin da aiki. Sun san
cewa, ba a samin matsayi dan dangantaka, sai dai ta aiki. Wannan ya nuna zurfin
ilimin sahabbai kenan.
8. Kwaɗayinsu
bisa ga aikin alheri.
9. Falalar al’ ummar Annabi (ﷺ) ta fuskar adadi da kuma siffofi.
10.
Falalar sahabban Annabi Musa.
11.
Gifta al'ummomi gaban Manzon Allah (ﷺ) .
12.
Kowace al’umma za a tashe ta, ita da
Annabinta.
13.
Ƙarancin waɗanda suke amsa wa Annabawa.
14.
Annabin da bai samu wanda ya amsa masa
ba, zai zo ranar ƙiyama shi kaɗai.
15.
Amfanin wannan ilimin tauhidi shi ne ba
a ruɗuwa da yawa da kuma rashin ƙyamatar adadi ya zama kaɗan.
16.
Yin rangwame a kan tofi saboda
kambun-baka, ko kuma cizon abu mai dafi.
17.
Zurfin ilimin magabata (Salaf), saboda
faɗinsu, “Lallai wanda ya yi aiki da ƙarshen abin da ya ji, to ya kyautata ba
da son rai ba, sai dai ni ina da hadisi kaza da kaza. Sai aka fahimci cewa
hadisin farko bai saɓa wa hadisi na biyu ba.
18.
Yadda magabata suke nisantar da kansu
daga yabon abin da ba su da shi.
SHARHI;
Mun fuhimci wannan a
wajen da Sa‘id ibn Jubair ya tambayi ɗalibinsa cewa wa ya ga tauraro cikin
dare? Ɗalibin ya ce ni ne, amma ba sallah nake ba kar ace ga waliyan Allah, ba
sa barci sai sallolin dare! Ba ya san ayabe shi da abin da ya san ba shi
yake ba. Amma mutanen yanzu, so suke a yabe su da abin da ba su yi ba ma.
19.
Faɗar Annabi (ﷺ) cewa. “Kai kana cikinsu." alama ce da
take nuna annabtar Annabi (ﷺ) .
20.
Falalar Ukkasha.
21.
Halaccin amfani da salon hannunka-mai-sanda
a cikin magana.
22.
Kyawawan halayen Annabi (ﷺ) .
(FASSARA DA SHARHI DA
GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ). (zamuci gaba Insha Allah)
Dan Allah sonake a fada min usullai uku
ReplyDelete