GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Apr 21, 2019

KITABUT-TAUHID (BABI NA HUƊU 4)


Jin Tsoron Afkawa Cikin Shirka
______________
Wannan babi zai yi magana a kan jin tsoron afkawa cikin shirka. Wato alamar imani ya kankama a jikin mutum shi ne kullum ya ji yana tsoron afkawa cikin shirka, mutum yana taka-tsantsan a magana ko aikin da yake shirka ne. Kar mutum ya amintu ya dinga jin cewa ya tsira ya hau tudun mun tsira daga afkawa cikin shirka.
********************
Da faɗin Allah;
“Haƙiƙa Allah ba ya gafarta wa haɗa shi da wani (shirka), yana gafarta wa abin da bai kai shirka ba, ga wanda ya so. (An-Nisaa:116)
________________
SHARHI;
Wannan aya ta maimaitu har sau biyu a Suuratul Nisaa’i. Menene shirka? Abin da ake nufi da shirka, shi ne kamanta abin halitta da mahalicci.
Abin halittar nan ko da mala’ika ne, ko Annabi ne, ko waliyyi ne, ko malami ne, aljan ne, ko ɗan Adam ne, kowannen su abin halitta ne. Ka kamanta abin halitta cikin abin da mahalicci ne kaɗai ya keɓanta da shi, kamar abin da ya shafi rububiyya (ayyukan Ubangiji). Idan ka. kudurce a zuciyarka abin da mahalicci yake yi, shi ma abin halitta yana iya yi, to ya yi shirka. Kamar abin da ya shafi ibada; keɓantaccen abu ne da ake yi wa Allah. Idan ka ƙudurce ban da Allah akwai wanda akan iya bauta masa, ko a kira shi ya ji, ya amsa, cikin abin da babu wanda yake iya yi, sai Allah, to ka kamanta wannan da Allah, shi ma shirka ne. Shirka ta kasu kashi biyu, akwai babba da Ƙarama.
a. Bubbar shirka: Shirka babba ita ce ka ɗauki nau’in ibada ka sarrafar da shi ga wanda ba Allah ba. Kamar addu’a wajen roko ba a kiran kowa sai Allah. Wannan haƙƙi ne na Allah, idan za a kira, a kira shi shi kaɗai. Da ya zama an sarrafa ba ga Allah ba, ya zama babbar shirka.
b. Ƙaramar shirka kuwa shi ne kamar riya. Yana daga cikin ƙaramar shirka rantsuwa ga wani wanda ba Allah ba. Idan mutum ya yi, bazaka ce ya kafurta ba, amma dai ya yi shirka. Yana daga cikinsu kukan mutuwa. alfahari da ƙabila ko yare. Malamai suka ce, dukkan abin da in dai an yi shi, zai kai mutum ga babbar shirka, to
wannan abu ya zama ƙaramar shlrka.

To, a nan wurin wace irin shirka ce Ubangiji ba ya gafartawa? Babbar ko har da ƙaramar, ko duka biyun? ƙarama da babba Allah ba ya gafartawa, sai dai rashin gafarta babba na dawwamar da mutum a wuta, rashin gafarta ƙarama na sa a kama mutum da laifi gobe ƙiyama, daga ƙarshe a kai shi aljanna. Ba a yafe babba da ƙarama! Haka Sheikh al-lslam ibn Taimiyya ya tabbatar.
Gaɓar, “Yana gafarta abin da bai kai shirka ba ga wanda ya so”
tana nufin sauran zunubban da ba su kai shirka ba waɗanda suke tsakaninka da Allah ne, Allah yana gafarta wa wanda ya so daga cikin bayinsa. Amma laifukan tsakanin ka da ɗan Adam kamar ka cinyewa ɗan uwanka kuɗi, to Allah ba ya gafarta wannan sai dai idan ɗan uwan ya yafe.
********************
Kuma Khalil (AS) ya ce;
“Kuma ka nisanatar da ni da ‘ya’yana daga bautar gumaka". (Ibraahim :35)
_______________
SHARHI;
Wato roƙon da Annabi Ibrahim (AS) ya yi, ga shi da matsayi na badaɗin Allah. Wannan na nuna cewa, hatta bayin Allah manya-manya, nagari, ba sa amintuwa, roƙon Allah suke yi ya kare su ga barin shirka; ta magana ko ta aiki ba tare da sun sani ba. To idan har Annabawa suna tsoron afkawa shirka, to waɗanda suke koma bayan su fa? Ai min babu aula kenan. Wannan shi yake nuna munin shirka. Wannan shi ne alaƙar babin da ayar.
Su waye ‘ya’yansa da yake roƙon a kare su daga bautar gumaka? Waɗansu suka ce, Annabi Isma’il (AS) da Ishak (AS), domin su ne ‘ya’yansa a tarihance, duk sauran jikoki ne. Saboda kalmar, ‘banin’ jam’i ne, daga uku zuwa abin da ya yi sama. Waɗansu suka ce, “A’a!” Dukkan
wanda yake dangantuwa zuwa ga zuriyarsa; Ishaƙ, Isma’il, Yaƙub da dukkan jikokinsa ne yake roka musu. To idan muka ɗauki cewa yana roƙar wa ‘ya’yansa biyu ne, Isma’il da Ishak, mun san Allah ya amsa addu‘ar kenan. ldan kuwa muka ɗauka cewa kalmar, banin tana ɗaukar ‘ya‘yansa. jikokinsa, da ‘ya’yan jikokinsa, shin za mu ce Allah ya amsa addu’arsa kenan'.’ Domin a cikinsu aka samu yahudu, maɓarnata a bayan ƙasa. Zai yiwu a ce addu’arsa Allah ya amsa ta, ko kuwa zai yiwu a ce ba a amsa addu‘ar Annabi ba? Amsar shi ne, an amsa wani ɓangare, kuma ba a amsa wani ɓangaren ba. Ba dole ba ne idan Annabi ya yi addu’a Allah ya amsa masa gabaɗaya, zai iya amsa rabi yaƙi amsa rabi. Shugaban halitta ma Annabi (ﷺ)  ya roƙi addu’o’i Allah ya amsa wani ɓangaren bai kuma amsa wani ɓangaren ba kamar yadda za mu gani a babi na ashirin da uku (23). To a nan Allah ya ƙi amsawa ne saboda wata hikima tasa ba wai don ba ya son annabin ba, ko kuma Annabi ba shi da matsayi ba ne, a’a saboda hikima ɓoyayya wajen Allah. Kamar yadda shi dai Annabi Ibrahim (AS) ya roƙi Allah ya azurta muminan Makka, sai Allah ya ce har kafiran sai na azurta. Ya amsa wani ɓangaren bai amsa wani ba. Kuma wannan shi yake nuna Ubangiji mulkinsa cikakken mulki ne, ba a yi masa dole, abin da ya ga dama yake yi kamar yadda ya ce:
“Mai aikata abin da ya yi nufi (Buruj:l6)
Wani cikin Annabawansa ko mala’lkunsa ba ya tursasa shi cikin abin da bai so ba. Wannan shi ne dalilin da wani sa’ilin idan Annabawa sukai addu'a Allah ba ya karɓa. To idan har wani lokacin Allah ba ya karɓar addu‘ar Annabawa, to wannan zai sa ka fi aiki kawai ka ce ‘Allah ya sa mu a tutar Annabi gobe ƙiyama’, kuma Allah ya karɓa? Ba zai yiwu ba.
-
Ya zo a cikin wani hadisin cewa, “Lallai mafi tsoron abin da nake ji muku tsoronsa, shi ne ƙaramar shirka. Sai suka ce, “Mene ne ƙaramar shirka, ya Manzon Allah! sai ya ce “riya!”
__________________
SHARHI;
Wannan hadisin Imam Ahmad ibn Hambali da Imam Ɗabarani suka ruwuito shi. Wunnan ruwayar lmam Ahmad ce da ke cikin Musnad [J5/428-429]. Sai Annabi ya cigaba da ƙarin bayani, ya ce, “Allah Maɗaukaki Sarki zai faɗa a ranar tashin Ƙiyama, idan ya kammala yi wa mutane sakamako da ayyukansu, sai Allah ya ce da masu riya, “Ku tafi zuwa wurin mutanan da kuka yi aiki don su yaba muku a duniya, ku je ku bincika ku gani ko za ku samu sakamako a wurinsu?” Wannan shi ne cikon hadisin.
Kalmar, ‘riya' daga kalmar ‘ru ’ya’ ne wanda yake nuna ido, ma’ana nuna wa mutane aikinka. Ka yi wani aiki don mutane su gani. To, menene hukuncin mutumin da ya yi aiki don mutane su ji ba su gani ba? Zai shiga cikin hadisin, saboda ya ba da labari ne don a yaba, kamar yadda wanda ya aikata yake neman a yaba masa. Domin wannan manufarsu ta don a yaba musu, ita ce ta rushe aikin. Ƙarin bayani zai zo a babin riya [Babi na 36].
Annabi (ﷺ)  ya ce abin da ya fi mana tsoro shi ne ƙaramar shirka bayan babbar shirka ta flta hatsari, to me ya sa'? Dalili shi ne ita babbar shirka a fili take, duk mai hankali da tunani da ilimi, kamar sahabbai da Annabi yake gayawa, za su guje ta. To amma ƙaramar shirka a ɓoye take, mutum zai iya faɗawa idan bai hankali ba, shi ya sa ya fi musu tsoron ƙaramar shirka. To idan har sahabbai da takawarsu da imaninsu ana ji musu tsoron shirka to ina ga wanɗa ba sahabi ba?! Sannan kuma ita babbar shirka ba a samun wata fa’ida ta duniya idan mutum ya yi, amma ƙaramar shirka kamar riya mutum na samun yabon mutane idan ya yi. To kuma zuciyar ɗan Adam tana da son duniya, wannan shi ne asali a zuciya kamar yadda Allah ya tabbatar:
“Ba haka ba ne ba! Ku kuna son mai gaggawa (duniya) Kuma kuna ƙyale gida na ƙarshe (lahira). (Ƙiyama 20-21)
“Sannan kuna son dukiya so mai yawan gaske” (Fajr)
ldan mutum zuciyarsa ta fi son lahira a kan duniya, to mutum ya hori zuciyarsa kenan, ya zama ulul azmi minan nass. Shi ya sa Annabi ya fi ji mana tsoron abin da zuciyar mutane ta fi karkata a kai na neman duniya. Don haka ne salaf yadda suke kullum za su kwanta barci sai su yi wa kansu hisabi, su auna a awa goma sha biyu na rana me su kai na kirki? Me
su kai na mummuna? Wanne su kai don Allah, wanne ne ba don Allah ba?
********************
An karɓo hadisi daga Abdullahi ibn Mas’ud (RA) cewa, Manzon Allah (ﷺ)  ya ce, “Wanda ya mutu alhali yana kiran wani wanda ba Allah ba, zai shiga wuta.”. Bukhari [#4497] ne ya ruwaito.
____________
SHARHI;
Man mata: Wanda ya mutu alhali ya kasance a kan tafarkin kiran wani wanda ba Allah ba. Wato mun ce addu'a iri biyu ne. Akwai du’a’u ibada’atin wanda haƙƙin Allah ne shi kaɗai. Du ’a ’u mas’alatin kuwa, za a kasa ta kashi biyu:
a. Idan ka roƙi ɗan Adam a kan abin da yake iya mallakarsa, to wannan ba ka yi shirka ba.
b. Idan ka roki ɗan Adam a kan abin da ba shi da iko a kansa sai Allah, to ka yi shirka.
Niddan: Kalmar niddu’ a Larabce daidai take da ‘al-shibhu’. Wato wane ya yi kama da wane. Wato ka kamanta wani tare da Allah, ka ga a nan ka yi wa Allah kishiya kenan. Annabi (ﷺ)  ya ce, ‘'Zai shiga wuta’' Dakala ɗin nan, fi'i madhi ne amma yana nuna abin da zai zo nan gaba.
********************
A riwayar Imam Muslim [#93] daga Jabir ibn Abdullahi (RA) cewa, Manzon Allah (ﷺ)  ya ce, “Wanda ya gamu da Allah gobe ƙiyama, ba ya haɗa Allah da wani wajen bauta, zai shiga aljanna. Amma wanda ya gamu da Allah, yana hada shi da wani abu (wajen bauta), zai shiga wuta.”
______________
SHSRHI;
Shi ne Imam Nawawi yake cewa, “Abin da muka sani a ilimance, duk wanda yake haɗa Allah da wani, kuma ya zamanto aka bincika abin nan shirka ce babba, to zai shiga wuta, kuma babu fita. Amma duk wanda yake haɗa Allah da wani, kuma ya zamanto shirka ce ƙarama, to hukuncinsa zai shiga wuta, sai dai ba zai dawwama a ciki ba.

Malamai sun ce, faɗin, “Wanda ya haɗu da Allah ba ya haɗa shi da wani abu, zai shiga aljanna.” To rashin yin shirka zai lamunce wa mutum shiga wuta ne ko kuwa? Domin tana iya yiwuwa mutum bai yi shirka ba, amma ya aikata wani abin da zai shigar da shi wuta. Shi ya sa Suka ce, wannan hadisin sai ka haɗa shi da sauran waɗansu hadisan, Domin akwai wasu hadisan da suke nuna shiga wuta idan an aikata wasu laifukan, ba wai sai shirka kaɗai ba. Ko kuma ka ba shi ma’ana daga Imam nawawi yana cewa, abin da ake nufi da shiga wuta shi ne, “Idan babbar shirka ce, babu shi ba shiga aljanna, idan kuma ya shiga wuta zai dawwama. ldan ƙaramar shirka ce, sai an yi masa azaba a wuta, amma bazai dawwamaba, daga karshe za a ɗauke shi zuwa aljanna.”
********************
A Cikin Wannan Babi Akwai Mas’aloli kamar haka:
1. Tsoron fadawa cikin shirka.
2. Lallai riya tana daga cikin shirka.
3. Riya tana cikin ƙananan shirka.
4. Riya ita ce mafi girman abin da ake tsoratar wa salihan bayi afkawa ciki.
5. Kusancin aljanna da kusancin wuta.
6. Yadda aka haɗa kusancinsu a hadisi daya.
7. Duk wanda ya haɗu da Allah ba ya shirka zai shiga aljanna, duk kuma wanda ya haɗu da Allah yana shirka zai shiga wuta, ko da ya fi mutanen zamaninsa yawan ibada.
8. Babbar mas’ala mai girma wato, yadda Annabi Ibrahim Khalilullahi ya yi addu’a a kare shi da ‘ya’yansa daga bautar gumaka.
9. Ƙoƙarin kare su daga bin taron yawa, kamar yadda ya faɗi cewa, “Ya Ubangiji! Su gumaka sun halakar da mutane masu yawa.” Shi ya sa yake so a kare shi daga karkatar masu yawa daga mutane.
10. A wannan babi mun fahimci tafsirin, ‘La’ilaha I'llallah’ kamar yadda Imam Bukhari ya faɗa” “Tafsirin La'ilaha illallaah shi ne rashin yin Shirka.”
1 1. Falalar mutumin da ya kuɓuta daga yin shirka!




(FASSARA DA SHARHI DA GA BAKIN GARIGAYI SHEIK JA’AFAR MAHAMUD ADAM {R} ).  (zamuci gaba Insha Allah)

No comments:

Post a Comment

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...