An karɓo daga Jabir ɗan Abdullahi
(R.A) ya ce, “Naji Manzon Allah(ﷺ), a
shekarar buɗe Makka, a lokacin (Manzon Allah(ﷺ), ) yana Makka, yana cewa “Lallai Allah da
Manzonsa sun haramta sayar da giya da mushe da alade da gunki.” Sai aka ce, Ya
Manzon Allah(ﷺ), ! Ba mu labari game da kitsen mushe, ana shafawa a jikin
jirgin ruwa, ana shafawa a fata, ana kunna fitilu da shi, (shin ya halatta ko
bai halatta ba?).”
A'UUZU BILLAAHIS SAMII'IL ALIM MINASSHAIƊAANIR RAJIIM, BISIMILLAAHIR RAHMAANIR RAHIIM. ALHAMDU LILLAAHI RABBIL AALAMIIN, WASSALAATU WASSALAAMU ALAA AS'ADIL NABIYYINAA WA'ASHARAFIL MURSALIIN NABIYYINA MUHAMMADIN WA'ALAA AALIHI WASAHBIHI AJMA'IIN WAMAN DA'AA BIDA'AWATIHI WASTANNAH BISSUNNATIHI ILAA YAUMIDDIN.
GABATARWA.
WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM
WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!
DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]
Friday, November 18, 2011
ARBA'UNA HAADITH (44) HADISI NA ARBA'IN DA HUDU
An karɓo daga A’isha (R.A) ta ce, Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Shayarwa tana haramta abin da haihuwa
take haramtawa.” Bukhari (#2646) da Muslim (#1444) suka rawaito shi.
SHARHI;
Ma’ana, idan mace ta haife ka
tana da matsayin mahaifiyarka, ba ka
aure ta a shari’ance; ba ka auren duk ‘yayan da ta haifa; ba ka da aurenƙannenta, domin sun zama ƙannen mahaifiyarka, ‘ya’yan da ta
haifa sun zama yayayenka ko ƙannenka, ba ka auren mahaifiyata, ta zamanto kakarka. To
haka matar da ta shayar da kai, ba ka aurenta a shari’ance; ba ka auren
‘ya’yanta a shari’ance, domin sun zama yayyenka ko ƙannenka; ba ka auren
ARBA'UNA HAADITH (43) HADISI NA ARBA'IN DA UKU
An karɓo daga ɗan Abbas (R,A) ya ce,
Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ku riskar da
kowanne rabon gado sananne ga ma’abotan wannan rabon, abin da ya ragu, to a ba
namiji wanda
ya fi kusanci.” Bukhari (#6732) da
Muslim (#1615) ne suka rawaito shi.
SHARHI;
Abin da wanna hadisi yake nufi shi
ne, rabon gado kashi biyu ne: Akawai waɗanda ake basu da farali, wato masu rabo
sananne, wanda shi kuma ya kasu kashi shida: ko a ce a baka rabin dukiya (1/2), ko ɗaya
bisa hudu (1/4) na dukiya, ko ɗaya bisa takwas(1/8) na dukiya,
ko ɗaya bisa uku (1/3) na dukiya, ko biyu bisa ukun (2/3) na
dukiya, ko ɗaya bisa
ARBA'UNA HAADITH (42) HADISI NA ARBA'IN DA BIYU
An karɓo daga Anas ɗan Malik (R.A)
ya ce, “Na ji Manzon Allah (ﷺ), yana
cewa, Allah Maɗaukakin Sarki yana cewa, “Ya kai ɗan Adam! Lallai ba za ka bauta
min ba, kuma ka sanya rai game da rahamata ba, face sai na gafarta maka ban
damu ba. Ya kai ɗan Adam! Da a ce zunubanka zasu cika sashen sama gaba ɗaya,
sannan ka nemi gafarata, sai in gafarta maka. Ya kai ɗan Adam!
Da a ce zaka zo min da cikin ƙasa
gaba ɗaya zunubai ne, sannan ka gamu dani, ba tare da ka haɗa ni da kowa ba, Ni
kuma zan kawo maka gafara, cikin ƙasa.” Tirmizi ne ya rawaito shi (#3540)
ya ce, hadisi ne mai kyau, ingantacce.
ARBA'UNA HAADITH (41) HADISI NA ARBA'IN DA DAYA
An karɓo daga Abu Muhammad
Abudullahi ɗan Amru ɗan As (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ɗayanku ba ya zama mumini, har sai son
zuciyarsa yana biyayya ga abin da na zo da shi.” Hadisin ne ingatacce, mai
kyau, mun rawaito shi a cikin littafin Hujja da sanadi ingantacce.
SHARHI;
Wanna hadisi an karɓo shi daga Abu
Muhamad, shi ne Abdullahi ɗan Amru ɗan As, ɗaya daga cikin ‘Abadila’
(wato waɗanda ake kira Abdullahi ) a cikin sahabbai,
waɗanda su huɗu ne, duk sunansu ya
fara Abdullahi: su ne, Abdullahi bn Umar, Abdullahi bn Abbas, Abdullahi bn
Mas’ud da Abdullahi bn Amru bn As. Waɗannan
Tuesday, November 15, 2011
ARBA'UNA HAADITH (40) HADISI NA ARBA'IN
An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar
(R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ), ya dafa
kafaɗata ya ce, “Ka kasance a duniya tamkar kai baƙo ne, ko kuma wanda yake kan
hanya.” Ɗan Umar (R.A) yana cewa, “Idan ka kai yamma, kar ka yi jiran safiya,
idan kuma ka wayi gari, to kar ka jira yamma. Ka riƙi aiki alheri lokacin
lafiyarka, saboda lokain rashin lafiyarka. Ka riƙi aiki alheri lokacin
rayuwarka, saboda ka
SHRHI;
Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Ka kasance a gidan duniya tamkar baƙo
ne…”
ARBA'UNA HAADITH (39) HADISI NA TALATIN DA TARA
An karɓo daga ɗan Abbas (R.A) ya ce
Manzon Allah (ﷺ), ya ce, “Allah Ya yafe
wa al’ummata, abin da ta yi dakuskure, da mantuwa, da abin da aka tilasta ta.”
Hadisi ne mai kyau Ibnu Majah ne ya rawaito shi (#2045) da Baihaƙi a
cikin Sunan.
SHARHI;
Waɗannan abubuwa guda uku an yafe wa
Al’ummar Annabi (ﷺ), . Kuma wannan ɗaya ne daga cikin abin da yake nuna
falalarmu a kan sauran al’ummai, saboda sauran al’ummai ba a basu wannan damar
ba. Mu kaɗai ne muke da irin wannan damar, don ya ce a hadisin, “Allah Ya yafe
wa al’ummata…” wanan ya nuna sauran al’ummar da suka gabata, ba su sami wannan
falalar ba.
Subscribe to:
Posts (Atom)
FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHAMUD ADAM (R)
KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)
SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...
-
SAURARI MUQADDIMA DA SHARHIN HADISI NA (1) DAGA BAKIN MARIGAYI SHEIK JAFAR MAHMUD ADAM DOWNLOAD An karɓo daga Sarkin Muminai, baban...
-
An karɓo daga Umar (R.A) ya ce, "Yayin da muna zaune a wurin Annabi (ﷺ) wata rana, sai wani mutum ya bayyana gare mu, mai tsananin far...
-
KITABUT-TAUHID _____________ SHARHI Abin da tauhidi yake nufi shi ne kaɗait...