GABATARWA.



WWW.TAFARKINSUNNAH.BLOGSPOT.COM

WANNAN SHAFI YANA DAUKE DA HADISAN ANNABI(SAW)ACIKIN HARSHEN HAUSA. IDAN ANGA MUNYI KUSKURE ASANAR DA MU.ALLAH YAYI MUNA JAGORA AMEEN!



DAMIN AIKO DA GYARA KO KARIN BAYANI;
{tafarkinsunnah@gmail.com]

Wednesday, September 14, 2011

ARBA'UNA HADITH (9) HADISI NA TARA

An karɓo daga Abu Huraira Abdur-Rahman ɗan Sakhrin (R.A), ya ce, na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, "Duk abin da na hane ku (da bari), to ku nisance shi. Abin da na umarce ku da shi, to ku zo da shi (wannan abin) gwargwadon iko. Abin da ya hallakar da waɗanda suke kafin ku, yawan tambayoyinsu, da saBawarsu ga Annabawansu."Bukhari (#7288) da Muslim (#1337) suka rawaito shi.

SHARHI

Wannan hadisi, an karɓo shi daga Abu Huraira, Iimamin masu hadisi cikin sahabban Annabi (ﷺ). Sunansa shi ne Abdur-Rahman bin Sakhrin Addausiy. Malamai sun yi

Monday, September 12, 2011

ARBA'UNA HADITH (8) HADISI NA TAKWAS

An karɓo daga Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, "Lallai Annabi (ﷺ) ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane, har sai sun shaida babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, (sun yarda Annabi) Muhammad Manzon Allah ne, su tsayar da sallah, kuma su bayar da zakka. Idan sun aikata haka, sun kare jininsu da dukiyoyinsu daga gare ni, sai da haƙƙin musulunci, hisabinsu yana wajen Allah Maɗaukaki." Bukhari (#25) da Muslim (#22) ne Suka ruwaitoshi.
                       
SHARHI
Da Annabi (ﷺ) ya ce, "An umarce ni in yaƙi mutane....", a nan kafuai ake nufi, ba dukkan mutane ba. Wannan wani salone na larabci, salo ne na Alƙur'ani, salo ne na hadisi, a

ARBA'UNA HADITH (7) HADISI NA BAKWAI

An Karɓo daga Abu Ruƙayya, (shi ne) Tamim ɗan Ausid Dari (R.A) ya ce, Annabi (ﷺ) ya ce, "Addini nasiha ne!" Sai muka ce, "Ga wa?" sai ya ce, " (Nasiha ne) ga Allah, da Littafinsa, da Manzonsa, da shugabannin musulmi, da dukkan mutane" Muslim ne ya rawaito (#55)

SHARHI

A larabce abin da kalmar annasiha take nunawa, shi ne tace zuciyarka, wanke zuciyarka dangane da wanda aka ce ka yi masa nasiha ɗin. Don haka shi tace zuciya ya sha bamban: Idan ya zamanto tace zuciya ga Allah ne, to kenan kar ka

ARBA'UNA HADITH (6) HADISI NA SHIDA

An karɓo daga Abu Abdullahi, Nu'uman ɗan Bashir, (R.A) ya ce, "Na ji Manzon Allah (ﷺ) yana cewa, "Lallai halal a bayyane take, kuma lallai haramun a bayyane take, amma a tsakaninsu akwai al'amura masu rikitarwa, da yawa daga cikin mutane ba su san su ba. Duk wanda ya nisanci abubuwa masu rikitarwa, haƙiƙa ya nemi kuɓutar da addininsa da mutuncinsa. Wanda ya auka cikin abubuwa masu rikitarwa, to ya auka cikih haram. Kamar makiyayi ne da yake kiwo a gefen shinge, ya kusanta ya shiga (ya yi kiwo) a cikinsa. Ku saurara! Kowane sarki yana da iyaka. Ku saurara! Iyakar Ubangiji ita ce abubuwan da ya haramta. Ku saurara! Lallai a cikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru, dukkan jiki ya gyaru, idan ta lalace, dukkan jiki ya lalace. Ku saurara! (Wannan tsokar ɗaya) ita ce zuciya."
Bukhari #59 da Muslim (#1599).

SHARHI
Ma'ana, halal a bayyane yake a cikin Alƙur'ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (ﷺ), haka kuma haramun a bayyane yake a cikin Alkur’ani da hadisai tabbatattu daga Annabi (ﷺ), amma a tsakanin halal da haram, akwai

Wednesday, June 1, 2011

ARBA'UNA HADIT (5) HADISI NA BIYAR


An karɓo daga Ummul Mu'uminina, Ummu Abdullahi, A'ishatu (R.A) ta ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ce, "Wanda ya ƙirƙiro wani abu cikin lamarinmu wannan, abin da ba ya cikinsa, to za a mayar masa da kayansa." Bukhari (#2695) Muslim (#1718)
A riwayar Muslim "Wanda duk ya aikata wani aikin da ba umaminmu a kai, an mayar masa da shi.

SHARHI

Aisha ɗaya ce daga cikin matan Annabi (ﷺ), ta samu falalar kasancewarta matar Annabi (ﷺ). Duk cikin matan Annabi (ﷺ) ya fi ƙaunar ta sama da kowa. Don an

Tuesday, May 31, 2011

ARBA'UNA HADITH (4) HADISI NA HUDU

An karɓo daga Abu Abdurrahman Abdullahi ɗan Mas'ud (R.A) ya ce, Manzon Allah (ﷺ) ya ba mu Iabari, shi ne mai gaskiya cikin dukkan al'amuran da yake, kuma abin gasgatawa, ya ce, "Lallai kowane ɗayanku ana tara halittarsa a cikin mahaifiyarsa, tsawon kwana arba'in yana maniyyi, sannan ya canza ya zama gudan jini kwatankwacin wannan, sannan ya juya ya zama tsoka kwatankwacin haka, sai a aiko Mala'ika ya busa masa rai, a umarce shi da rubuta kalmomi huɗu: A rubuta arziƙinsa da ajalinsa, da aiyukansa, da kuma, ɗan wuta ne ko aljanna. Na rantse da wanda babu wani abin bauta sai shi, lallai ɗayanku zai yi aiki irin na 'yan aljanna, har ya zamanto ba abin da ke tsakaninsa da aljanna sai zira'i ɗaya, sai rubutun can ya rigaye shi, sai ya yi aiki irin na 'yan wuta, sai ya shige ta. Lallai ɗayanku da zai yi aiki irin aikin 'yan wuta, har ba abin da ke tsakaninsa da ita sai zira'i ɗaya, sai littafi ya rigaye shi, sai ya yi aiki irin aikin 'yan aljanna, sai ya shige ta. Bukhari (#3208) Muslim #2643).

SHARHI

Abdullahi bin Mas'ud (R.A) yana cikin

ARBA'UNA HADITH (3) HADISI NA UKU

An karɓo daga Abu Abdurrahman, Abdullahi ɗan Umar (R.A) ya ce, “Na ji Manzon Allah( ﷺ) yana cewa, "An gina musulunci a kan abubuwa guda biyar: Shaidawa babu abin bautawa bisa ga cancanta sai Allah, kuma Annabi Muhammad (ﷺ) Manzon Allah ne, da tsayar da Sallah, da ba da zakka, da ziyarar ɗakin Allah, da azumin watan Ramadan." Bukhari (#8) Muslim (#16).

SHARHI

"Abdullahi ɗan Umar yana cikin mutane bakwai da suka fi kowa haddace hadisan Annabi (ﷺ). Abin da za mu lura da shi a nan shi ne, a wancan hadisi na biyu da aka tambayi Annabi (ﷺ) musulunci, sai ya

FASSARA DA SHARHI DAGA MARIGAYI SHEIKH JAFAR MAHAMUD ADAM (R)

KITABUT-TAUHID (Babi Na Goma Sha Biyar15)

  SHARHI Babukan da suka wuce sun yi magana a kan yana daga dangin shirka neman taimako wajen wanin Allah. Wannan babi kuma zai nuna maka ...